22/07/2026
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
GAYYATAR TARON SAUKA/HADDA ALQUR'ANI MAI GIRMA
Hukumar Gudanarwa, Malamai da Daliban Hasseb Achievers Academy suna farin cikin gayyatar ku zuwa Bikin Saukar Dalibai na makarantar da kuma ɗaliba ɗaya da ta haddace Alqur'ani mai Girma.
Rana: Asabar, 9/2/1448H- 26/07/2026
Wuri: Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi College (wacce aka fi sani da Makarantar Chachangi).
Lokaci: Karfe 9:00 na safe In Allah ya kaimu.
Kasancewarku a wannan taro zai ƙara wa taron armashi tare da nuna goyon baya ga ilimi da ƙoƙarin ɗalibanmu.
Muna fatan za ku amsa wannan gayyata tare da halartar wannan gagarumin biki.
Allah Ya sanya alheri, Ya albarkaci taron, amin.