Hussaini Hudu

Hussaini Hudu

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hussaini Hudu, Education, Hayin Banki, Kaduna State, Kaduna.

26/01/2026

Brian Boom Lumbus

17/01/2026

With Brian Boom Lumbus – I've just earned their Boom Family badge!

29/11/2025

*MA'ANAR SALATUL FATIH..*

Daga: *Maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Alhussaini (RadhiyalLahu Anhu)..*

*Allahumma* : Ya Allah..

*Salli* : Ka yi salati. Wannan kuma addu'a ce da mumini yake fuskantar Ubangijinsa mai girma da ɗaukaka; domin ya yi salati ga Annabinsa Muhammad (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), wannan shi ne ma'ana *"Allahumma Salli".*

*Salli ala Sayyidina Muhammad Alfatihi Lima Ughliq:* Ma'ana: ka yi wa shugabanmu, Annabi Muhammad salati, wanda shi ne ya buɗe abin da aka riga aka rufe: ma'ana: da shi ne Allah ya buɗe rufaffun zukata, da doɗaɗɗun idanuwa, da tosassun kunnuwa, da shi ne Allah ya buɗe ƙofofin imani, da ƙofofin rahama; saboda da ma shi ne rahamar Allah, wanda akansa ne Allah yake cewa: *((Lallai ba mu aiko ka ba sai domin ka zamo rahama ga talikai)),* wannan abu a bayyana ne, *Lallai shi ne ya buɗe abin da a da a rufe yake..*

*Wal khatimi Lima sabaƙ:* Wanda ya cika abin da ya gabata, hakan yana nufin cewa: shi ne cikamakin Annabawa da Manzanni, da shi ne aka cika wahayi da duk wani saƙon da ya zo daga Allah.. wannan ma a fili yake..

*Nasiril haƙƙi bil haƙƙi:* mai taimakon gaskiya da gaskiya, ma'ana: Lallai wannan Annabi, Muhammad (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), wanda muke roƙon ka yi masa salati, shi ne ya taimaki addininka da gaskiya, ko kuma shi ne ya taimaki Allah mai girma da ɗaukaka da gaskiya, ma'ana: ya taimaki gaskiya da gaskiya. Mai taimakon gaskiya da gaskiya, saboda idan ka ce: ma'anar gaskiya a nan ita ce: Musulunci, to babu shakka ya taimaki Musulunci da gaskiya, idan kuma ka ce: gaskiya a nan tana nufin Allah mai girma da ɗaukaka ne, to shi ma dai ya taimaki Allah Maɗaukakin Sarki, saboda ayar da take cewa: *((In dai har kuka taimaki Allah, to shi ma Allah zai taimake ku ya kuma tabbatar da ku akan daidai)).* Wannan ne ma'anar *"mai taimakon gaskiya da gaskiya..*

*Walhadi ila siradikal mustaƙim:* Mai shiryatarwa zuwa ga hanyarka madaidaiciya, Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: *((Wallahi kai ɗin nan kana shiryatarwa zuwa ga hanya madaidaiciya)),* wannan ma a fili yake..

*Wa ala Alihi haƙƙa ƙadrihi wa miƙdarihil azim:* ka haɗa da alayensa, salatin ya zamo daidai da matsayinsa da darajarsa masu girma, ma'ana: Ka kuma yi irin wannan salatin ga iyalan gidan zaɓaɓɓenka Annabi Muhammad (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), gwargwadon matsayinsa, ma'ana: salatin da za ta tabbata, tamkar irin yanda matsayinsa ya tabbata a wurinka, ko gwargwadon girma, da darajarsa a wurinka. Idan ka ƙaddara wannan girma, da matsayi, da daraja, da lada, ko kyawawan ayyuka, ko girmamawar da Ubangiji yake yi wa Manzonsa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) duka sun yi, domin abubuwa ne da ba za ka iya lissafa su ba, ba kuma za ka taɓa yin masu iyaka ba..

Wannan shi ne ma'anar *"Salatul Fatih lima Ughliƙ".* Siga ɗaya ce daga cikin sigogin salatin Annabi. Ki karanta littafin As Shifa na Alƙali Iyadh za ki ga wannan maganar. Wannan ɗaya ce daga sigogin salatin Annabi da Imam Aliyu Bn Abuɗalib (KarramalLahu wajhahu) yake yi wa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati da shi, ki duba littafin Ibn Kasir, da littafin Shifa'ul Asƙam" na Imam As- Subkiy...

26/11/2025

Brain Jotter

Want your school to be the top-listed School/college in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Culinary Team

Attire

Website

Address

Hayin Banki, Kaduna State
Kaduna
09017351576