MAI LAMAI Islamiyyah Kaltungo

MAI LAMAI Islamiyyah Kaltungo An Islamic School that is integrated with both Madarasah and Western Western Education.

Which aim to promote the intellect of younger one within Kaltungo chiefdom.

Alhamdulillah Yaukenan Daga Mai lamai islamiyya,Yayinda babban Malaminmu Ya gabatar mana Da Nasiha,Muna godiya malam All...
13/08/2026

Alhamdulillah Yaukenan Daga Mai lamai islamiyya,
Yayinda babban Malaminmu Ya gabatar mana Da Nasiha,
Muna godiya malam Allah ya biya,Ameen

20/07/2026

Karatun AlQur'ani mai Girma tare da Alaramma Abubakar Sadiq Hussaini daga wannan makaranta Mai Albarka ta Mai Lamai Islamiyyah Kaltungo

إنا لله وإنا إليه راجعون، اللهم اغفر لها وارحمها 🤲 Cikin alhini da jimami, muna miƙa saƙon ta'aziyyarmu ga iyayen Ɗaliba...
20/07/2026

إنا لله وإنا إليه راجعون، اللهم اغفر لها وارحمها 🤲
Cikin alhini da jimami, muna miƙa saƙon ta'aziyyarmu ga iyayen Ɗaliba Fatima Dalhatu Sani da dukkan 'yan uwanta, mazauna Unguwar Kalorgu, da Kaltungo gabaɗaya, bisa ga wannan babban rashi.

Muna roƙon Allah (SWT) Ya gafarta mata, Ya sanya kabarinta ya zama daga cikin lambunan Aljannah, Ya sa ta huta daga wahalhalun duniya, Ya haɗa ta da bayinsa na ƙwarai a Aljannatul Firdaus.

Allah Ya ba iyayenta da 'yan uwanta haƙurin jure wannan babban rashi, Ya maye musu da alheri.

Allah Ya jikanta da rahama. Amin.

13/07/2026

SANARWA GA IYAYE DA MASU KULA DA ƊALIBAI

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Idan aka ga alamun haɗari mai tsanani ko kuma ana hasashen ruwan sama sosai, ana roƙon iyaye da masu kula da ɗalibai su hanzarta zuwa makaranta domin ɗaukar yaransu, saboda a irin wannan hali ana iya sallamar ɗalibai kafin lokacin tashi na yau da kullum, gudun kada ruwan sama ko wani haɗari ya tare su a hanya.

Amma idan babu wata matsala ta yanayi, lokacin tashi na yau da kullum shi ne ƙarfe 5:10 na yamma, don haka ba a buƙatar zuwa ɗaukar ɗalibai kafin wannan lokaci.

Allah Ya kiyaye mu da ɗalibanmu baki ɗaya.

Bissalam.

11/07/2026

SANARWA

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Alhamdulillah, muna sanar da iyaye da ɗalibai cewa gobe Lahadi, 27 Muharram 1448H (12 July 2026), za a ci gaba da karatu bayan hutun sati ɗaya da aka bayar, In shaa Allah.

Muna roƙon iyaye da su tabbatar da cewa yara sun halarci makaranta a kan lokaci. Haka kuma, duk wanda bai biya kuɗin Islamiyyah na watan shida ba, a zo da kuɗin gobe, In shaa Allah.

Allah Ya ba mu zaman lafiya da albarka a sabon makon karatu. Bissalam.

04/07/2026

Ga kaɗan daga cikin abin da ɗalibanmu s**a gabatar kafin a bada hutun ƙarshen zango

03/07/2026

Alhamdulillah😍
Wannan kaɗan ne daga cikin abin da ɗalibanmu s**a samu damar koya a wannan zangon karatu.

Muna roƙon Allah ﷻ Ya sa ilimin ya amfani rayuwarsu, Ya ƙara musu fahimta da istiqama, Ya saka wa iyaye da malamai da mafificin alheri.

Ku kalla, ku yi sharhi, sannan ku yi wa ɗalibanmu addu'a. 🤲

03/07/2026

Ba karatu kaɗai ake yi ba… ana gina tarbiyya, ana koyon Al-Qur'ani, Hadisi, da harshen Larabci.

Ga ɗan haske daga ayyukan ɗalibanmu kafin hutun ƙarshen zango.

Allah Ya sa mu haɗu bayan hutu cikin alheri. Ameen 🤲.

01/07/2026

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh.

Ana sanar da iyaye, ɗalibai, da al'ummar makaranta cewa, gobe Alhamis, 17 Muharram 1448H (2 July 2026), za a ba da hutun ƙarshen zangon karatu na makarantar Islamiyya.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sa abin da aka koya ya amfani ɗalibai, Ya ba su hutu mai albarka, Ya kuma ba mu ikon sake haɗuwa cikin ƙoshin lafiya da nasara.

Jazakamullahu Khayran.

13/06/2026

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ

Muna miƙa saƙon taya murna ga malamammu masu daraja na Mai Lamai Academy Islamiyyah:

🎓 Malam Muhammad Saminu Hussaini wanda ya kammala karatun digiri na farko a fannin Computer Science.

🎓 Malama Khadija Alhassan Abdullahi wadda ta kammala karatun digiri na farko a fannin Microbiology.

Muna taya ku murna bisa wannan babban nasara. Muna roƙon Allah (SWT) Ya sanya ilimin da kuka samu ya zama mai amfani gare ku da al'umma baki ɗaya. Allah Ya ƙara muku basira da hikima, Ya buɗe muku ƙofofin alkhairi da arziki mai albarka, Ya ba ku nasara a dukkan al'amuranku na gaba.

Allah Ya sanya wannan nasara ta zama mafarin ɗaukaka da cigaba a rayuwarku. Ameen Ya Rabbal-'Alamin. 🤲

🌹 Taya murna da kammala karatun First Degree. 🌹

Daga: Mai Lamai Academy Islamiyyah.

Address

Yola Road
Kaltungo

Opening Hours

Monday 02:00 - 05:00
Tuesday 02:00 - 05:00
Wednesday 02:00 - 05:00
Thursday 02:00 - 05:00
Friday 09:00 - 06:00
Saturday 09:00 - 06:00
Sunday 02:00 - 05:00

Telephone

+2347038594031

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MAI LAMAI Islamiyyah Kaltungo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share