Rigasa Reporters News

Rigasa Reporters News

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Rigasa Reporters News, Kaduna.

Wannan kafar yada labarai ne dake Wallafa sahihan Labarai na gida da wajen Nigeria a harshen Hausa Akan internet kadai, Domin samar dazaman lafiya da wayar dakan Jama'a

25/05/2026

RA'AYIN AL’UMMA – ZABEN ADC 2027

A ra'ayin ka, wa ya k**ata jam’iyyar ADC ta tsayar takara a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa?

🔘 Ameachi
🔘 Alh Hayatu
🔘 Atiku Abubakar
🔘 Nasir El-Rufa’i
🔘 Wani daban (Ka faɗa a comment)

✍️ Ka bayyana ra’ayinka cikin mutunci da siyasa mai tsafta.

25/05/2026

DOMIN FARANTA MARAYU, DA SAKA SU NISHADI.

Kungiyar Nisa'ul Barakah Foundation ta gudanar da aikin alheri inda ta yi wa maza da mata sama da marayu 200 aski, lalle da kitso,

Domin faranta musu rai da sanya su cikin annashuwa k**ar yadda sauran yara masu iyaye suke murnar Sallah.

Wannan karamci ya kara nuna kulawa da tausayi ga marayu tare da cusa musu farin ciki da jin cewa suma ba a manta da su ba.

Daga Shugabar Kungiyar
Haj, Khadija S Umar.

25/05/2026

Wa kuke ma fatan samun nasara a zaben Fidda Gwani na Gwamnan Jihar Kaduna a Jam'iyyar ADC ?

25/05/2026

Lokutan Sallah Idi Babban

Sanarwar daga Shugaban Kungiyar Izala ta Rigasa Karkashin Jagorancin Mal Abu Sufyan da Kwamitin sa,

Sun saka lokutan sallar Idi bana 1447 A.H 9:00am

Dafatan za'ayi sallah lafiya.

Photos from Rigasa Reporters News's post 25/05/2026

LABARI MAI DAƊI GA AL’UMMAR KAHUTU 🔥

Inji: Abbany rara

Yanzu-yanzu an fara rabon tallafin Sallah a garin Kahutu inda mutane sama da 4,000 za su amfana da buhunan shinkafa da kuma kuɗin cefane domin sauƙaƙa wa jama’a gudanar da bukukuwan Sallah.

Wannan tallafi na fitowa ne daga hannun Maimartaba Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa, Dauda Kahutu Rarara, wanda ya ci gaba da nuna ƙauna da tausayi ga al’umma musamman a wannan lokaci na bukukuwa.

Al’umma da dama sun bayyana farin cikinsu tare da yabawa wannan karamci da kulawar da ake nunawa talakawa.

Tambaya:
Shin irin wannan tallafi yana ƙara haɗin kai da soyayya a tsakanin al’umma?

23/05/2026

BA BELLO KADAI NAYI ZABE BA 2023.

Inji: Hon Samaila Farar Aniya.

Tsohon ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kaduna North, Samaila Farar Aniya ya bayyana cewa zaben 2023 da aka yi bai tsaya kan mutum ɗaya ba, illa haɗin kai da goyon bayan gwamnati da al’umma gaba ɗaya.

A cewarsa:

“Bada Bello kaɗai na zabe ba a 2023. Ni da Bello da Gwamnatin Jihar Kaduna da kuma jama’a muka yi zaɓe tare a wancan lokacin.”

Ya ƙara da cewa an nuna wa Bello gata sosai a lokacin zaɓen, amma yanzu siyasa ta canja salo.

“A wannan karon, tsakanina da Bello ne za a yi zaɓe kai tsaye. Babu maganar gatar da ya samu k**ar yadda aka yi a 2023.”

Wannan furuci na Hon. Farar Aniya na nuni da cewa siyasar Kaduna North na 2027 za ta kasance mai zafi da ɗaukar hankali,

musamman ganin yadda manyan jiga-jigai ke fara bayyana matsayinsu tun kafin lokacin zaɓe ya ƙarato.

Tambaya Ga Jama’a:

Shin kuna ganin wannan magana ta Hon. Farar Aniya na nuna ƙarfin siyasa ne, ko kuwa alamar sabuwar takaddama ce tsakanin sa da Bello a tunkarar zaɓen 2027?

23/05/2026

Shin zaka iya zaban Obi/Kwankwaso a matsayin Shugaban Kasar Najeriya ?

A- Eh zan iya
B- Zan fara duba manufofinsu
C- A’a bazan zaba ba

Tambaya ga Jama’a:

A ra’ayinku, wane irin shugaba Najeriya ke bukata a wannan lokaci ?

Photos from Rigasa Reporters News's post 20/05/2026

Jam’iyyar ADC ta tabbatar da Atiku Abubakar a matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa bayan kammala tantance shi, yayin da matakin ke ci gaba da jan hankalin al’ummar Najeriya da masu bibiyar siyasa a fadin kasa.

Yaya kuke kallon sa a zabe na gaba?

20/05/2026

Inda Wata babbar mota ta kubuce a Hannun Direban yayi kan mutane acikin kasuwa.

Wace Irin shawara zaku bawa masu Irin wannan motar musamman idan s**a shigo gari ?

19/05/2026

Idan Shi Aka Ba, Zan Bi Shi — Idan Ni Aka Ba, Zai Bi Ni” 🔥

Wannan kalamai daga Rt, Hon Zailani da Sen, Shehu sani sun dauki hankalin mutane bayan zaben fidda gwani.

Sai dai tambayar da mutane da dama suke yi ita ce: Shin wannan hadin kai zai dore bayan an bayyana wanda ya samu tikiti? 🤔

A siyasa, kalamai masu dadi suna da muhimmanci, amma abin da jama’a s**a fi so shi ne ganin hadin kai da aiki tare a aikace, ba kawai a baki ba.

Idan har wannan alkawari ya tabbata, zai iya zama babban darasi ga sauran ‘yan siyasa cewa siyasa ba fada ba ce, siyasa hadin kai ce da mutunta juna domin cigaban al’umma.

Rigasa reporters news

Photos from Rigasa Reporters News's post 18/05/2026

KOTU TA BADA BELIN NASIR EL-RUFAI.

Kotu ta bayar da belin tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai a kan kudi Naira miliyan 100

Mai shari’a Joyce Abdulmalik, a hukuncinta, ta bayyana cewa wanda zai karbi belin Malam dole ne ya kasance mazaunin unguwannin Maitama ko Asokoro dake Abuja

Sannan kuma dole ne ya ajiye takardar shaidar asalin mallakar kadararsa (Certificate of Occupancy)

Amma ance kuma yanzu haka jami'an tsaro na farin kaya sun sake k**a Malam Nasir El-Rufai bayan ya samu beli daga Kotu k**ar yadda IG Wala ya bayyana

Yaa Allah Ka bawa Malam Nasir mafita na alheri

Want your school to be the top-listed School/college in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Kaduna