24/05/2026
Hukunce-hukuncen Layya
Tunkiya/Rago — wata 6
Bunsuru/Akuya — shekara 1
Sa/Saniya — shekara 2
Raƙumi — shekara 5
Lokacin Yankan Layya
Lokacin da ya halatta a yanka layya yana farawa ne bayan sallar Idi a ranar 10 ga Zul-Hijja (Ranar Sallah), har zuwa faduwar rana a ranar 13 ga Zul-Hijja.
Siffofin Layya
✅ Ta kasance lafiyayyiya ba tare da nakasa ba
✅ Ta kai shekarun da Shari’a ta gindaya
✅ Ta kasance mai ƙiba, ba rame ba
Tunatarwa ga Muminai
23/05/2026
Kwanaki Goma Masu Albarka: Hajji, Arfa Da Layya
Khudubar Sallar Juma’a
Tare da Sheikh Adam Mahmud Sharada
Masjid Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Sharada
A cikin wannan khuduba mai albarka, Malam ya yi bayani kan falalar kwanaki goma na farkon Zulhijja, muhimmancin aikin Hajji, darajar Ranar Arfa, Sallar Idi da kuma falalar Layya tare da yadda ake gudanar da ita bisa koyarwar Musulunci.
22/05/2026
Muna cikin ranar Juma’a, kuma a cikin kwanaki goma mafi falala na watan Zul-Hijjah — kwanaki masu albarka da Allah Ya fifita akan sauran kwanaki.
Wannan rana mai girma cike take da damarmaki ga masu ibada, masu tuba, masu zikiri da masu roƙon Ubangiji. Lokaci ne na neman gafara, yawaita salati ga Annabi ﷺ, addu’a, sadaka da sauran ayyukan alkhairi.
Kada mu bari wannan rana ta wuce ba tare da mun kusanci Allah da ayyukan da suke jawo rahama da amsa addu’a ba. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya biya mana bukatunmu na alkhairi duniya da lahira. 🤲
15/05/2026
Khudubar Sallar Juma'a
Mai Taken Ni’imomin Rukunan Musulunci Sallah, Azumi, Zakka Da Hajji
Tare Da Sheikh Adam Mahmud Sharada