06/03/2023
Program: CUSTOMERS SERVICES
Day 1
Duration: 3days
Time: 9:00pm
Venue: Facebook (Murtala Abubakar &Alabeer Business School)
🛑GABATARWA
Kafin Mutsunduma zanso nayimaku wasu Tambayoyi Dan Allah ka amsasu kafin Kacigaba da karatu a kasan COMMENT BOX
1. A Fahimtarka menene Customer's service??
2. Shin zaka iya Tuna Yaushene Karshen Business dinda kayi siyayya gurinsu s**a tarbeka da kyakyawan Customer's service?? Idan Eh yakaji???
3. Hmm! Ya kaji gurin Tunowa?? Akwai saukin tunawa ko kuma wahalar tunawa??
▪️MA'ANAR CUSTOMER'S SERVICES
Customer's service nanufin bayarda nagartaccen taimako da shawarwari daga kamfani, kasuwanci, dan kasuwa ko wakilin dan kasuwa zuwaga wanda yazo siyayya kokuma wanda ke amfani da kayan da kamfani ke samarwa.
A takaice zamuce bangaren Customers services bangarene mai matukar muhimmanci a kowanne irin kasuwanci domin shine ke mu"amala ta kai tsaye da aboka huldar kamfani.
Yazama wajibi ga Dan kasuwa yabama wannan bangare kula ta haqiqani domin duk wata nasara ta kasuwanci ta dogara da iya mu'amala da abokan huldar kamfanin
Duk inda na kira kalmar kamfani ina nufin kasuwanci suk kankantarsa.
▪️WANENE CUSTOMERS SERVICE REP.
Customers service Rep kokuma representative, shine mai bayarda taimako na musamman ko shawara ta musamman zuwa ga abokan huldar kamfani, zai iya kasancewa mai kamfanin ne dakansa kokuma wani daya dauka musamman domin kula da bangaren.
Dayawa mutane na fadin Customers service baiwace da Allah ke halittar dan adam da ita, zakaga akwai wanda naturally Allah yamasa baiwar iya magana da tsari da iya convincing wani kuma kaganshi gashinan ne dai k**ar.......
To amma a ra'àyina customers service ba naturally kawai ne ba ana iya koyonsa akuma kware. Dan haka dan uwa karka sama ranka natural ne kayi kokari ka koya domin inganta kasuwancinka
Zan tsaya anan insha Allah gobe zamu dora da Rabe raben Customers dakuma abubuwan da customers suke tsammani daga dan kasuwa na girmamawa dasauransu
Kucigaba da bibiyata
©Mur