12/12/2025
Assalamu Alaikum
🌳🌹🎄🪷🌴🌷🍀❤️💚
A ranar 20 ga watan Jimada sani hijiriya duniya ta kuma samin wani haske
da ya haskakata na samun
Alkhairi babba.
Ina nufin a wannan wata ne aka haifi sayyida Fatima (A.S.)
'Ya ga shugaban halitta(S.A.W.W.) Annabin Rahma Muhammad Sallallahu Alaihi Wa'alihi wa sallam.
KO KA SAN WACECE
FATIMA (S.A.)
Daga bakin da bai taba qarya ba baban Fatima yace;
Fatima tsokace daga gare ni.
Fatima Allah yana yadda da yaddar ta yana fushi da fushin ta.
Fatima shugabar matan Aljanna.
Fatima mahaifiyar shuwagabannin samarin Aljanna.
Fatima matar Zakin Allah dan uwan shugaban halitta.
Fatima 'ya ga sayyida khadijatul kubra matar Annabin Rahma ta farko wacce Annabi yake cewa Allah bai bani mata ba kamar khadija kuma ba zai bani kamar ta ba.
Fatima Batul Azzahra Maradhiya Ma'asuma Zakiya Saddiqa Ummu Abiha Kausar sunayen ta suna yawa salamullahi alaiha.
💚 🌹💜🌳❤️🍀🪷🎄🙏 🙏 🙏💌👸🍏🍓✈️
Yau rana ce ta farin ciki da murna domin taya masoyin Allah murna na kyautar da Allah yayi masa ya bashi Fatima (S.A.) lokacin da Allah cikin ikon sa ya karbi 'ya'yan Annabin Rahma suna qanana sai kafiran maka s**a riqa yi masa gori cewa bashi da wanda zai gaje shi har ma suna cewa mai yankakkan baya.
Sai Allah mabuwayi da daukaka ya sau karmar da
INNA A'ADAINAKAL KAUSAR.
Karanta har qarshen sura.
Allah yace mu mun baka KAUSAR wato sayyida Fatima salamullahi alaiha
Kuma aka sanya wani kogi a gidan Aljanna Kausar ba mai shansa sai masoyin sayyida Fatima salamullahi alaiha.
Ya Allah muna son Fatima da Babanta da Mijinta da 'ya'yanta.
Ya Allah bama tare da makiyanta da makiyan Babanta da da makiyan mijin da makiyan 'ya'yan ta da duk wanda ya cutar da su har izuwa ranar qiyama.
🌳🌹🌴🌷🎄🪷🍀💚🍓💜🍏❤️✈️
09/11/2025
Assalamu Alaikum barkanmu wannan lkc fatan kowa yanacikin koshin lafiya ga kadan daga cikin fassarar Littafin
“Tarihin Rayuwar Mista Hempher, Jambin Sirri na Birtaniya zuwa Gabas ta Tsakiya”
Fassarar Chapter 1 – Hausa
Babi na 1: Farkon Labari da Aikina a matsayin ɗan leƙen asiri
Sunana Hempher. Ni ɗan leƙen asiri ne na Burtaniya, an tura ni zuwa ƙasar Larabawa don bincike da tattara bayanai game da al’amuran Musulmai. Aiki na na farko shi ne ganin yadda za a samu hanyoyin da za su raunana Musulunci daga ciki, musamman ta hanyar shigar da wasu tunani marasa kyau a cikin zukatan mutane.
Tun kafin in isa Larabawa, an koya mani dabarun yaɗa rikici da rarrabuwar kawuna, sannan an ja hankalina kan cewa wasu mutane za su iya zama abokan haɗin gwiwa a cikin wannan aiki. Na fara karatu sosai game da al’adun Larabawa, addininsu, da yadda suke gudanar da rayuwarsu. Wannan bincike ya zama muhimmiyar hanya domin ni fahimtar inda za a iya shiga cikin al’umma ba tare da an gano ni ba.
A wannan babi, Hempher ya bayyana dalilin aikinsa:
Samun bayanai kan halayyar Musulmai
Fahimtar shugabannin addini
Nemo hanyoyin da za a shafar addini daga ciki
Ya bayyana cewa aikin sa na farko a zahiri shi ne samun abokai da jin ra’ayoyi da kuma fara shigar da wasu ra’ayoyi masu tada hankali ga wasu mutane, domin a hankali su fara shakkar koyarwar da suke bi.
A ƙarshe na babi na farko, Hempher ya nuna cewa zai fara aiki cikin hankali, yana amfani da dabaru da wayo, domin kada a gano cewa shi ɗan leƙen asiri ne.
Rubutawa 🙏👇🥰
✍🏾🥰
21/09/2025
https://whatsapp.com/channel/0029VbAQiQaChq6OfsnIEd0s/1982
*KU KOYA WA YARANKU HALAYE UKU:*
1. Yawan gaishe da na gaba dasu.
2. Nutsuwa da barin wasa ahanya.
3. Futa cikin kyakykyawar shiga.
KU HANA YARANKU HALAYEN NAN:
1. Yawan yawace-yawace.
2. Yawan Abokai/kawaye barkatai.
3. Rashin kunya da fadace-faface.
KU RIKA GWABE BAKIN YARANKU:
1. Idan suna sa baki a maganar manya
2. Idan suna kawo tsegumi da gulma.
3. Idan suna zagi ko karyata manya.
KUYI MUSU HORO ME TSANANI:
1. Idan suna wasa da Sallah.
2. Idan s**a fara kwadayi da roko
3. Idan s**a fara karya da lalaci.
KU KARA JAWO YARANKU JIKI:
1. Idan s**a balaga.
2. Idan basu da lafiya.
3. Idan kuna gida a zaune.
KU KWADAITAR DA YARANKU:
1. Nacin karatu da rubutu.
2. Dagewa wajen cimma buri.
3. Lada da nasara in anbi hanyar Allah.
KU NUNAWA YARA MUHIMMANCIN:
1. Riko da Addinin musulunchi.
2. Zumunchi da ziyarar dangi.
3. Lafiya, Lokachi da chance/kuruciya.
KU DAINA WADANNAN AGABANSU:
1. Bayyana tsiraici/mu'amalar aure
2. Wasan banza na kuruciya, kallo.
3. Bayyana rashin jituwa atsakaninku.
KU YAWAITA AGABAN YARANKU:
1. Karatun Alqur'ani da salloli.
2. Aikata gaskiya da Rukon Amana.
3. Wadatar zuci da godiyar Allah.
SUKE JIN TSORON KU TA HANYAR:
1. Tsawatar musu in sunzo da wargi.
2. Rashin barinsu babu abinyi.
3. Taqaita nuna musu so kuru-kuru.
KU DAGE KU CIREWA YARANKU:
1. Tsoron mutuwa.
2. Tsoron talauchi.
3. Tsoron wanda baya tsoron Allah.
KU GOYI BAYAN YARANKU INHAR:
1. sune ke da gaskiya.
2. Ba sa6o s**a aikata ba.
3. sunyi abu domin kare mutuncinku.
KUKE TSORATAR DA YARANKU:
1. Illar Hadama.
2. Futinar rigima.
3. Hadarin taqama da girman kai.
KU RIKA SANARDA YARANKU:
1. Asali da Tarihi.
2. Mutuwa da kabari.
3. Dadi da rashin sa.
KU BAWA YARANKU HORO NA:
1. Taqaita cin abinchi.
2. Karancin Barchi da zaman hira.
3. Watsar da dogon buri da sharholiya
whatsapp.com
03/08/2025
Farashin kaya a Karamar Hukumar Akko Tumu Ward 19/07/2025
Farashin Masara =27k zuwa 35k
farashin Dawa= 35k zuwa 40k
farashin shinkafa= 30k zuwa 40k
farashin farin wake= 60k zuwa 70k
farashin waken suya= 60k zuwa 70k
Ubangiji Allah ya cigaba da shiga Cikin lamarin mu Allah yayi Mana jagoranci
12/12/2024
🎉 Just completed level 3 and I'm so excited to continue growing as a creator on Facebook!
11/07/2024
Ina Yan'uwa na Hussaina wa wannan wata watan juyayi ne Yakamata mudage da karanta tabat yada ba adadi akan makasan imamai😭😭😭 da wanda suke da hannu akisansu d wd s**aji daɗi Allah ya ƙara jaddada la anarsu