05/06/2026
Murmushin Tsakanin Duniya Biyu: Labarin Soyayyar Rasulullah ﷺ da Fatimah az-Zahra رضي الله عنها
Lokacin da Rasulullah ﷺ yake kan gadon mutuwa, Fatimah رضي الله عنها ta shigo cikin ɗakin.
Sai ﷺ yayi mata wasu maganganu a kunne.
Ta fashe da kuka.
Sai ya sake yi mata wasu maganganu a kunne.
Ba zato ba tsammani, fuskarta ta haskaka da murmushi.
Daga baya, Aisha رضي الله عنها ta tambaye ta, “Me ya ce Maki?”
Fatimah ta amsa:
“Da farko, ya gaya mini cewa yana gab da mutuwa, don haka na yi kuka. Sai ya gaya mini cewa zan zama na farko daga cikin iyalansa da zai hadu da shi. Saboda haka na yi murmushi.”
(Sahih al-Bukhari 3624)
Bayan da Annabi ﷺ ya bar duniya, Fatima az-Zahra — wadda take haskakawa — ta dushe.
Ta kasance tana cewa sau da yawa:
“Babu wani bala’i da ya taɓa samu na fiye da mutuwarka, ya Rasulullah ﷺ.”
Ta yi kuka har mutanen Madina s**a ce mata:
“Ya ’yar Rasulullah, kukan ki yana damun mu.”
Baƙin cikinta ya kasance k**ar tsaunuka.
Bayan watanni shida kawai, Fatimah ta yi rashin lafiya. Ta san lokacinta ya kare.
Ta faɗi a hankali wa kuyanginta:
“Ki zuba mini ruwa in yi wanka. Ki lulluɓe ni da sabbin tufafina kuma ki ajiye ni inu fuskantar Qibla.”
Sai ta kwanta, ta rufe idanunta, kuma ta jira — tana tunawa da maganar mahaifinta: “Zaki zama ta farko wanda zata hadu da ni.”
Ali ibn Abi Talib رضي الله عنه ya shigo ya same ta tana murmushi a cikin mutuwa.
Ba murmushin zafi da ke barin jiki ba ne.
Murmushin ’yar da ta sake ganin ƙaunataccen mahaifinta ne.
A hannunta akwai wani yanki na rigar Annabi wanda ta ajiye kusa da ita tun bayan an binne shi. Ta riƙe shi yayin da take komawa gare shi.
Tana da shekara 29 kawai.
Ta bar ’ya’yanta — Hasan, Husayn, Zaynab, da Umm Kulthum رضي الله عنهم — da kuma al’ummar Musulmai masu baƙin ciki.
Amma ta samu abin da zuciyarta ta fi so: mahaifinta ﷺ.
Watanni shida na rabuwa sunyi k**ar dawwama ga irin zuciyarta.
Wannan soyayya ce da ko mutuwa ba za ta iya karyawa ba.
Mahaifi wanda ya ta’aziyar ’yarsa a kan gadon mutuwarsa.
’Yar da baƙin cikinta ya zama ibada, kuma murmushinta a mutuwa ya zama tabbataccen imani.
Alaƙarsu ta kasance na duniya da Lahira.
Wannan shine abin da “iyali” ke nufi a Aljanna.
Ga kowace ’ya mace da ke kewar mahaifinta…
Ga kowane uba da ya binne ƙaramar ’yarsa…
Ba ku kasance ku kaɗai ba.
Haɗuwa ta gaskiya ce.
Murmushi yana zuwa.
> “Kuma waɗanda s**a yi imani kuma zuriyarsu s**a bi su da imani — Za Mu haɗa su da zuriyarsu…”
> (Surah At-Tur 52:21)
Sahih al-Bukhari, Ibn Sa’d’s
Tabaqat, Sahih Seerah.
~👨🏾💻✍🏾📝