27/12/2024
AL-WALA A SAUKAKE [DAIDAI DA FATAWAR AYATULLAH KHAMENAEI(D)]
Wajibi ne yin Al-wala kafin yin Sallah ko duk wani aiki da aka shardanta masa yin tsarki.
YANDA AKE AL-WALA
1. Wanke Fuska
2. Wanke Hnnaye
3. Shafar Kai
4. Shafar Kafafu
1. Tsayin Fuska: Daga mabubbugar gashin Kai zuwa kasan Haba.
2. Fadin Fuska: Cikon hannu; daga babban yatsa zuwa yatsan tsakiya.
3. Tsayin Hannu: Daga gwiwar hannau zuwa karshen yatsu.
4. Yanda ake wanke Fuska da Hannaye: Daga Sama zuwa Kasa, sau 1 ko 2, haramun ne wankewa sau 3.
5. Shafar Kai: Daga tsakar Kai zuwa Goshi.
6. Shafar Kafafu: Ana shafar saman Kafa ne, daga ‘yan yatsu zuwa saman Kafa.
7. Ana shafar Kai da Kafafu ne: Da sauran danshin ruwan wankin Hannaye.
8. Wajibi Kai da Kafafu su kasnce a bushe kafin shafarsu, doriya akan kauda shamakin da zai hana a shafesu kai-tsaye.
9. Wajibi ne Gabobin Al-wala su kasance masu tsarki.
10. Wajibi ne Ruwan Al-wala su kasance masu tsarki; doriya akan kasancewar su Ruwa zalla, halastattu.
11. Wajibi ne Jerantawa; farawa da wanke Fuska har zuwa shafar Kafa.
12. Wajibi ne gaggautawa; yin Al-wala a lokaci daya.
13. Wajibi ne yin Niyyah; yin Al-wala don samun kusanci da Allah.
14. Wajibi ne mutum yayi Al-wala da kansa; matukar zai iya.
WAJIBI NE YIN AL-WALA DON:
1. Yin Sallah.
2. Yin Dawafi (Ka’aba).
3. Taba rubutun Qur’an.
4. Taba sunan Allah.
5. Taba sunayen Annabawa(as) da Ma’asumai(as).
MUSTAHABBI NE YIN AL-WALA DON:
1. Yin karatun Qur’ani.
2. Kaukar Qur’ani.
3. Taba bango ko takardun Qur’ani.
4. Ziyartar Makabarta.
5. Yin Al-wala don son zama cikin tsarki.
ABUBUWAN DA KE BATA AL-WALA
1. Yin Fitsari
2. Yin Bahaya
3. Yin Tusa
4. Yin Barci (Kwana)
5. Duk abinda ke wajabta wanka (Janaba, Hailah, Istihalah…).
6. Gushewar Hankali.
MARAJI'U (REFERENCES)
- منتخب الأحكام (طبقا لفتوى آية الله الخامنئي)، الشيخ حسن العاملي، دار الولاية، بيروت لبنان. 2012
- زبدة الأحكام، طبقا لفتوى آية الله الخميني، طهران إيران، 1404 ه
- أجوبة الاستفتاءات، السيد علي الخامنئي، ...
- توضيح المسائل,