Sunnah Network Kaduna STATE

Sunnah Network Kaduna STATE

Share

ILMANTARWA DA FADAKARKAWA

24/02/2022

Assalamu'Alaykum

Tambihi*****

Yakai dan uwa shin kataba tunawa da laifin aibanta ko tazarta dan uwanka kuwa
Shin kasan hukuncin da Allah Ta'ala yatanadarwa duk wanda zai kasance yana mai tozarta ko aibanta dan uwanshi

Mai tozarta ko aibanta dan uwanshi inda Allah ta'ala yayi kaman ceceniya da laifinshi shine kamar ace mutum yasadu da mahaifiyarshi, Fa innalillahi wa inna Ilaihi Rajiun, Wana'uzubillahi minhazal fitna

Yakai dan uwa wanda kamaita tozarta dan uwanka ba a bakin komai ba

Yakai dan uwa wanda kamai da cin mutuncin dan uwanka ba a bakin komai ba

Har jira kake kaganshi ya aikata wani laifi tsakaninshi da Allah kaikuma zaka dauka kazo kana yadashi a duniya idon jama'a kana aibantashi da laifin da ya aikata daga shi sai Allah

Muyi hattara fa muyiwa kanmu fada muguji yawo da laifukan da yan uwan mu suke aikatawa wajan aibantansu
In har bazaka iya yimasu nasiha ba tohm kayi masa Addu'ah agiryiwa

Ya Allah kakara karemana imanin mu
Ya Allah kakara tabbatar damu akan yimaka cikakken biyayya

30/03/2021

Assalamu'Alaykum Warahmatullah wabarkatuh

Gaisuwa tare da fatan Alkhairi

Inasan inyi amfani da wannan daman wajan jan hankalin mu wajen kiyayewa a kan wadansu abu buwa

Sau da dama munkasance masu aibanta yan uwan mu wajan zagi cin mutunci tozarci da sauransu

Yana da kyau musani aibanta dan uwanka ko cin mutuncin dan uwanka ko tozartashi laifine babba ko da kuwa ka aibanta shi akan laifin da yake aikatawa ne

Da yawa mutanen mu munfada wannan musibar ta aibanta junan mu da cin mutuncin junan mua har mun maidashi fashion

Zakaga Aboki ya tozarta a bokinshi ko yaci mutuncin shi a cikin jama'a ko Abokai sai kaga anfashe da dariya, wannan ba dae dae bane

Kar kasake kazama mai aikata haka ko da kuwa da wasane laifine babba ka tozarta dan uwanka musulmi

Sannan jan hanakalina zuwa ga masu madafin iko masu mukamai kar kasake aikin yasaka karinga ganin kai kafi kowa

Kada kasake matsayi ko mukami ya rude ka ko yarufe maka ido kamanta da yan uwanka kokuma asalinka

Watarana ba kai bane a wannan wurin kafin kazo anyi wasu da yawa yanzu basa nan wasu sun mutu wasu kuma suna raye amma basu da abin cewa sai dae kallo

Dan haka muyi kan mu fada mu gyara halayyan mu mu kyautatawa yan uwan mu

Mu tausayawa na Qasa damu

Ya Allah kakara tabbatar damu akan yi maka cikakken biyayya

Ya Allah kakara shiryar damu akan hanya ma dae daeciya

Ya Allah kakara karemu da kariyarka

06/10/2019

Wata Rana Manzon Allah SAW ya Shiga Cikin Masallaci sai ya ga wani Mutumin Madina ana ce Masa Abu Umamah, Sai Annabi SAW yace dashi; *(Yaa abaa Umamah Meyasa na ganka a zaune a Masallaci yanzu alhali ba Lokacin Sallah bane)* Sai Wannan Mutumin Abu Umamah yace: "Ya Manzon Allah Ina cikin damuwa da 'Kuncin rayuwa ga kuma bashi yayi min yawa na rasa yadda Zanyi"

Sai Manzon Allah SAW yace; *( Shin in Koya Maka abinda zaka Karanta Allah ya Yaye maka damuwar ka ya biya maka bashin ka)* Sai Yace "Ehh Ya Manzon Allah"

Sai Manzon Allah SAW yace; (Idan Ka Wayi gari Ko yammacu Kayi ta Karanta Wannan ba adadi
*(اللهم إني أعوذ بك من الهمّ والحزن وأعوذ بك من العجز والكسل وأعوذ بك من البخل والجبن وأعوذ بك من غلبة الدين وقهر الرجال)*

Sai Wannan Sahaibi yace "Sai naje na aikata hakan Wallahi da nayi tayi Sai gashi Allah ya Yaye min damuwa ta ya bani Mafita a 'kunci rayuwa ya Kuma h**e min hanyoyin samu har na biya bashi na."

*Hadithin Abu Sa'eed Alkhudreyy Wanda Abee Dawud ya ruwaito a Sunan (1555)*

Mafita ga Wanda Shiga damuwa shine kawai ya koma ga Allah, babu amfanin yawaita fadawa Mutane domin Wani dadi yake ji ya ganka cikin Matsalolin rayuwa.!!! Sai kadan Wanda zasu tayaka da addu'ah da roka maka Allah Mafita irin Wannan Mutanen kuwa da zasu Maka addu'ah tsakani da Allah ko ka rike su da kyau domin ko bayan mutuwarka sune zasu ta Maka addu'ah yayinda Kake kwance a Qabari.

# faroouQ..

23/01/2019

GAGARUMIN WA'AZI A KADUNA


A Madadin Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa'iqamatis Sunnah reshen Jihar Kaduna Tana farin Cikin Gayyatar Yan'uwa Muslimi Zuwa Gagarumin Wa'azi Wanda Kungiyar Izala ta Jiha ta shirya Karkashin Jagorancin Shugabannin Kungiyar Izalar ta Jihar Kaduna,

Alh. Muhammad Tukur Isah
(Shugaban Kungiyar Jibwis Kaduna)

- *Sheikh Imam Aliyu Abdullahi Telex Zaria
(Shugaban Majlisar Malamai ta Jiha)

- *Alh Adamu ibrahim*
(Daraktan Yan Agaji ta Jiha)

Wanda Inshaa Allahu Wa'azin zai gudana da yardan Allah kamar haka;

1- *NA MATAN AURE*

>Ranar : *Juma'ah 18/05/1440, 25/01/2019*
> Lokaci: *Karfe 9:30 na safe*
> Wuri: *A filin idi na Mai Ruwan Tanki, Rigasa. Kaduna*

2- *NA MAZA*

>Rana: *Juma'ah 25/01/2019*
>Lokaci: *Bayan Sallar Magrib*
> Wuri: *Masallacin Sultan Bello, Kaduna*

3- *NA MATAN AURE*

> Ranar: *Asabar 26 /1/2019.*
> Wuri: *Masallacin Yan Izala a Unguwar Kawo Kaduna*
> Lokaci: *Karfe 9:30 na safe*

Kadan daga Malamai Masu Wa'azi;

- *Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau*
(Shugaba Kungiyar Jibwis na kasa)

- *Sheikh Yakubu Musa Kastina Sautis-Sunnah*
- *Sheikh Dr. Muhammad Kabiru Gombe*
- *Sheikh Dr. Mansur Ibrahim Sokoto*
- *Dr Abubakar Sani Birnin Kudu*
- *Sheikh Aliyu Telex Zaria*
- *Sheikh Jamilu Abubakar Albani Samaru Zaria*

- *Alaramma Ahmad ibrahim Sulaiman Kano*
- *Alaramma Nasiru Saluhu Gwandu*
- *Alaramma Salisu Unguwan Kanawa*
- *Alaramma Isma'il Imani*

+ *Da Sauran Malamai da Alarammomi Masu yawa.*

- Babban Mai Masaukin Baki -
*Mal Nasiru Ahmad El-rufa'i*
(Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna)

- Babban Bako -
*(Mallam Uba Sani)*

- Masu masaukin Baki -
(Kakakin Majalisar Dokokin Jahar kaduna)
*Hon. Aminu Abdullahi Shagali*

- *Yan Majalisun Tarayya da na Jihohi da Shugabannin Kanan Hukumomin K/North, K/South, Igabi.*

Allah ya bada ikon zuwa Amin

- Sanarwa daga Sakataren Yada Lababari na Jiha
*Imam Nuradeen Mujahid*

*Jibwis Social Media*
*Kaduna State*
16.01.1440
23.05.2019

11/12/2018

Kayi sani yakai dan uwa baka da wani aikin yi aduniya da yawuce kabautawa Allah shi kadae

Kada ka hadashi da wani wajan bauta

Hakika Allah mai hakuri ne kuma yana san masu hakuri

Kar kayi la'akari da matsayi ko mukamin da kasamu a rayuwarka har yakai ka ga girman kai da nuna kai kafi wani

Kasani cewa Allah ya halicce mu gaba daya kuma daya muke a wajan Allah

Babu Wanda yafi wani sai Wanda yafi jin tsoran shi (Allah)

Ya Allah kabamu ikon bautata maka

Yq Allah kabamu ikon gujewa sabonka

Ya Allah kakara shiryar damu hanya madai daiciya

Muhammad Yusuf Kubau
Abu sudais
on Instagram

01 Sheikh Abdullahi Bala Lau - Wa'azin Kasa Konni 2018 - Muhadarori 16/10/2018

*WA'AZIN KASA 2018*

Complete Mp3 din Wa'azin Kasa kenan da aka gabatar a Konni Janhuriyar Niger.

01. Sheikh Abdullahi Bala Lau
👉http://darulfikr.com/s/56242

02. Sheikh Muhd Kabir Haruna Gombe
👉http://darulfikr.com/s/56243

03. Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
👉http://darulfikr.com/s/56244

04. Sheikh Abubakar Gero Argungu
👉http://darulfikr.com/s/56245

05.Sheikh Sani Ashir Kano
👉http://darulfikr.com/s/56246

06. Sheikh Yusuf Abdulwakil Al-Infaq
👉http://darulfikr.com/s/56247

07. Sheikh Saminu Ali Aqidah
👉http://darulfikr.com/s/56248

08. Sheikh Abubakar Garba
👉http://darulfikr.com/s/56249

09. Sheikh Abdulmumini Zinder
👉http://darulfikr.com/s/56250

10. Sheikh Ibrahim Muhammad
👉http://darulfikr.com/s/56251

11. Sheikh Abdurrahim Shu'aib
👉http://darulfikr.com/s/56252

12. Sheikh Mustapha Abubakar
👉http://darulfikr.com/s/56253

13. Sheikh Jamilu Yusuf
👉http://darulfikr.com/s/56254

14. Sheikh Buhari
👉http://darulfikr.com/s/56255

15. Sheikh Isma'il Maradi
👉http://darulfikr.com/s/56256

16. Sheikh Saminu
👉http://darulfikr.com/s/56257

17. Sheikh Sanusi Abubakar
👉http://darulfikr.com/s/56258

18. Sheikh Sulaiman Bonfery
👉http://darulfikr.com/s/56259

*Ayi sauraro lafiya*

Darulfikr.com Ta kuce Domin Yada Sunnah.

*_© JIBWIS KATSINA_*
_7 Safar, 1440.Ah_
_16 October, 2018.Ac_

01 Sheikh Abdullahi Bala Lau - Wa'azin Kasa Konni 2018 - Muhadarori -

31/07/2017

DAILY REMINDER:

▫ بِسْمِ ٱللهِ ٱلرَّحْمٰنِ الرَّحِيْم ▫

KALIMAH TAYYIBAH:

The Believer & his Faith:

Allah Subhanahu wa Ta'ala says (Qur'an Translation) : The believers are only those whose hearts tremble with fear whenever Allah is mentioned. And when His verses are recited to them, these increase their faith; and in their Rabb (Sustainer) they vest their trust.
(Al-Anfal 8: 2)

11/05/2017

Ni Muhammad Yusuf Kubau bana gaba da kowa sabida manzon Allah yayi hani a kan hakan

Sannan bana hassada wa kowa sabida manzon Allah yace mai hassada, hassadan tana cinye kyawawan ayyukan shi kamar yadda wuta take cin audiga

Bana zagin kowa sabida manzon Allah yace zagin musulmi faskincine

Haka kuma bana tozarta kowa sabida Allah yayi hani a kan hakan

Toh yakai Dan uwa mai aikata wadannan ayyukan wallahi yakamata kayi kanka fada kayiwa kanka karatun ta natsu

Kasami duk Wanda kasan kaci mutuncinsa KO ta aibantawa KO ta zagi ko ta hanyar tazartawa wallahi kaje kanaimi tubanshi sannan kanai mi tuban Allah

Yakai dan uwana mai Albarka kazama mai kyautata mu'amalar Ka da mutane har tsakanin Ka da ubangijinka

Ya Allah kakara mana hakuri da juriya

Ya Allah kakaraman kariya daga sharrin dukkanin wani mai sharri

Ya Allah kakara karemu daga sharrin shethan (La'ana tullah)

Muhammad Yusuf Kubau
Abu Sudais
on Instagram

04/04/2017

Tambaya Ta 12: Mene ne Ma’anar watan Rajab?

Daga Littafin Zararren Takobi akan Bidi’o’in Shekara.

Wallafar: Sheik Abdulwahab Abdallah (Imamu Ahlussunnah Wal’jama’ah).

Yadawa: Cibiyar Bn Baaz Islamic Foundation.

Tambaya Ta 12: Mene ne Ma’anar watan Rajab?
Amsa:
Mafi yawan Malaman Luga sun ce: Kalmar “Rajab” a harshen larabci, tana karvar canje-canje, misali; idan aka ce “Rajaba” to, an tsagota ne daga:
رَجَبَ الرَّجُلَ رَجَبًا، وَيُرَجِّبُهُ رَجَبًا وَرُجُوبًا.
Kuma dukkaninsu suna nufin ganin girman mutum da kwarjininsa.
Watan Rajab yana da sunaye da yawa, amma ga kaxan daga cikinsu.
أ- شهر رجب Watan Rajab
An ambace shi da wannan suna ne saboda mutanen jahiliyya su na girmama shi.
ب- شهر الأصم Kurman Wata
Saboda ba a jin sautin kayan faxa da sautin neman agaji a cikinsa.
ج- شهر الأصب Watan Kwarara
An ambace shi da wannan suna ne saboda Quraishawa su na riya cewa Rahamar Allah tana kwarara a cikinsa.
د- شهر الرجم Watan Jefewa
An ambace shi da wannan suna saboda Quraishawa su na riya cewa wata ne da ake jefe shaixanu a cikinsa.
هـ- الهرم Daxaxxe
An ambace shi da wannan suna saboda kasancewarsa watan da aka daxe ana girmama shi tun a zamanin Mudar Ibn Nizar.
و- المقيم Tsayayye
An ambace shi da wannan suna saboda alfarmarsa tabbatacciya ce.
ز- المعلي Maxaukaki
Sun ambace shi da wannan suna saboda mutanen Jahiliyya su na xaukaka shi fiye da kowane wata.
ح- المبرىء Kuvutacce
Sun sanya masa wannan suna ne saboda wanda bai yi zalunci a cikinsa ba, to, ya kuvuta daga zalunci da munafunci.
ط- شهر العتيرة Watan Yanka
Sun sanya masa wannan suna ne saboda su na yanke-yanke na neman kusanci ga Allah da gumakansu a cikinsa.
ي- رجب مضر Watan Qabilar Mudar
An danganta shi zuwa ga qabilar Mudar ne saboda su ne s**a fi girmama wannan watan fiye da sauran Larabawa..

15/02/2017

*Daily Hadith*:
*18th Jumada al-Awwal 1438*
(15th February 2017)

```Bismillah Walhamdulillah Was Salaatu Was Salaam 'ala Rasulillah```

Narrated 'Abdullah bin 'Umar (Radi-Allahu 'anhu):

The Prophet (Sallallahu 'Alaihi Wa Sallam) said, "Everyone of you is a guardian and everyone of you is responsible (for his wards). A ruler is a guardian and is responsible (for his subjects); a man is a guardian of his family and responsible (for them); a wife is a guardian of her husband's house and she is responsible (for it), a slave is a guardian of his master's property and is responsible (for that). Beware! All of you are guardians and are responsible (for your wards)."

```Bukhari Vol. 7 : No. 116``` 📚

*Ma'asalaam*

*Sabahul khair*
*صباح الخير*

06/10/2016

INNA LILAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

WAI YANZU HAKA RAYUWAR TAKOMA ????

Jiya da daddare ina saurqran Radio nasami wani labari wanda yatayar min da hankalin sosai

jiya nasmi labarin wai ankama wani bawan Allah a masallaci yana saduwa da yaro dan shekara 10

wa iyazubillah

kai wannan ma ba komai bane a kan na wannan shikuma ankama wani bawan Allah dan shekara 27 yayiwa yarinya 'yar shekara 2year biyu a duniya fyade

fa inna lillahi wa INNA ilaihi raji'un

wai yanzu haka rayuwar mu zata kasance ??

shin wai bama tuna cewa zamu mutu mukoma ga Allah ??

Shin yanzu kai zaka so a ce kanwarka a kayiwa haka ??

Sannan wani abun ban haushi ma wadannan mutanen da s**a aikata wannan laifin bawai daga kudancin Nigeria s**a fito ba

anan Arewacin mune abin yafaru Arewar ma wai a cikin wannan gari mai Albarka Kaduna a cikin kadunan ma Anguwar Hausawa (Rigachikun)

Fa iyazubillah

yanxu shin bama tunannin yadda wannan rayuwar tamu take ne ??

Yanzu bama ganin halin jarabawan Da Allah yamana ne nashiga wani yanayi na tabar barewan harkoki ga rashin lapiya ??

Ya Allah ka kara karemana imanin mu

Ya Allah kakara karemu daga sharrrin abokan banza

Ya Allah kakara karemu daga sharrin shethan

Ya Allah sukuma wadanda suke aikata wannan halin kasan su kasan suwaye su

Ya Allah I masu shiryuwane Allah kashirye su

ina ba Masu shiryuwane ba ya Allah ka tsine masu

Ya Allah ka la'ance su

Ya Allah ka yimasu nau in azabar da kayi wa mutanen Annabi {LUD (A.S)}

Ya Allah Gamu gareka bamu da wa yau ko dabara kai kadai ne mai hukunci a kan dukkan wanda ya kaucewa umarninka

Ya Allah kakara shiryar damu a kan tafarkin manzonka Annabi Muhammad (S.A.W)

Muhammad Yusuf Kubau
Abu sudaia
1438Ah. /2016.

23/09/2016

ALLAH SARKI !!! 001

Ina zaune sai nayi wani dogon tunani a cikin zuciyata

Naga nakasance ina yawan hawa online inayin wasu rubutu kuma ina share na rubtun wasu daga malamaina

Sai naga cewa yanxufa wataran bazanyi wannan rubutun ba ko share din da nakeyi

Nakasancr idan naji Rasuwa na dan uwa kokari nakeyi wajan sanarwa jama'a dan sanyashi a cikin addu'a

Sai naga watarana nawa sanarwan za ayi dan naimamin addu'a
Sabida lokacin nabar duniyar

Yawan hawa online babu shi daga wannan ranan

Yawan posting da sharing shima daga wannan lokacin babu shi

Zan kasance offline babu wanda zai karajin labarina sai wanda mayi mu' amula ta Alkhairi dashi

Babu Wanda zai karajin labarina sai wanda nataba zaluntarshi ko na cutar dashi

Babu wamda zai tuna dani sai wanda mukayi zaman amana dashi

Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un

Yanzu haka rayuwa take yau kaine gobe ba kai bane

Ya Allah kasa muyi kyakkyawan karshe

Muhammad Yusuf Kubau
Abu sudais.

Want your school to be the top-listed School/college in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address

Kaduna