Wani Mao hazaka ne zai iya bamu
Amsan wannan
3×4+6=?
Mathematics A harshen Hausa
This is the place where you get to know Mathematics is really easy and fun.
"Barkanmu da wannan lokaci, ’yan’uwa masu albarka! Darasinmu na yau a lissafi shine: BODMAS. Ku kasance tare da mu don samun ilimi!"
BODMAS wata hanya ce da ke koya mana yadda ake bin tsarin warware matsalolin lissafi idan akwai haɗin ayyuka daban-daban kamar ƙari, ragi, ninkawa da dai sauransu.
BODMAS na nufin:
B – Brackets (abu cikin kame/kaka, a fara warware shi)
O – Orders (lamba mai iko kamar 2² ko √4)
D – Division (raba)
M – Multiplication (ninkawa)
A – Addition (ƙari)
S – Subtraction (ragi)
Muhimmin ka’ida: Idan akwai rabawa da ninkawa, ko ƙari da ragi, a warware su daga hagu zuwa dama.
*Misali:
Warware:
5 + (3 × 2) - 4
1. Fara da brackets:
(3 × 2) = 6
Yanzu ya zama: 5 + 6 - 4
2. Sannan a yi ƙari da ragi daga hagu zuwa dama:
5 + 6 = 11
11 - 4 = 7
Amsa: 7
A mafi yawan lokaci, abu na farko da zai taimaka maka/ki wajen fahimtar karatu shi ne kawar da tsoro ko shakka game da abin da kake/kike koya. Babu wani abu da ke da wahala sai dai wanda aka ɗauka a zuciya cewa shi ne mai wahala
Barka da zuwa shafin koyar da Lissafi(mathematics) a saukake🤗🤓
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the school
Telephone
Website
Address
Zaria
Kaduna