14/04/2025
Yaushe Rayuwa za ta kai Magaryar Tuƙewa a Mahangar Kimiyya?
Masana ilimin kimiyya sun yi hasashen cewa nan da shekara ta 1,000,002,021 bayan fakuwar Annabi Isa (AS) (wa zai iya lissafa mana saura shekara nawa kenan?), rayuwa (Life) ba za ta iya cigaba da wanzuwa a wannan duniyar tamu ta أرض (Earth 🌍) ba, kasancewar a lokacin girman rana ya ƙaru matuƙa ainun, a sabili da cigaba da ƙarar da makamashinta da take tayi, wanda shi kuma zai ƙare ne nan da shekaru biliyan biyar masu zuwa.
Izuwa yanzu dai rana ta wanzu tsawon sama da shekaru biliyan huɗu da miliyan ɗari shidda (>4.6 billion years) da s**a shuɗe, kuma a matsayinta na ɗaya daga cikin taurarin da'irar taurari ta Milkyway (Milkyway Galaxy) waɗanda basu da girma sosai, wacce kwatankwacin girmanta bai wuce a ruɓanya girman duniyarmu sau miliyan ɗaya da dubu ɗari ukku ba, ana sa ran makamashin ire-irensu yana ƙarewa ne a wanzuwarsu ta shekara biliyan goma kacal.
Makamashin taurari ko kuma in ce ranaiku da ya kasance sinadirin Hydrogen, wanda kuma yake sauyawa zuwa sinadarin Helium ta hanyar bin wani tsari da ake kira 'da Nuclear Fusion', yana ƙarewa taurarin za su tashi daga aiki, wasunsu za su kumbura sai kuma su noƙe, manyan taurari kuma za su yi bindiga ne su fashe su zama 'Black Hole', da dai sauran ire-iren hakan.
Ita ma rana kamar sauran taurarin, da zarar tana cigaba da ƙona sinadarin Hydrogen ɗinta zuwa na Helium, da zarar kuma tana ƙara girma, hakan kuma zai cigaba da ta'azzara zafinta a nan duniyarmu da ma sauran duniyoyin da ke maƙwabtaka da ita, wanda kuma izuwa sanda za ta ƙarar da makamashin nata ta zama gwangwani (White Dwarf) a samaniya, ana sa ran tuni duniyoyi guda uku da suke kusa da ita sun liƙe a jikinta sun narke sun zama sashenta.
Tambayoyi a :
1. Shin za mu yi 'evolving' ne zuwa masu juriya ga tsananin zafin rana domin mu ɗan ƙara jimawa akan wannan duniyar tamu kafin ranar ta kamushe ta?
2. Ko kuma zamu yi hijira ne zuwa wata daga cikin duniyoyin unguwar rana (Solar System) ne, ko wani daga cikin watannin (Satellites) ɗin da ke kewaya manya duniyoyin unguwar?
3. Ko kuma kawai ilimin kimiyya da fasaha za su taimaka mana ne mu ƙera manya maɗaukanmu (Space Ships) da za suyi ta yawo damu a samaniya ne?
4. Ko ko zamu nemi sabon mazauni ne daga wasu daga cikin duniyoyin wajen unguwar Rana (Exoplanets) a can nesa da nan?
Dr. Las Ɗanbuzu