Real Jamilu Gambo

Real Jamilu Gambo

Share

what is your name

19/10/2024

MASHA ALLAH

27/12/2023

Masha allah

18/03/2022
02/03/2022

masha allah

08/02/2022

burin kowane masoyi yasami abokiyar rayuwa tagari a kullum ina yiwa allah godiya daya bani nagartacciyar mace irinki

07/02/2022

SABON TSARIN YADDA ZAKU BUƊE JAMB PROFILE, DOMIN YIN RIJISTAR JAMB TA SHEKARAR 2022

A lokacin da ya rage kwanaki biyar kacal a fara rijistar jarrabawar JAMB UTME da DE, tuni Ɗalibai da dama s**a fara buɗe JAMB Profile, ta hanyar Aikawa da lambobin su na katin ɗan ƙasa zuwa ga hukumar JAMB, ta sakon kar ta kwana na SMS, hakan ne yasa muma muka garzayo domin bayyana muku matakan da za ku bi domin buɗe JAMB Profile ɗin naku, a shirye-shiryen tunkarar rijistar jarrabawar JAMB ta wannan shekarar.

Toh!!, yanzu sai ku ɗauko wayoyinku domin mu garzaya muga yadda tsarin buɗe Profile ɗin yake :

• Da farko zaku ziyarci wurin rubuta sakon Message na wayoyinku (New Message), sai ku rubuta ''NIN'' sannan ku bada tazara (Space), sai ku rubuta lambobin katinan ku na ɗan ƙasa, Misali :

NIN 63094545641

👉Sannan sai ku aika da saƙon zuwa lambar 55019, ko kuma sabuwar lambar da hukumar JAMB ta ƙaddamar ta 66019.

~Bayan kun aika saƙon, sai ku jira zaku samu saƙo daga hukumar JAMB ta wannan layin da kuka tura NIN ɗinku, ɗauke da cikakken sunanku tare da lambobin ku na Profile Codes, wanda kuma da lambobin ne zaku yi amfani domin sayen e-PIN .

Ababen Lura :

√• Wajibine ya kasance akwai kuɗaɗen da basu gaza Naira 50 ba a layukan wayoyinku, a lokacin da zaku tura wannan saƙon, saboda za'a ɗauki Naira 50 daga Asusun wayoyinku da zarar kun tura saƙon.

√• Babu dama kuyi amfani da lambobin wayoyin da kuka yi amfani da su wajen rijistar JAMB a shekarun da s**a gabata, ma'ana dole ne kuyi amfani da layin da ba'a taɓa yin rijistar JAMB da shi ba.

√• Haka zalika kowanne Ɗalibi ɗaya zaiyi amfani da layi ɗaya ne kawai, ma'ana babu damar ku bawa ƙannenku ko wasu ƴan uwanku suma su tura NIN ɗinsu da wannan layin.

👉 copy by jgs

Want your school to be the top-listed School/college in Jigawa?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address

Sankara Yamma
Jigawa
MURTALA