Majlisu Ahlil Qur'an Tv

Majlisu Ahlil Qur'an Tv A platform for the promotion of first international Qur'an award in Nigeria

National Qur'an Conference
16/08/2026

National Qur'an Conference

15/08/2026

Labari | Ƙaramin yaro ɗan Nigeria, ya samu shaidar karatun Alƙur’ani a shirin horar da kananan Ƙwararrun makaranta Alkur’ani na duniya

Imran Musa daga Nigeria, ya samu wannan nasara ne a cikin "Shirin Samar da Ƙananan Ƙwararrun Ƙur’ani da Horar da Su a Riwaya da Diraya”, karo na biyu, a wannan shekara.

Wane fata ku ke yi masa?

Ahlul Qur'an TV

04/08/2026

Labari | Ƴan Gida Ɗaya Zainab Adam Bunkau da Asmau Adam Bunkau Sun Haddace Alƙur'ani Gaba Ɗaya

An shaida wani abin alfahari a wajen bikin SIA Schools 2026 Speech & Prize-Giving Day / Graduation Ceremony, inda 'yan gida ɗaya, Zainab Adam Bunkau da Asmau Adam Bunkau, s**a samu karramawa bayan kammala haddar Alƙur'ani mai girma gaba ɗaya da Riwayar Hafs An Asim.

Bikin na bana ya gudana ne ƙarƙashin taken "Building Future Leaders Through Quality Education, Entrepreneurship, Character & Innovation," inda aka haɗa yaye ɗalibai, raba lambobin yabo ga fitattun ɗalibai, da kuma ƙaddamar da shirin Future CEO & Business Establishment na ajin da ya kammala karatu na shekarar 2026.

Kammala haddar Alƙur'ani da Zainab Adam Bunkau da Asmau Adam Bunkau s**a yi ya kasance wani babban abin farin ciki ga iyalansu, malamansu da daukacin al'ummar makarantar. Nasarar ta nuna muhimmancin tarbiyya ta gari, jajircewa da kuma haɗa ilimin addini da na zamani wajen gina ɗalibai masu nagarta.

Ahlul Qur'an TV

31/07/2026
30/07/2026

“Yawan sauraron karatun Alkur'ani yana sauƙaƙawa mutum haddar Alƙur'ani”

Ahlul Qur'an TV

26/07/2026

Labari Da Ɗumi-Ɗumi | Gwani Muhammad Adam Alkali OON, Ya Ba da Tallafin ₦2,500,000 Ga Ƙungiyar Musabaƙar Alƙur'ani Ta Jihar Plateau, Jos.

Cikin jawabinsa, Hon. Gwani Muhammad Adam Alkali OON, ya ƙarfafa gwiwar mahalarta gasar da su kasance masu ƙwazo ba kawai a fannin karatu da haddar Alƙur'ani ba, har ma wajen kyawawan ɗabi'u da aiwatar da abin da Alƙur'ani ya koyar. Ya tunatar da su cewa ainihin darajar Alƙur'ani tana bayyana ne ta hanyar aiki da koyarwarsa.

Ya kuma shawarci matasan mahaddata da su ci gaba da kasancewa masu jajircewa, ladabi da biyayya ga koyarwar addini, tare da rayuwa bisa gaskiya, tawali'u da hidimtawa al'umma.

A matsayin nuna goyon baya ga ci gaban ilimin Alƙur'ani da tarbiyyar al'umma, Hon. Gwani Muhammad Adam Alkali OON ya ba da gudummawar ₦2,500,000 domin tallafa wa ayyukan gidauniyar.

Ahlul Qur'an TV

26/07/2026

Labari Cikin Hoto | Ɗaliban Makarantar AlFajr College of Education Da Su ka Haddace Alƙur'ani, Littafin Shaɗibiyya da Kuma Durrah a Garin Kano.

Ɗalibai daga Makarantar AlFajr College of Education sun samu gagarumar nasara bayan kammala haddar Alƙur'ani Mai Girma, tare da haddar fitattun littattafan ilimin ƙira'a na Shaɗibiyya (Hirzul Amānī) da kuma Durrah Al-Muḍiyyah.

Ana kallon wannan a matsayin babban ci gaba ga makarantar, domin ta ci gaba da fitar da ƙwararrun mahaddata da masu ilimin ƙira'a da za su amfani al'umma da iliminsu.

Address

34, Masallacin Jumma'a Street, Adjacent Fire Service, Jos North
Jos
930103

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Majlisu Ahlil Qur'an Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share