24/02/2022
Assalamu'Alaykum
Tambihi*****
Yakai dan uwa shin kataba tunawa da laifin aibanta ko tazarta dan uwanka kuwa
Shin kasan hukuncin da Allah Ta'ala yatanadarwa duk wanda zai kasance yana mai tozarta ko aibanta dan uwanshi
Mai tozarta ko aibanta dan uwanshi inda Allah ta'ala yayi kaman ceceniya da laifinshi shine kamar ace mutum yasadu da mahaifiyarshi, Fa innalillahi wa inna Ilaihi Rajiun, Wana'uzubillahi minhazal fitna
Yakai dan uwa wanda kamaita tozarta dan uwanka ba a bakin komai ba
Yakai dan uwa wanda kamai da cin mutuncin dan uwanka ba a bakin komai ba
Har jira kake kaganshi ya aikata wani laifi tsakaninshi da Allah kaikuma zaka dauka kazo kana yadashi a duniya idon jama'a kana aibantashi da laifin da ya aikata daga shi sai Allah
Muyi hattara fa muyiwa kanmu fada muguji yawo da laifukan da yan uwan mu suke aikatawa wajan aibantansu
In har bazaka iya yimasu nasiha ba tohm kayi masa Addu'ah agiryiwa
Ya Allah kakara karemana imanin mu
Ya Allah kakara tabbatar damu akan yimaka cikakken biyayya