09/12/2025
Tazara tsakanin Makka da Madina kusan kilomita 410 ne — wanda yau ake shafe kusan awanni huɗu a mota a tashi ɗaya ba tare da tsayawa ba.
Amma ka É—an tsaya ka tunani girman wannan lamari:
Manzon Allah ﷺ ya raba wannan hanya gida biyu — rabinsa yana hawa, rabinsa kuma yana tafiya a ƙafafunsa masu tsarki, a cikin zafin jeji, na tsawon kwanaki takwas a jere, tare da abokinsa mafi ƙauna Abu Bakr As-Siddiq (RA).
Wannan tafiya ba wai wata tafiya ce ta wucewa kawai ba. Tafiya ce ta juriya, haƙuri, da tsayin daka. A cikinta Manzon Allah ﷺ ya ɗauki daƙile-daƙilen rayuwa cikin sauƙin kayansa, yana ɗauke da babban amana — israro addinin nan ya iso gare mu tsarkakke, tsaftatacce, ba tare da ɓarna ko dusashewa ba.
Wallahi, wadanne manyan sadaukarwa aka yi don mu yau mu zauna cikin ni’imar Musulunci muna jin daɗi lafiya da kwanciyar hankali?
✨
Ya Allah! Ka yi wa Annabi Muhammad ﷺ salati gwargwadon yawan ƙafafun da s**a nufi gareshi cikin neman albarka.
Ya Allah! Ka yi masa salati gwargwadon abin da ya sha na tsanani da dare da rana.
Ya Allah! Ka yi masa salati har Ya gamsu, idan Ya gamsu, bayan Ya gamsu.
Ya Allah! Ka yi salati ga waÉ—anda s**a É—auko hasken shiriya s**a kawo mana,
ga iyalansa, sahabbansa, da masu binsu da kyautatawa har zuwa Ranar Qiyama.