17/08/2026
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi (BASIEC) ta sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar ranar Litinin, 17 ga Agusta, 2026.
A cewar hukumar, jam’iyyar APM ta lashe kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 20, yayin da ta kuma samu nasarar lashe 319 daga cikin kujerun kansiloli 323.
Ga sakamakon shugabannin ƙananan hukumomi:
Alkaleri: Bappah Aliyu Mohammed – APM, 107,482
Bauchi: Umar Mohammed Aliyu – APM, 125,170
Bogoro: Zakka Luka Magaji – APM, 25,282
Dambam: Iliya Isah – APM, 19,730
Darazo: Ya’u Samaila Sade – APM, 67,276
Dass: Mohammed Abubakar Jibo – APM, 35,264
Gamawa: Ali Babayo – APM, 54,423
Ganjuwa: Mohammed Idris M. – APM, 24,150
Giade: Mustapha Alhaji Musa – APM, 33,864
Itas/Gadau: Dankawuwa Ya’u – APM, 24,989
Jama’are: Inuwa Abdullahi – APM, 36,766
Katagum: Yusuf Babayo Zaki – APM, 65,626
Kirfi: Garba Musa – APM, 24,787
Misau: Salisu Hussaini – APM, 34,378
Ningi: Yahuza Adamu Haruna – APM, 29,387
Shira: Saleh Hodi Jibir – APM, 37,135
Tafawa Balewa: Sama’ila Wakili Lere – APM, 46,625
Toro: Abubakar Ibrahim Dembo – APM, 109,999
Warji: Habibu Idris Usman – APM, 43,066
Zaki: Mas’ud Aliyu – APM, 19,984
A bangaren kujerun kansiloli, SDP ta samu Dandango Ward a Bauchi, NRM ta lashe Darazo South Ward, ZLP ta samu Wandi Ward a Dass, yayin da YPP ta lashe Zirami Ward a Giade.
Shugabar BASIEC, Hajiya Jummai S. Abubakar (Gimbiyar Dass), ta ce hukumar ta tabbatar da sakamakon ne bayan kammala ƙirga ƙuri’u, tattarawa da tantance sakamakon, tare da bin tanadin dokar zaɓe.
Ta kuma taya waɗanda s**a yi nasara da al’ummar Jihar Bauchi murna.
Rahoto Zamani Tv