PRESS STATEMENT BY THE SUPREME COUNCIL FOR SHARI’AH IN NIGERIA (SCSN) ON ALLEGED DISCREPANCIES IN THE GAZETTED TAX REFORM BILLS
The Supreme Council for Shari’ah in Nigeria (SCSN) has followed with deep concern developments on the floor of the National Assembly yesterday, where Hon. Abdulsamad Dasuki, a duly elected member of the House of Representatives, raised an alarm over disturbing discrepancies between the tax reform bills passed by the National Assembly and the versions subsequently gazetted and presented to the Nigerian public.
The Council notes with utmost seriousness the allegation that additional clauses and other substantial material alterations appearing in the gazetted tax laws signed by the President were neither debated nor approved by the National Assembly. If established, this represents a grave and egregious constitutional infraction with far-reaching implications for democracy, governance, economic stability, and public trust.
Given the profound impact of tax legislation on the lives, livelihoods of ordinary citizens, businesses, and religious, social, and economic obligations of Nigerians, the Supreme Council for Shari’ah in Nigeria actively monitored and contributed immensely throughout the legislative process of considering these tax reform bills at the National Assembly. Our engagements were guided by the need to ensure fairness, equity, transparency, constitutional compliance, and protection of the public interest.
The Council is therefore shocked and deeply disturbed by allegations on the floor of the House of Representatives that what Nigerians collectively debated, scrutinised, and agreed upon through their elected representatives may have been altered at the executive level. Such action, if established ,tantamounts to tampering with the sovereign will of the Nigerian people and undermines the very foundation of constitutional governance.
Accordingly, we hereby call on all stakeholders, in particular, the leadership of the National Assembly - the Speaker of the House of Representatives, Rt. Hon. Tajuddeen Abbas, and the President of the Senate, Senator Godswill Akpabio to rise to their constitutional responsibilities by ensuring that these claims are transparently examined and appropriate actions taken before the commencement of the Tax Laws, on the 1st of January, 2026. Nigerians deserve respect, transparency, and fidelity to due process. Members of the National Assembly must be allowed, without hindrance, to conduct a critical, open, and transparent comparison between the harmonised bills passed by both chambers and the versions that were eventually gazetted, in order to establish the nature, extent, and impact of any alterations.
The consequences of such alleged infractions are grave. They include erosion of public confidence in democratic institutions, weakening of the doctrine of separation of powers, exposure of the affected laws to constitutional challenges, economic uncertainty, and loss of investor confidence. Most critically, they set a dangerous precedent where laws become negotiable instruments rather than binding outcomes of democratic deliberation.
Tax laws, by their compulsory nature, demand the highest level of constitutional integrity and procedural fidelity. Nigerians cannot be expected to comply with fiscal obligations arising from laws whose authenticity and legislative origin are in doubt. The Council therefore urges that this matter be treated with urgency, sincerity, and transparency in order to preserve constitutional order, protect institutional credibility, and reaffirm the supremacy of the Nigerian Constitution.
Nigeria’s democracy must not be undermined by executive overreach or procedural shortcuts. The will of the people, as expressed through the National Assembly, must be respected and defended.
Signed:
Nafiu Baba-Ahmad, mni
Secretary General
Supreme Council for Shari’ah in Nigeria (SCSN)
27 Jumada II 1447 AH/ 17 December 2025
Daarul Huffaz Lit-tatbiq Shanono Rigasa Kaduna
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Daarul Huffaz Lit-tatbiq Shanono Rigasa Kaduna, Education, Turaki Road Shanono, Kaduna.
26/11/2022
Muna gayyatar kowa da kowa.
17/08/2022
INNAA LILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UN
Allah yayi wa Imam Murtala Jibril, Limamin Masallacin Khalid Bn Al-Waleed Rasuwa, kuma Na'ibin Limamin Masallacin Juma'a na Kaduna Polytechnic dake Tudun Wada, Kaduna.
Jana'iza gobe Alhamis 20 Muharram, 1444 (18/08/2022) a Masallacin Khalid Bn al-Waleed, dake bye-pass, Kaduna.
Da karfe 9:00 na safe.
Allah ya gafarta ma sa kurakuran sa.
05/08/2022
Nasiha a Takaice
✍️ Prof. Mansur Sokoto, mni
Maimaitawa daga Rubutun 3 Rajab 1442H (15/02/2021)
Yafiya:
Ibnu Hibban _rahimahullah_ ya ce: "Abinda yake wajibi a kan mai hankali idan dan uwansa ya neme shi yafiya a kan wani laifi da ya yi masa ko wata kasawa da ta bayyana daga wurin sa, ya karbi uzurinsa, ya yafe laifinsa, ya mayar da abinda ya wuce a baya k**ar ba ayi ba".
📚 Raudhatul Uqalá', Shafi na 183.
29/07/2022
Barkan mu da Juma'a, Allah ya sa mu dace da dukkan Alkhairin dake cikin wannan rana.
22/07/2022
HADISIN YAU NA ( 71)
(WANDA ALLAH YA FI SO A CIKIN MUTANE.)
MANZON ALLAH (SAW) YACE : WANDA ALLAH (TA'ALA) YA FI SO A CIKIN MUTANE, SHI NE WANDA YA KE AMFANAR MUTANE
FA'IDA
WANNAN HADISI YANA KOYA MANA MU ZAMA MASU AMFANAR MUTANE TA KO WACCE HANYA,
AMFANIN DUNIYA DA LAHIRA.
DUK WANI TAIMAKO DA ZA KA IYA,
DA DUK WATA DAMA DA ALLAH ( TA'ALA) YA BAKA KA YI, AMFANI DA ITA KAFIN TA ƘARE WAJAN AMFANAR DA JAMA'AR ANNABI (SAW).
DUK WATA HANYA DA ZA KA BI WAJAN ƘARE CUTA DA CUYARWA GA AL'UMMA KA YI ZA KA ZAMA CIKN WAƊANDA ALLAH TA'ALA YA KE SO.
MAI KAKE YI WANDA AL'UMMA TAKE AMFANUWA DA KAI.?
20/07/2022
AL-GHADIR:
KALUBALE GA ‘YAN SHI’A
✍ Prof. Dr. Mansur Sokoto , mni
18/12/1434M
22/10/2013M
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
INGANTACCEN LABARIN GHADIR:
Ma’anar Ghadir:
Kalmar Ghadir a larabce, tana nufin wurin da ya tara ruwa da ciyawa.
“Ghadir Khum” sunan wani tafki ne da yake a yankin Juhfa, kilomita 15 daga Rabigh. Nisan sa daga Makka kilomita 160 ne.
Labarin Ghadir:
Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aiki Khalid dan Walid a matsayin kwamandan rundunar da za ta yi yaki a kasar Yaman daf da fara aikin Hajjin shekara ta 10H, hajjin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kansa ya jagoranta.
Bayan da rundunar musulmi ta ci nasara sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aika Sayyidi Ali don ya kula da sha’anin Ganimar da aka samu.
Ali Radhiyallahu Anhu ya raba Ganima, kuma ya cire hakkin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam na Khumusi k**ar yadda Alkur’ani ya zayyana. Daga ciki kuma ya cire ma kansa wata kuyanga da ta ba shi shawa.
Sayyidi Ali bai bata lokaci ba ya zarce zuwa Makka don ya riski maigidansa Sallallahu Alaihi wa Sallam a wurin aikin Hajji. Ya kuma wakilta wani daga cikin sojoji akan sauran aikin da ya rage.
Domin ya dadada ran sojojin, wakilin Sayyidi Ali ya raba ma su tufafi kyawawa daga cikin abin da aka ganimanto. Ya kuma yi ma su izini kowa ya hau rakumin da yake so daga cikin kayan Ganima. Kafin haka, sojoji sun gabatar da bukatar haka ga Sayyidi Ali amma bai amince ba. Sai ya ce ma su, rabonku sai an je Madina.
Sojojin wannan runduna sun hadu da Sayyidi Ali tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam a kan hanyar su ta dawowa bayan gama aikin Hajji. Sayyidi Ali ya nuna rashin jin dadinsa a kan wannan rabo da aka yi kafin lokacin yinsa. Nan take ya yi umurni duk su sauka daga rakuman, s**a kuma mayar da tufafin da aka raba masu. Rayukansu sun baci matuka a kan haka kuma sun kai karar sa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam suna zargin sa da cewa ya kuntata masu.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya iso Ghadir Khum, kuma ya lura da fushi a fuskar wadannan sojoji. Ya yi huduba yana tambayar su ((ألستُ أولى بالمؤمنين من أنفسهم))؟! “Ashe ban fi muminai cancanta da kawunansu ba?” S**a ce masa, haka ne. Sai ya ce, ((فمن كنت مولاه، فعلي مولاه)) “To, duk wanda nake majibincinsa Ali ma majibincinsa ne”. Ma’ana, bai dace ku bata ranku a kan hukuncin da ya yi ba.
Da wannan babban jagora ya kwantar da wannan rikici da rashin fahimta, ya kuma nuna wajabcin a yi ma jagora da’a, sa’annan ya bayyana matsayin dan uwansa Sayyidi Ali a wurin muminai. Sojojin s**a ba shi hakuri, s**a gane matsayinsa, s**a wuce Madina tare da sauran ayarin mahajjata da suke tare da shi.
Wannan shi ne abin da ya faru. Illa iyaka.
TATSUNIYAR GHADIR
‘Yan Shi’a sun ribaci wannan abin da ya faru kuma ya zo ya wuce k**ar sauran ire-irensa. S**a fank**a shi, s**a fadada shi, s**a mayar da shi wani gagarumin bukin nadin sarauta. S**a kuma jefi duk Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da kin Allah da kauce ma gaskiya, da jayayya da wannan nadi da s**a ce an yi.
Wannan akidar ta Ghadir a matsayin ranar buki ba a san ta a cikin tarihi ba sai bayan sama da shekaru 340 gwamnatin Shi’a ta Buwaihawa ta kago wannan bidi’a a kasar Iraqi. S**a mayar da ranar 18 ga watan Dhul Hajji a matsayin ranar wannan buki ta kowace shekara. S**an taru a wurin kaburburan manyansu suna ta kururuwa suna la’antar masoyan Allah wadanda s**a ce sun kauce ma umurni Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da ya bayar na mika mulki ga maigida Sayyidi Ali.
Sun kago ruwayoyi barkatai a kan falalar wannan rana, cikin su har da cewa wai, Imam Ar-Ridha ya ce, da mutane sun san matsayi da falalar wannan rana da Mala’iku sun rinka musafaha da su har sau goma a kowace rana.
Haka kuma sun kitsa tatsuniyoyi masu nuna wai, manyan Sahabbai sun yi ma Ali mubaya’a amma a munafurce, sannan s**a shirya makarkashiyar kashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam. A cikin su kuma wai har da duk sauran tara daga cikin mutane goma da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya yi ma su bushara da aljanna.
KALUBALE GA ‘YAN SHI’A
Muna kalubalantar ‘yan Shi’a a kan wannan batu da wadannan tambayoyi:
1. Idan wannan magana ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa “Duk wanda nake majibincinsa Ali ma majibincinsa ne” tana nuna wajabcin shugabantar da shi, to me za ku ce game da fadar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam “Ko wace al’umma tana da amintacce, mu kuma amintaccenmu a cikin wannan al’umma shi ne Abu Ubaida”? Wa ya fi cancanta a cikin su kenan?
2. Idan har gaskiya ne an yi wannan nadin k**ar yadda kuke cewa, me ya sa ba a umurci Sayyidi Ali da ya ci gaba da ba da Sallah ba musamman bayan da ciwon ajali ya k**a Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam?
3. Me ya sa ba ayi wannan bukin a zamanin da Sayyidi Ali yake Khalifa ba ko Sayyidi Al-Hasan ko a zamanin duk Imamanku goma sha daya da s**a rayu kafin Malam Na-boye (Mahadinku) ya zo duniya? Me ya sa sai lokacin da Buwaihi Bafarise mai kamun kifi ya kafa gwamnati sannan aka fara wannan buki a shekarar 352H?
4. Idan hudubar Ghadir tana nufin nadin sarauta ne, me ya sa ba ayi ta a Makka ba in da duk alhazan duniya s**a taru su sama da mahajjata dubu dari?
5. Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam bai yi hudubobi a can Makka da Minna da Arafat ba? Me ya sa bai ware huduba ta musamman a kan wannan babbar maganar ta halifancin Sayyidi Ali ba?
6. Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam bai yi huduba a kan jinainai da dukiyoyi a ranar babbar sallah ba? Ashe bai yi ma al’umma wasici da muhimman abubuwan da suke bukatar sani ba? Ita wannan maganar ba ta kai muhimmancinsu ba ne ya manta da ita? Me ya sa sai da aka watse, kowa ya bi hanyar garinsu saura mutanen Madina kawai s**a rage sannan ya yi wannan magana a cikin sunkurmin daji a tafkin Ghadir?
7. Ya ya aka yi Sahabbai s**a riwaito wannan hudubar ta Ghadir alhalin kun ce sun boye kaso biyu cikin uku na Alkur’ani masu bayyana falalar Ahlulbaiti?
8. Kun ce duk rikicin da musulmi s**a shiga a tsawon tarihi dalilin kauce ma wannan umurni na ranar Ghadir ne da sahabbai s**a yi. Me ya sa Alkur’ani ya yi biris da labarin Ghadir?
9. Allah Tabaraka wa Ta’ala ya saukar da sura ta musamman a cikin Alkur’ani kan maganar Hudaibiya da mubaya’ar da sahabbai s**a yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da har wuri da bishiyar da s**a yi mubaya’a a karkashinta, kuma ya ce ya yarda da su a kan haka bisa ga abin da ke cikin zukatansu na imani da ikhlasi. Kuma ya ce, a lokacin da suke yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam mubaya’a hannun Allah yana saman nasu. Me ya sa idan har an yi wannan mubaya’a Allah bai kawo ta ba a cikin Alkur’ani?
10. Mubaya’ar da mata s**a yi ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ita ma Allah ya kawo labarinta cikin Suratul Mumtahana. Shin ita wannan mubaya’ar ta Ghadir ba ta da muhimmanci ne irin wannan mubaya’ar mata ko kuwa?
‘Yan Shi’a ku ji tsoron Allah! Malamanku suna zargin Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam da boye wannan bayani wai a cikin Makka har suna cewa a kan wannan boyewar da ya yi sai da Allah ya saukar da ayar ”Ya kai wannan manzo ka isar da sakon da aka saukar ma ka daga wurin Ubangijinka. Idan kuwa har ba ka yi ba to, ba ka isar da sakonsa ba. Kuma Allah zai kare ka daga mutane”. To, sannan wai, ya tsaya a Ghadir Khum ya isar da wannan sako. Ku ji tsoron Allah! Ku darajanta manzonsa, ku koma ga gaskiya.
Wallahi, Sayyidi Abubakar da Sayyidi Umar da Sayyidi Usmanu da ma duk sauran sahabbai almajiran Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ba su jiye ma Sayyidi Ali da kome. Kuma ba su da wani kwadayi ga duniya b***e su nemi shugabanci. Allah Ta’ala da kansa cewa ya yi a kan su:
((للفقراء المهاجرين الذين أُخرجوا من ديارهم وأموالهم يبتغون فضلا من الله ورضوانا وينصرون الله ورسوله أولئك هم الصادقون))
“-A bayar da Fai’i- ga talakawa Muhajirai wadanda aka fitar da su daga gidajensu da dukiyoyinsu suna neman falala daga Allah da yarda, kuma suna taimakon Allah da manzonsa. Wadancan su ne masu gaskiya”
To, ka ji. An kore su daga garuruwansu, aka kwace dukiyarsu kuma a cikin zukatansu ba zaman gida ko mallakar dukiya ne a gabansu ba. Babban gurinsu shi ne taimakon Allah da manzonsa. Ka kuma ji Allah ya ce ma su masu gaskiya. Don Allah ta ina wadannan za su yi kwacen mulki kuma har su shirya ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam makarkashiyar kisan sa?!
Ya Allah! Ka shiryar da bayinka, ka ceto su daga muguwar akidar da Farisawa ‘yan bautar wuta s**a kago s**a lullube ta da rigar musulunci don su halaka su. Allahumma Ameen.
Sheikh Ibrahim Adam Almadanany ke gabatar da Muhadara na goron Sallah a Masallacin Juma'a dake Shanono Rigasa Kaduna.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
Kaduna