Abu Mansur Mustapha Sani Albani Jimeta

Abu Mansur Mustapha Sani Albani Jimeta

Share

WANNAN PAGE INSHA ALLAH ZAI DINGA KAWO MUKU VIDEOS DA AUDIOS DA SAURANSU DOMIN GINA GOBE MAI KYAU DA ABUNDA YA SHAFE RAYUWAR YAU DA KULLUM

17/05/2026

An Samu Labarin Ganin Jinjirin Watan Zulhajja a Nageriya don haka gobe Litanin shine 01 ga watan Zulhajja 1447

09/05/2026
19/04/2026

🌿 Darasin Rayuwa 🌿
Shin ka san cewa giba (gulma) babbar illa ce mai tsanani?

Wasu suna ɗaukar giba da sauƙi, alhali tana daga cikin manyan zunubai da ke lalata zumunci da tsarkakewar zuciya.

Allah MaÉ—aukaki ya ce:
“Kada ku yi giba juna. Shin ɗayanku zai so ya ci naman ɗan’uwansa da ya mutu? Lallai za ku ƙi haka…”
(Qur’ani 49:12)

Annabi ď·ş ya ce:
“Kun san menene giba?” Sai s**a ce: Allah da Manzonsa ne s**a fi sani. Ya ce:
“Ka ambaci ɗan’uwanka da abin da ba ya so.”
(Hadisi sahihi – Muslim)

Haka kuma Annabi ď·ş ya ce:
“Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to ya faɗi alheri ko ya yi shiru.”
(Hadisi sahihi – Bukhari da Muslim)

🤲 Mu kiyaye harsunanmu, mu nisanci giba, domin neman yardar Allah da tsarkin zukata.

18/04/2026

🌿 Darasin Rayuwa 🌿

Shin ka san cewa yin shiru ya fi alheri akan faÉ—in sharri?

Sau da yawa mutum yana shiga matsala ne saboda harshensa. Kalma guda na iya É—aga mutum, haka nan kalma guda na iya jefa shi cikin nadama.

Allah MaÉ—aukaki ya ce:
“Babu wata magana da mutum yake furtawa face akwai mai sa ido a kansa, mai rubutawa.”
(Qur’ani 50:18)

Annabi ď·ş ya ce:
“Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to ya faɗi alheri ko ya yi shiru.”
(Hadisi sahihi – Bukhari da Muslim)

Ka kiyaye harshenka daga gulma, zagi, da faÉ—in abin da ba zai amfani ba. Ka yi shiru idan abin da zaka faÉ—a ba alheri ba ne.

🌙 A wannan daren Juma’a, mu tsaftace zukatanmu da harsunanmu, domin samun yardar Allah.

🤲 Allah ya sa mu cikin masu faɗin alheri ko yin shiru. Ameen.

18/04/2026

🌿 Kyawawan Halaye 🌿

Rayuwar mutum ba ta cika sai da kyawawan halaye. Duk wanda ya gyara halinsa, yana samun daraja a wajen Allah da kuma mutane. Mu riƙa yin magana mai kyau, mu guji cutar da juna, mu zama masu haƙuri da yafiya.
Allah MaÉ—aukaki ya ce:
“Ka yi afuwa, ka yi umarni da alheri, ka kau da kai daga jahilai.”
(Qur’ani 7:199)

Annabi ď·ş ya ce:
“An aiko ni ne domin in cika kyawawan halaye.”

🤲 Mu gyara halayenmu, domin su ne hanyar samun rahamar Allah.

17/04/2026

Mu kyautata niyyarmu,
Aikin Addini duk kayi baka kyautata niyya ba
To ka shiga ukku

17/04/2026

Wanda Allah ya nufe shi da Alheri,
sai ya fahimtar da shi Addini

17/04/2026

Ku yawaita Salati ga Manzon tsira
Muhammadur Rasulullah(S.A.W)
Musamman a ranar Juma'a

12/04/2026

Kada ka yarda ka gane gaskiya, amma da gangan ka kauce mata.

Dr. Jabir Sani Maihula

Want your school to be the top-listed School/college in Jimeta?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address

Jambutu Haske
Jimeta
640283