1. Ki gargadi 'yar ki kada ta kuskura ta
zauna a cinyar wani, koda kanin babanta ne
ko Almajirin gidansu.
2. Kada ki dinga canja kaya a gaban
'ya'yanki wadanda s**a kai kamar shekara
biyu. Ki dinga cewa su fita.
3. Kada ki yarda wani babban mutum ya
dinga kiran 'yar ki da "Mata ta" ko
"Amarya ta" dds.
4. Idan 'ya'yanki suna wasa da wasu yaran,
ki dinga lura wane irin wasa sukeyi. Saboda
wasu yaran suna wasa da al'aurar junansu.
5. Kada ki matsawa 'yar ki zuwa wajen
wanda ba ta so ta je wajensa. Kamar
wani me siyar da kayayyaki ko
makamancinsu.
6. Ki saka lura sosai idan kika ga dan ki ko
'yar ki sun shaqu da wani mutum a waje
kuma suna son zuwa wajensa.
7. Kada ki bari dan ki ko 'yarki su dinga
yawo ba riga ko wando a cikin gida b***e su
fita waje.
8. Idan kin yiwa 'yar ki kwalliya, to ki gaya
mata iya gidajen da za ta shiga.
Kuma daga nan ta dawo gida. Kada ta zauna
a rariya ko shige-shigen gidaje.
9. Idan ki ka ji an yiwa abokin dan ki ko
kawar 'yarki wani abu mara dadi, to kema ki
binciki na ki sosai. Ki tuhume shi.
10. Idan 'ya'yanki mata sun fara girma, ki
koya musu yadda ake kula da jini. Da yadda
ake kula da budurci da hadarin kawar da
shi. In ba haka ba zata fara koyar munanan
dabi'u a wajen kawaye.
11. Ki kula da irin kayan wasan da yaranki
suke amfani da su. Kamar yartsana me
hoton tsiraici da makamantansu.
12. Ki koyawa 'yar ki me shekara uku yadda
ake wanke muhimman gurare ajiki, har da
kirji kuma ki gaya mata kada ta bari kowa ya
ta6a mata nan wajen da nan wajen.
13. Ki tabbatar duk wani hoto ko abin
amfani wanda zai 6ata tarbiyyar yaro kin
nisanta shi da inda yaranki za su gani.
14. Duk sanda 'yarki ko danki ya kawo miki
karar wani babba ya cire masa
kaza ko ya ta6a masa kaza, to kada ki dau
mastalar da wasa.
A bi duk matakan da s**a dace don
tabbatar da
abinda ya faru.
15. Ku tuna Tarbiyyah tana farawa ne daga
gida
*Pls kutura zuwa wani group din don sauran iyaye mata su ankarar da iyalansu* 👏🏼👏🏼👏🏼
Isah Lawan Jhn
I am a physicist
11/08/2022
BSC. PHYSICS; ilimin Kimiyyar Ƙwayoyin Halitta Da Makamashi..
'Arewa Students Orientation Forum'
Physics Duniyar Science..
Babu ko Tantama kan Zamowar ilimin Physics Uba ga duniyar Science Dan haka nema Ɗaliban BSC. PHYSIC Kan zamowa na musamman kuma zaƙaƙurai a fannonin Kimiyya , Bsc. Physics maɓuɓɓuga ne ga dukkan Wani Nau'in Ƙere-ƙere a duniya Da Samar da ababen rayuwa na zamani shekaru aru-aru.
Bsc. Physics Kimiyyar ƙwayoyin halitta da makamashi da kuma mu'amalar da ke tsakanin su biyun, an rarrabe zuwa traditional Field (fannonin Physics na gargajiya) kamar su acoustics, optics, mechanic, thermodynamics, da electromagnetism, haka nan kuma akwai ɓangaren modern Physics (na zamani) da s**a haɗa da atomic da nukiliya physics, da cryogenics, solid-state physics, particle physics, da kuma plasma physics dasauransu.
Kimiyyar Physics kimiyya ce da ke da alaƙa da Properties, canje-canje, hulɗa, da dai sauransu na Ƙwayoyin halitta da makamashi wanda ake ɗaukar makamashi a matsayin ci gaba (classical physics), ciki har da wutar lantarki, zafi, na'urorin gani, makanikai, da dai sauransu, kuma yana hulɗa da ma'aunin atomic na yanayi wanda a cikinsa ake ɗaukar makamashi a matsayin mai discrete (Ƙwayoyin kimiyyar lissafi), gami da irin waɗannan rassa kamar su atomic, nuclear, da sulfur-state physics ka iya zamowa Gagara badau da sai dai ace mutum yayi iyakar iyawar sa.
a fannonin da s**a haɗa da injiniyoyi, acoustics, optics, zafi, wutar lantarki, magnetism, radiation, da kimiyyar atomic da nukiliya Physics shine kimiyyar yadda abubuwa ke aiki da wanzuwa a duniya da tsarawa da sarrafa yadda za'a ci moriya da ƙirƙire-ƙirƙiren zamani dana da can baya
Bsc. Physics shine kimiyyar daɓi'a da ke nazarin ƙwayoyin halitta, ainihin abubuwan da ke tattare da su, motsinsu da halayensu da sararin samaniya da lokaci, da abubuwan da s**a danganci makamashi da kuzarin Motsawa, Physics yana ɗaya daga cikin mafi mahimmancin ilimin kimiyya, tare da babban burinsa shine fahimtar yadda duniyar Kaunu ke wanzuwa.
Ga Jerin Wasu Daga Cikin Courses Ɗin da'akeyi a Physics:
1st Semester Level One:
Mechanics
Electricity And Magnesium
Physic Practical 1
Elementary Mathematics ¡
Elementary Mathematics ¡¡
Introduction to Computer science
Organic chemistry
2nd
Behaviour Of Matter
Physic Practical 1
Probability 1
Elementary Mathematics 3
Physical Chemistry
Practical Chemistry
200 level 1st
Renewable Energy
Physic Practical
Electric Circuits and Electronics
Elementary Modern Physic
Mathematical Method
2nd
Electronic Practical
Waves and optics
Thermal Physic
Elementary Differential Equation
Probability 3
300 level 1st
Vector And tensors
Solid State Physics
Energy and Environment
Physics and Electronic laboratory
Complex analysis
Analytical Mechanic 1
Quantum Physics
Electricity And Magnetism
Design Studies
Introduction to acoustics
Introduction to geophysics
Semiconductor device
Electronic circuits
Siwes
Level 400:
Quantum Mechanics 1
Mathematical Methods in Physics1
Computational Physics
Statistical and thermal Physics
Electromagnetic Waves
Analytical Mechanic 2
Dss.
(a Lura cewa Courses suna iya sauyawa Daga Makaranta zuwa makaranta, kuma wannan mun tsakuro kaɗan ne)
Wasu Kaɗan Daga cikin Branch Na Physics:
Classical Physics
Modern Physics
Nuclear Physics
Atomic Physics
Geophysics
Biophysics
Mechanics
Acoustics
Optics
Thermodynamics
Astrophysics
Wasu Kaɗan Daga cikin Ɓangarorin Da za'a iya cigaba da karatu bayan Bsc. Physics
MBA in Data Science
MBA in Information Technology
MSc in Materials Science and Engineering
M. Sc Vacuum Sciences
M. Sc Acoustics
MSc in Applied Physics
MSc in Physics
M. Sc Applied Electronics
MSc in Atmospheric Science
MSc in Nanotechnology
MSc in Astronomy/Planetary Science/Astrophysics
MSc in Aeronautics
Master in Atomic and Molecular Physics
MSc in Particle/Nuclear Physics
MSc in Geophysics
MSc in Molecular Physics
MSc in Optical Physics
MSc in Medical Physics
MSc in Biophysics
Wasu Daga cikin Short-term Courses/ Training Bayan BSc Physics:
PG Diploma in Data Science
PG Diploma in Astronomy
PG Diploma in Nanotechnology
Diploma in Medical Lab Technology
PG Diploma in Community Health Nursing
Certificate in Lab Assistant/Technician
Diploma in Operation Theatre Technology (OTT)
PG Diploma in Machine Learning/Artificial Intelligence.
•Shin BSc Physics Yanada tasiri a wannan zamanin?
A wannan zamanin, ana amfani da Physics a kowane fanni na rayuwa, Bayan kammala wannan kwas, ɗalibai suna da damar aiki daban-daban ga kaɗan Daga Ciki:
Petroleum and gas
Science
Engineering
Business and finance
Technology
Construction
Physicist
Physics Lecture
Lab Assistant
Research Associate
Subject Matter Expert
Technician
Radiologist Assistant
Quality control manager
Research associate
Statistician
technician
academic counselor
Dss.
©ASOF-2022
Whatsapp 08086251045
02/08/2022
01/08/2022
MAZA GA SAKO MAI KARFI!
MATSALAR DA MATA KE FUSKANTA.
'Mafi yawan samarin yanzu duk mutanen banza sunfi yawa a cikinsu, burinsu kawai su taɓa yarinya ko su ƙwanta da ita, ko tanaso ko bataso ta hanyar shirya mata muguwar yaudara da sunan zasu aureta, ko wasu dabaru Idan taƙi yarda sai su rabu da ita, dama iskanci ya kawosu ba aure ba.
Karki yarda ya taɓaki, b***e har ya samu damar ƙwantawa dake, zina bala'i ce masifa ce, tsiya ce.
Ki bari yayi fushi ɗin ya tafi gwanda ya barki da mutuncinki, karki bari ya taɓa miki mutunci karki yarda sai an shafa fatiha kin tabbatar an kammala komai koda kuwa ya kawo lefe kuma ya bada sadaki, wannan ba aure bane sai an ɗaura, to kome yakeso kiyi masa karki kuskura ki bari ya latsaki keba dabba bace, dabbace kaɗai ake latsawa kafin a siya ko a ƙwanta da ita babu aure, idan kika yarda kin zama dabba, koda kuwa zai aure kine, da gaske, karki kuskura ki yarda.
Idan kuna ko ƙwanto, ku sami ƴan mata ku tambayesu zakuji da iskanci yanzu samari suke zuwa gurinsu, shine babban ƙalubalen da suke fuskanta, zai wahala kaga yarinyar da wani baije mata da maganar iskanci ba, abin da ciwo babu daɗi ƙwata-ƙwata.
Wallahi muji tsoron Allah, muma zamu haihu koda ace babu kamun ubangiji.
Allah ya shirya mu, baki ɗayan mu, ya rabamu dason zuciya da shiriritar banza da wofi.'
Imam Anas.
HOW MATHEMATICIANS WRITE A LOVE LETTER
Dear Someone,
Yesterday, I was passing by your rectangular house in trigonometric lane. There I saw you with your cute circular face, conical nose and spherical eyes, standing in your triangular garden. Before seeing you, my heart was a null set, but when a vector of magnitude from your eyes at a deviation of theta radians made a tangent to my heart, it differentiated. My love for you is a quadratic equation with real roots, which only you can solve by making good binary relation with me.
The cosine of my love for you extends to infinity. I promise that I should not resolve you into partial functions but if I do so, you can integrate me by applying the limits from zero to infinity. You are as essential to me as an element to a set. The geometry of my life revolves around your acute personality.
My love, if you do not meet me at parabola restaurant on date 10 at sunset, when the sun is
making an angle of 160 degrees, my heart would be like a solved polynomial of degree 10. With love from your higher order derivatives of maxima and minima, of an unknown function.
Yours Truly,
Me as:PYTHAGORAS
RAYUWA A TERTIARY INSTITUTION...
Shirin Ƙungiyar 'Arewa Students Orientation Forum'
Acikin Shirin Na Wannan Mako Abdulhakim Mustapha yabayyana Yanda Yayi JAMB So Uku Amma Sai a ta Ukun yasamu damar zuwa jami’a amma fa tsawon shekara ukun Ba'a zaman kashe wando Yayi su ba yagama NCE...
: KAI TSAYE ZAMU FARA DA GABATARWA!
Mustapha: Sunana abdulhakim mustapha malumfashin jahar katsina, Dalibi a
Makarantar isa kaita College of Education
ASOF: ATAQAICE MENENE TARIHIN KARATUN KA?
: Na yi primary school a heritage dake malumfashi, Lokacin da nakai primary 4 sai aka maidani Sallau model primary school aka Dawo dani Primary 2
Inda har nagama a 2009, natafi Great Ambassador international college Malumfashi
: WANNE KALUBALE KAFARA FUSKANTA A SIKANDIRE?
:
Rashin iya turanci, Makarantar basa Hausa
Sakamakon haka duk abinda s**ayi banaganewa sai kadan daga ciki
Hakan yasa lokacinda zamuje jss2 akaimin Repeat
: DA WANNE BURI KASHIGA SIKANDIRE?
: Lokacin da naje Ss1 nayi burin zama Masanin Bangaren Noma Wato "Agricultural Science" Amma lokacin damuka fara karatun ss1 sai na fahimci wulakanta mata musamman musulmai da a keyi Yayi yawa sai na dau alkawarin zama lauya.
Daganan na maida hankali Akan Duk Abunda yashafi bangaren lawyer
: KANASO KACE MATA NA FUSKANTAR TSANGWAMA TA FUSKAR ILIMI KENAN?
: eh Yadda naga ana hana mata sanya hijabi a makarantar mu kuma gasu musulmai
: MEYA CHANJA RA’AYINKA NA ZAMA LAWYER?
: Lokacin da naje ss2 zamuje excursion donganin yadda aikin shari’a yake gudana asannan ne mahaifina yasancewa ba bangaren Science nake karanta ba sai ya Mayar dani Science
: ME YAJA HANKALIN KA DAFARKO KAKESON AGRICULTURE?
: Yadda naga mahaifina yana noma ya saida asamu kudi dayawa, na fahimci cewa noma yana kawo kudi sosai
: REPEAT DIN DA'AKAYI MAKA SO BIYU BE KASHE MAKA KWARIN GWIWA BA?
: Gsky da farko ba abinda naji amma na biy
26/06/2022
🚨 Real Madrid’s expected lineup for next season according to
21/06/2022
Irin Mafarkin Da Zaki Gane Aljanu Suna Tare Dake Ko Sun Aureki Irin Mafarkin Da Zaki Gane Aljanu Suna Tare Dake Ko Sun Aureki
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Contact the school
Telephone
Website
Address
Opening Hours
| Monday | 09:00 - 17:00 |
| Tuesday | 09:00 - 17:00 |
| Wednesday | 09:00 - 17:00 |
| Thursday | 09:00 - 17:00 |
| Friday | 09:00 - 17:00 |
| Saturday | 09:00 - 17:00 |
| Sunday | 09:00 - 17:00 |