(ZUMUNCI)

(ZUMUNCI)

Share

Dalilin bude wannan page shine dan
kara dankon zumunci da jaddada
zumunci

Zumunci : Umarni ne na Allah manzon Allah, muyi kokarin sadar da zumunta, kuma kar mu yanke zumunta, duk wanda yake da sadar da zumunci to zumunci zai cece shi a ranar kiyawa, musamman akan siradi, duk wanda ke yanke zumunta kuwa to bashi ba rahamar ubangiji.

16/11/2025

Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un
Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un
Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un

Allah Yayiwa Mahaifinmu Mahaifin Dan Uwanmu Abokinmu Wato

MUSTAPHA SALIHU NINGI

Za’ayi Janazansa Ayau Dinnan Anjima Kadan Da Misalin Karfe 9:00am Na Safennan, Insha Allah!

Allah Yajikansa Yayi Masa Rahama, Allah Yakarbi Bakuncinsa, Allah Ya kyautata Makwancinsa, Jinyar Dayayi Fama Da’ita Allah Yasa Tazama Kaffara Agarashi, Allah Yasa Annabi (SAW) Yasan Da Zuwansa, Allah Yabaka Ya Bamu Hakuri, Juriya Da Dangana Tareda En Uwa Da Abaokanan Arziki Gamida Zuri’a Baki Daya, Aameen Ya Hayyu Ya Qayyum.

Mu Sakashi Cikin Addu’oinmu!

Ga Lambar Shi Nan (Mustapha Salihu)
Domin Yi Masa Ta’aziyya!
08062538181

Zumunci Peoples Association of Nigeria - ZUPAN
(ZUMUNCI)

12/06/2025

Jarrabawa Tana Zuwa da Daukaka

A rayuwa, jarrabawa wani abu ne da babu wanda ya tsira daga gare ta. Kowanne mutum – mai arziki ko talaka, matashi ko dattijo – yana fuskantar irin tasa jarabawar. Sau da yawa, muna kallon jarrabawa a matsayin azaba ko wahala, amma a gaskiya, jarrabawa hanya ce da Allah ke amfani da ita domin shiryar da bawanSa zuwa daukaka.

Idan muka duba tarihin annabawa, za mu ga cewa sun fuskanci manyan jarrabawa, amma a ƙarshe sun samu matsayi mai girma. Annabi Yusuf (A.S) ya tsinci kansa a cikin ramin ƙasa da kurkuku, amma daga bisani ya fita ya zama shugaba a Masar. Annabi Ayyub (A.S) ya yi fama da cuta da talauci, amma ya jimre, sai Allah ya ba shi lafiya da dukiya fiye da wadda ya rasa. Wannan yana nuna cewa jarrabawa ba sharri ba ne, illa dai tana da manufar Allah.

A rayuwarmu ta yau ma haka abin yake. Wani zai rasa aiki, wani zai rasa iyali, wani zai gamu da tozarci ko tozarta – amma idan muka yi haƙuri da dogaro ga Allah, zamu ga wannan jarabawar na kawo mana sauyi da daraja da muka fi tsammani. Lokacin da Allah ke son daukaka bawa, yana fara jarrabta shi – domin ya tsarkake zuciyarsa, ya gyara halayensa, kuma ya nuna kwarewarsa cikin jimrewa.

Wani lokacin jarrabawa na zuwa ne domin fitar da ƙarfin da ke cikinmu wanda mu kanma ba mu sani ba. Tana koya mana tawakkali, haƙuri, da godiya. Tana hana mu izgilanci rayuwar wasu, domin ta nuna mana cewa kowa na da nashi gwagwarmaya. Kuma tana sa mu fahimci cewa ni’ima da daukaka ba sa zuwa da sauƙi – sai da gwaji.

Ka tuna: ba don wahala ba da Yusuf ya zama shugaban Masar. Ba don jimrewa ba da Ayyub bai sami lafiya da arziki ba. Idan kana cikin jarrabawa a yau, kada ka ji rauni. Ka dage, ka yi haƙuri, ka roki Allah, ka kuma san cewa daukaka na gab da zuwa. Jarrabawa ba ƙarshen rayuwa bace – wata hanya ce zuwa ga sabon mataki.

-✍🏾

11/06/2025

ZUMUNCI is loading..........
(ZUMUNCI)

10/06/2025

In Sha Allahu ZUMUNCI Yana nan tafe kamar yadda aka Saba, Chairman Maishaq Muhammad yace a sanar da Duka Members zumunci is Loading........
(ZUMUNCI)

10/06/2025

Hadin Kai , Da Zumunci 🤩👏💖

08/06/2025
06/06/2025

Muna ADDUA, Allah ya karbi Ibadummu Allahumma Amenn ya hayyu ya Qayyum (ZUMUNCI)

06/06/2025

Muhimmancin Yin Aboki Nagari.

Idan 'Yan Aljannah Sun Shiga Aljannah,
Kuma S**a Ga Cewa Ba Su Ga Wasu Daga Cikin Abokansu Na Nan Duniya Ba, Za Su Tambayi Ubangiji SWT Game Dasu.

Za Su Ce: "Ya Ubangiji SWT! Ina Abokanmu, Masoyanmu Su Wane Da Wane? Mun Kasance Muna Yin Sallah Da Azumi Tare Da Su A Duniya. Yaya Ba Mu Gansu A Nan Ba?".

Nan Take Sai Ubangiji SWT Ya Umurci Mala'ikunsa Su Je Cikin Wuta Su Zaga Su Fitar Da Duk Wanda Yake Da Imani A Zuciyarsa Koda Misalin Kwayar Zarra Ne.

Imam Hasanul Basary (R.T) Ya ce: "Ka Yawaita Abokanai Mutanen Kirki A Duniya. Domin Za Su Yi Ceto A Gare Ka Ranar Alkiyamah. Cikakken Aboki Shine Wanda Zai Yi Maka Dalilin Shiga Aljannah Idan Ya Samu Dama".

Ibnul Qayyim Aljauziyyah Yana Kuka Yana Fad'aWa Almajiransa Cewa: "Don Allah Idan Baku Ganni Atare Daku A Gidan Aljannah Ba, Ku Yi Tambaya Game Da Ni.

Ku Ce "Ya Ubangiji SWT Akwai Wani Bawanka Wanda Ya Kasance Yana Tunasar Da Mu Game Da Kai …(Sai Ya Sake Fashewa Da Kuka).

Allah Yasa Mudace Da Abokanai Na Kwarai
Wadanda Zasu Samu Shagala Cikin Lammuran
Ubangiji SWT, Aameeen.
(ZUMUNCI)

Want your school to be the top-listed School/college in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Address

Http://m. Facebook. Com/profile. Php?¡d=405840712818616
Kaduna
ZUMUNCIPEOPLE'SASSOCIATIONOFNIGERIA(ZUPAN)