Al-Haramain Kids College

Al-Haramain Kids College

Share

A learning center established to develop a passion of learning purposely to replace an empty minded society with an open minded community.

Section: Model Islamiyya & Modern Tahfeez

03/09/2024

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

As-Salamu alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh

Bayan wannan daddaɗar gaisuwa mai tarin albarka, Hukumar Makarantar Al-Haramain Kids College na sanarwa ɗokacin al'ummar musulmi cewa tuni ta fara ɗaukar sababbin ɗalibai a ɓangarori kamar haka:

Ɓangaren Tahfeez:
Admission Form: ₦500
Registration Fee: ₦1,000
School Fee: ₦3,000
Kwanakin Karatu: Asabar da Lahadi
Lokutan Karatu: 9:00 (na safe) - 4:00 (na yamma)

Ɓangaren Islamiyya:
Admission Form: ₦500
Registration Fee: ₦1,000
School Fee: ₦1,500
Kwanakin Karatu: Litinin, Talata, Laraba, Alhamis
Lokutan Karatu: 2:30 (na rana)-5:30 (na yamma)

Ɓangaren Boko (Nursery and Primary)
Admission Form: ₦1,500
Registration Fee: ₦1,500
School Fee: ₦5,000
Uniform for Boys: ₦4,000
Uniform for Girls: ₦4,500

ƘARIN BAYANI: Saboda yanayin da ake ciki, muna bada damar Part Payment (Biya Biyu), zaka biya kaso biyun ukun kuɗin a karin fari, sannan bayan sati huɗu ka biya ragowar kaso ɗayan ukun kuɗin.

A ƙarshe, muna yiwa kowa fatan alheri, tare da addu'ar Allah ya yaye mana wannan tsanani da matsatsi da ake ciki, ya h**e mana baki, ya bamu ikon sauke nauyin ilmantar da al'umma zuwa ga ilimi mai amfani duniya da Lahira.

TUNTUƁE mu a Harabar Makarantar dake Sheka Sabuwar Abuja kan hanyar zuwa Sheka Majalisa, Kumbotso L.G.A., Kano.
KIRA mu a lamba 08133338700, 08180989690.

Mun gode.
Wassalam!

School Director:
Kabir Isa Muhammad

01/08/2023

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

As-Salamu alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh!

Bayan haka, Kwamitin Makarantar Al-Haramain Kids College mai albarka yana sanar da ɗokacin al-ummar Musulmi cewa ta fara gudanar da Ƙwarya-ƙwaryar Karatu (Extra Lesson) ga ɗalibai na tsawon Sati Biyar a Ranakun Litinin, Talata da Laraba, da misalin 9:00 (na safe) zuwa 12:00 (na rana), a harabar Makarantar dake S/Abuja kan hanyar Sheka Majalisa.

Manufa da ƙudirin wannan zaman karatu shi ne:

1) Koyar da Sanin Baƙi wajen tantance kowanne harafi da surorin sa cikin kalmomi, sautin sa in an masa wasali, tare da iya bambance harufa masu kamanni wajen furta su ko wajen rubutu,

2) Koyar da Karatun Al-Ƙur'ani Mai Girma da Tajwidin sa, wajen Ada'i da Taɗbiqi (iya furta kowanne harafi baiwa kowanne hukuncin Tajwidi abin da ya cancanta,

3) Koyar da Arabiyya wajen sanin salon zance yanayin tattaunawa da zauƙi irin na Larabawa Tsantsa na Asali.

A ƙarshe, muna godiya ga Allah da ya raya mu zuwa yanzu kuma yake bamu nasarar abubuwan muka saka a gaba.

Wassalam

15/10/2022

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Assalamu alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh!

Kwamitin wannan Makarantar Al-Haramain na sanar da ɗokacin al'ummar musulmi cewa in Allah ya kai mu kuma ya yarda bisa h**ewar shi Ranar Juma'a mai zuwa wato 21 - 10 - 2022 za a fara karatu a Ɓangaren Matan Aure wanda zai ke gudana duk sati kamar haka:

RANA: Juma'a
LOKACI: 3:00 na yamma zuwa 5:30 na yamma

Yadda za a bi wajen shiga wannan ɓangaren da masu buƙata shi ne:

1) Siyan Takardar Neman Shiga (Admission Form) kan kuɗi N250
2) Biyan Kuɗin Shiga (Registration Fee) N250
3) Biyan Kuɗin Makaranta (School Fee) N250 duk wata, ko N1,000 duk Zango
4) Ɗinka Hijabi yalwatacce da zai kai har ƙasa da ya dace da sharaɗan Hijabi na Muslunci

NB: Kalar Hijabin ita ce Kore Mai Duhu sosai (Dark Green) da cin baki Hijabi da Fuskar Hijabi da Ruwan Ɗorawa (Butter Milk).

Littattafan da za a karantar sune kamar haka:

Ƴan Matakin Farko (Beginners):
1) Qur'ani: Hizb Biyar (5)
2) Hadisi: Al-Fawakihush Shahiyyah na 1
3) Tauhidi: Munyatul Murid na 1
4) Huruf: (Al-Qa'idatun Nuraniyyah)
5) Fiqhu: Mukhtasarul Muharrar fil Fiqhil Muyassar
6) Azkar: Hisnu Aɗfalil Muslim
7) Arabiyya: Durus al-Luggah na 1

Ƴan Matakin Tsakiya (Intermediate):
1) Qur'ani: Hizb 20
2) Hadisi: Al-Fawakihush Shahiyyah na 2
3) Tauhidi: Munyatul Murid na 2
4) Fiqhu: Al-Muharrar fil Fiqhil Muyassar na 1
5) Azkar: Hisnul Muslim
6) Sirah: Khulasatu Nuril Yaqin na 1
7) Tahzib: Tarbiyyatul Aulad fi Dau'il Kitabi was-Sunnah
8) Mu'amalat: Sifatuz Zaujatis Sallah
9) Arabiyya: Durus al-Luggah na (2)

Ƴan Matakin Tsakiya (Intermediate):
1) Qur'ani: Hizb 60
2) Hadisi: Umdatul Ahkam
3) Tauhidi: Al-Usul al-Thalathah wal-Ƙawa'idul Arba'u
4) Fiqhu: Al-Muharrar fil Fiqhil Muyassar na 2
5) Azkar: Hisnul Muslim
6) Sirah: Khulasatu Nuril Yaqin na 2
7) Tahzib: Kaifa Nurabbi Auladana na Li Muhd Jamil Zainu
8) Mu'amalat: Zaduz Zaujain da Fannut Ta'amul bainaz Zaujain
9) Arabiyya: Durus al-Luggah na (3)

Allah ya bada iko...

19/09/2022
Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Majalisa Street
Kano
700321

Opening Hours

Monday 09:00 - 18:00
Tuesday 09:00 - 18:00
Wednesday 09:00 - 18:00
Thursday 09:00 - 18:00
Friday 09:00 - 15:00
Saturday 09:00 - 19:00
Sunday 09:00 - 19:00