Nαzαrin Mαi Hαnkαli

Nαzαrin Mαi Hαnkαli Allah SWT yana cewa: Shin kuna tunanin Mun halicce ku Dan Wasa? Sannan Baza ku dawo garemu ba😭💔🥺

DALILAI 10 DA YASA MATA S**A FI SON NAMIJIN DA BAYA SON SU:Idan na fada muku gaskiyar yadda kwakwalwar mace take aiki, w...
20/09/2026

DALILAI 10 DA YASA MATA S**A FI SON NAMIJIN DA BAYA SON SU:

Idan na fada muku gaskiyar yadda kwakwalwar mace take aiki, wasu zasu dauka tsana ce. Amma zahirin magana shi ne: Mata da yawa suna kyamatar namijin da yake durkusa musu da tsantsar kauna, su koma suna haukatar da kansu a kan wanda bai ma san da zamansu ba.

Ga dalilan da yasa hakan take faruwa:

1.
Kalubale: Mace ba ta son abin da yake zuwa mata da sauki. Namijin da baya nuna damuwa, yakan zama kamar wani babban kofi na trophy da take son lashewa don ta tabbatar da cewa kyanta yana aiki.

2.
Rashin Zakuwa: Namijin da yake nuna zakewa yana nuna rauni a idonsu. Amma wanda yake tafiyarsa yana nuna cewa rayuwarsa tana tafiya daidai koda babu ita, wannan rashin damuwar ita take tayar musu da hankali.

3.
Gasa a Tsakanin Mata: Idan mace ta ga baka damu da ita ba, lissafinta yana bata cewa akwai wasu matan da kake bawa kulawa. Wannan tunanin na gasa shi yake rura wutar son ta mallake ka.

4.
Kwarjini Da Jan Aji: Namijin da ya cika yi wa mace bayanin komai yana rasa kwarjininsa. Wanda yake yin shiru bai cika magana ba, shi ne yake sa ta raba dare tana tunanin waye shi a zahiri.

5.
Raunin Motsin Zuciya: Rayuwa da namijin da yake nuna kauna dari-bisa-dari tana basu gajiya saboda babu wani sabon abu. Suna son wanda zai sa su fargaba yau, gobe ya sa su dariya; wannan shi yake sa su ji suna raye.

5.
Karyar "Zan Iya Canza Shi": Wata irin dabi'a ce ta son nuna karfi. Mace takan so ta auri taurin kan namiji da nufin cewa ita kadai ce zata iya yin amfani da dabarunta wajen sassauta shi.

6.
Yawan Kulawa Yana Kawo Raini: Idan ka mayar da mace ita ce duniyarka ta hanyar yi mata bauta, zata fara kallonka a matsayin mara aikin yi. Amma wanda yake watsar da ita yana fuskantar abin gabansa, shi ne take kallo a matsayin namiji mai tsari.

7.
Kuskuren Fahimtar Karfi: Mata da yawa suna fassara nuna ko-in-kula a matsayin tsantsar karfin 'Da Namiji. Suna ganin wanda bai damu da zafin soyayya ba, shi zai fi basu kariya a rayuwa.

8.
Yaudarar Hankali wato Reverse Psychology: A dabi'ance, zuciya tana gudu ne zuwa ga abin da yake guje mata, sannan tana tattaka abin da yake rarrafe a gabanta yana rokon ta.

9.
Tabbacin Daraja: Namijin da baya nuna tsoron rasa mace, ya riga ya tabbatar da cewa darajarsa tana da girma. Ita kuma mace kullum burinta ta hada inuwa da wanda darajarsa ta fi tata.

A matsayinka na 'Da Namiji, ka daina gina rayuwarka a kan lallashin mace ko bauta mata don neman yardarta. Ka Gina kanka, ka fuskanci neman na kai, ka ajiye tsarin kanka. Idan ka zama wani abu, su da kansu za su neme ka.
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️

Qanwata!Shin an taba cewa da ke "irin tufafin da k**e sakawa yayin fita yana cikin dalilin da ya kawo Miki jinkirin Aure...
07/09/2026

Qanwata!

Shin an taba cewa da ke "irin tufafin da k**e sakawa yayin fita yana cikin dalilin da ya kawo Miki jinkirin Aure???😊

🤎Qanwata ki dan saurari abin da zan fada Miki; mazan nan fa kowa zai iya zama MIJI, daga cikin masu zama MIJIN har da maza yan uku Ashirin, da yan Biyu sha biyar, da yan hauma hauma, da yan ta more, da yan takife....da dai sauransu, kowa yana iya zama MIJI, madamar ya Kai sadaki, anyi siga, an sanya shaidu.....kalaas!👌

🤎Qanwata amma shi Namijin da ya Kai Aure Kuma ya isa Aure na shari'a, Namijin da ya shirya riqe Auren, Namijin da ya San kansa, Namijin da ya San Lissafin Rayuwa, Namijin da ya San darajar Aure, Namijin da ya San iyakoki da qa'idojin Aure, ba kasafai s**a yawaita ba, sannan ba hakanan yake yarda ya qulla zuriar sa da yar mutane va, dole Yana buqatar sanin;

•Wani irin value ma za ki iya qarawa ga Rayuwar sa?
•Qualities dinki
•Potential dinki.
•Da Kuma ta wata hanya ma za kuyi complementing din juna??
Tunda ance "AURE rabin addinin mutum yake cikewa, Kuma kece za ki cika masa gurbin da ya rasa, idan Kuma mace haqarqarin Namiji ce, to shin me kika qunsa da Zaki cike wannan duk gurbin??

🤎Qanwata! Lissafin Aqili kenan, ba Lissafin yan saman katanga ba.

🤎Dakata Qanwata! Aqili baya buqatar Hoda, Jan baki, fitsara, rashin ta ido, fizge-fizge, Boqare-boqare, ko Kuma nuna ke kin Kai Linta kafin ki fizgi Hankalin sa, ko ki burge sa, ko ya ji ya nutsu ki zamo tufafin sirrin sa na Biyu, wannan Lissafin sai Yan ta more, masu Auren shekara daya wata 10...daga Nan su fara Miki kallon hadarin kaza, ko kallon "kasuwar ai ta watse...✍️

Ki jira me Hankali, ki jira wanda zai dauke ki a cikin mutunci da daraja, ki jira me gani da tunani, da yardar Allah zai zo, Kuma zai ganki, Kuma Alqawarin Allah zai cika a kanki da izinin sa.

Allah ya zaba Miki Alkhairi. Ameeeen.

Zoohrah Oummu Deederht ✍️

04/09/2026

Mata wai kuma kuna ganin Namiji akan hanya ko wajen biki, kuji kamar ku tsaidashi ku mishi magana akan kuna sonshi?

02/09/2026

Duk wanda yake da wata damuwa to ga Magani daga Manzon Allah 😍❤️

Big shout out to my newest top fans! 💎 Aishamuhammadtj Aisha, Ibrahim Sani, Aliou Aboutourab, Sani Wakili, Mansur Aminu,...
02/09/2026

Big shout out to my newest top fans! 💎 Aishamuhammadtj Aisha, Ibrahim Sani, Aliou Aboutourab, Sani Wakili, Mansur Aminu, Umar Muhammad, Muhammad Sani Sadau Muhammad, Abdullahi D Hashim, Abdullahi Badamasi, Abdulrahman Bako, Dade Sabo Idrissa Idrissa Dade Sabo, Zaharaddini Ibrahim Saikanadashi, Yahya Ben Yahya Alhadj, Aisha Bello, Alameen Sadauki Nuhu, Rashidatu Isma'ila, Muhammad Nura, Suleiman Zamani Shuaib, Najibu Aliyu Abbas, Yasmeen Isah, Muhammed Buba, Muhammad Sadeeq, Buhari Abubakar, Kabir Muhammad Dan, Abdulkadir Matawalle, Muhammad Rabiu Usman, Muhammad Auwal Drz, Isa Adamu Hassan, Moussa Mohamed, Abubakar D. Khalid, Gwagwaren Jibia, Hafsat Muhammad Sani, Nassirou Habibou, Abu Tazneem Comrade, Mas'ud Idris, Hafsat Mustapha, Al Ameen Yushau, Zainab Adamu Liman, Engr Saadu, Baaba Anharuddeen, Ibrahim Sani Garba, Muhammad Abdullahi Umar, Ahmed Shuwa, Fatimerh Zahrah, Zainab Muh'd Salis, Aliyu Adamu, Shehu Imam Itas, Comr A Paka

Drop a comment to welcome them to our community,

Maza Kuji da kyau..!Da yawan mata na son miji ko saurayin da zai tsaya masu a harƙoƙin su na rayuwa, ba wai kowane lokac...
01/09/2026

Maza Kuji da kyau..!

Da yawan mata na son miji ko saurayin da zai tsaya masu a harƙoƙin su na rayuwa, ba wai kowane lokaci bane kalmar Ina sonki ina ƙaunarki ke tasiri a zuciyar mace ba. Abinda take buƙata ka nuna ma ta son a aikace, ba a baki ba. Ka ba ta duk wata gudunmuwa da kake gani za ta taimaka ma ta a rayuwa wajen cikar burin ta.

©️ Nusaiba Tasiu Abdulrahim

01/09/2026

Inde yana cemata karbi tana um um um 😀😀

01/09/2026

Mata kuji da kyau Duk wadda ta Dauki KEWAYENTA sune zasuyi..

31/08/2026

Duk wanda ya yarda da haka bazai yi hassad ba

31/08/2026

Akwai inda akeso ka tafi. Hankali akwai inda ake so kayi sauri

Address

Katampe Ext. Abuja
Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nαzαrin Mαi Hαnkαli posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Nαzαrin Mαi Hαnkαli:

Shortcuts

Share