Wild Hausa

Wild Hausa Hausa Content Creation | Environment | Wildlife | Education | Tourism | Travel | Entertainment | Culture

07/09/2026

Ka taɓa shan irin wannan Kwakwar? Shekaru goma sha biyar rabo na da ita tun ziyarar Benin Republic.

Da na ganta na ji daɗi, amma fa kuɗin da su ka kira yai yawa duba da a cikin Lekki Conservation Centre ne. Idan ka auna yarda ake sayar da ita a wasu sassan na garin Lagos da wajen Nigeria za ka ji banbanc sosai.

Ba laifi dai, an sha ruwan Kwakwa kuma an ci Kwakwar.

Wasu daga cikin irin kuɗaɗen da ake dasu daga sassa na duniya ya ishe ka ka san irin ƙasashe da al'adun mutane a duniya....
07/09/2026

Wasu daga cikin irin kuɗaɗen da ake dasu daga sassa na duniya ya ishe ka ka san irin ƙasashe da al'adun mutane a duniya. Wataƙila ka hango wani mai kyau ka ce dama shi ne kuɗin ƙasar ku ko?

Ƙafar Mikiyar Golden eagle 🦅. Mikiya ce da ake samun ta a sassa da yawa na duniya. Kai da ganin wannan makaman da su ke ...
06/09/2026

Ƙafar Mikiyar Golden eagle 🦅. Mikiya ce da ake samun ta a sassa da yawa na duniya.

Kai da ganin wannan makaman da su ke ƙafar ta kasan duk abinda ta riƙe zai ji a jikin sa.

📸 US Fish and Wildlife Service

Harar, ƙauye ne a ƙasar Habasha, Ethiopia da mutan garin ke zama lafiya lumi da Kuraye. Har abinci su ke basu a baki, ku...
06/09/2026

Harar, ƙauye ne a ƙasar Habasha, Ethiopia da mutan garin ke zama lafiya lumi da Kuraye. Har abinci su ke basu a baki, kuma masu yawon buɗe ido ma suna iya haka domin nishadi.

Ya kamata mu kai musu ziyara gaskiya.

05/09/2026

Yau ranar Ungulu ce ta duniya, World Vulture Day.

Ungulu ta samu kan ta a wani irin yanayi a arewacin Nigeria. Ka saurara da kunnen ka ka ji.

Nike Art Gallery, wajen kayan al'adu ne da hotunan zane, irin na Paintings da ake yi da hannu. Malam ka san fa paintings...
04/09/2026

Nike Art Gallery, wajen kayan al'adu ne da hotunan zane, irin na Paintings da ake yi da hannu. Malam ka san fa paintings akwai kyau amma akwai tsada.

Hoto na uku na tambaya aka ce min naira miliyan biyar. Na uku kuma naira miliyan ɗaya da rabi. Na ce musu idan na samu kuɗin zan dawo 😀.

04/09/2026

Indirizzo

Carpi

Notifiche

Lasciando la tua email puoi essere il primo a sapere quando Wild Hausa pubblica notizie e promozioni. Il tuo indirizzo email non verrà utilizzato per nessun altro scopo e potrai annullare l'iscrizione in qualsiasi momento.

Contatta La Scuola/università

Invia un messaggio a Wild Hausa:

Scelte rapide

Condividi