25/01/2025
BILKIN SAMBO TA MAMMAN SHATA
Ana yi wa Dr Mamman Shata kirari da:
"Sarkin wakar Kanawa, Duna na Bilkin Sambo. Warga-wargan namiji Mai daci k**ar bula..."
Wai shin Bilkin Sambo, matar sa ce, ko kuma k'anwar sa ce? Kuma meye tsakanin su da Yalwa?
Wannan ita ce tambayar da Fatuhu ya yi a Majalisar Marubuta kwanan nan. Ni kuma na ba shi amsa k**ar haka:
Malam Fatuhu, lallai ka yi tambaya ga d'an gida. Tambayoyin ka su ne:
1. Wai shin Bilkin Sambo, matar Shata ce, ko kuma k'anwar sa ce?
2. Kuma meye tsakanin su da Yalwa?
BILKIN SAMBO
Wata mata ce a garin Funtuwa, Jihar Katsina, wato garin da Shata ya yi rayuwar sa, inda iyalin sa su ke. A farkon zuwan Shata Funtuwa, bayan ya taso daga Bakori (wanda shi ma gari ne kusa da Funtuwa) sai su ka shak'u da Alhaji Nagoya, wani d'an kasuwa mai cinikin auduga. Nagoya ya d'auki Shata k**ar d'an sa. Don haka ne ya had'a shi da wasu 'ya'yan sa biyu mata, Indon Dutsen Reme da k'anwarta Bilki.
Akwai kuma Sambo, wanda shi ne babban d'an Nagoya d'in. San da duk aka yi haihuwa a gidan Alhaji Nagoya, ya kan kirawo Shata ya ce, "Ga uwargida!" ko "ga ubangida na yi maka!"
Da aka haifi Bilki, Shata ya na makad'in gidan, sai maigidan ya ce masa, "To ga sabuwar uwargida na yi maka."
Daga nan ne ita Bilki, wadda akan kira Bilkin Sambo, ta zama Bilkin Shata, sa'annan shi ma Shata ana ce masa Na-Bilkin Sambo (har marokan sa su kan yi masa kirari da "Mai tambura Na- Bilkin Sambo!").
Abin mamaki, Shata bai yi Bilki waka ba (a iya sani na), amma kuma ya wak'e Indo da wakar "Indon Dutsen Reme Lambawan."
A yanzu ita Indo ta na auren Magajin Garin Musawa, Alhaji Abdullahi Inde. Ita kuma Hajiya Bilki, ta nan da ran ta a Funtuwa, inda ta yi aure har ta hayayyafa. Ga hoton ta nan tare da d'an ta (amma tsohon hoto ne, domin na ke jin kila ma wannan yaron ya girme ka!)
2. YALWA
Akwai Yalwa guda biyu a rayuwar Shata. Ta farkon ita ce kanwar sa mai bi masa, wadda ta rasu tun tuni. A garin su Musawa ta yi aure, har ta haifi d'a wanda ake kira Umbaje (ka san ana yi wa Shata kirari ana cewa "Uban Umbaje").
Yalwa ta biyu kuma ita ce Hajiya Yalwa Bature, wadda matar sa ce da ya fi so a rayuwar sa. Sun dad'e da rabuwa, har ta auri marok'in sa Alhaji Bature Sarkin Magana (wanda shi ma ya dad'e da rasuwa, tun kafin Shata ya rasu). Hajiya Yalwa ta na nan zaune a Kaduna tare da 'ya'yan ta, cikin su har da 'ya'yan da su ka haifa da Shata (Umma, matar Kanar Bala Mande wanda ya tab'a yin gwamna a zamanin Abacha, kuma ya yi ministan Obasanjo), da Bilkisu Shata wadda d'aliba ce a fagen Political Science a Jami'ar Abuja, da kuma Nura).
Da ka ji ana kiran Shata, "Shata na Yalwa", to k'anwar sa din nan ake nufi, ba matar ba, domin tun kafin ya auri Yalwa ake ce masa hakan.
Da fatan ka gamsu.
DAGA BAHAUSHE MAI BAN HAUSHI
-IBRAHIM SHEME