Ibrahim Chiroma Birnin Kudu - Baban Mahmud

Ibrahim Chiroma Birnin Kudu - Baban Mahmud TATTAUNA AL'AMURAN DA S**A SHAFI ADDININ MUSULUNCI CIKIN TSARI DA MUTUNTA JUNA. YIN NASIHA DOMIN GYARAN ZUKATA DA DABI'UN AL'UMMA A BISA MANHAJIN SALAFUS-SALIH.

23/07/2024

عن عائشة رضي الله عنها أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «إن الرفق لا يكون في شيء إلا زانه، ولا ينزع من شيء إلا شانه».
[صحيح] - [رواه مسلم]

13/07/2024

ZANGA-ZANGAR LUMANA, TSAKANIN MALAMAI, MAGADA ANNABAWA DA MATASA, TUSHEN AL'UMMA:

بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على رسول الله

Bibiyar abubuwan da suke faruwa a Kasata Mai cike da Albarka na matsaya da wasu cikin Malamanmu na Addinin Musulunci s**a dauka na kira ga gujewa Zanga-Zanga ko da an kirata ta Lumana, domin farkonta kawai aka sani, ba a san karshenta ba, da misalan da Malaman suke bayarwa na yadda ta kaya a wasu Kasashe kamar Sudan, Libiya da wasunsu, da kuma wasu cikin Matasanmu da kowace al'umma ke alfahari da su wajen gini da dorewarta, na ke ganin a matsayina na tsaka-tsakiya, wato ni ba Malami ba ni kuma kamar dai na gama tashi sai gangarawa ta ragemin zuwa kabarina, nake ganin ya kamata na ba da wadannan shawarwari:

Amma kafin shawarwarin, ina ba wa Malamanmu hakuri bisa wasu kalamai da wasu cikin wadannan Matasa s**a yi wadanda Sam basu dace ba, domin DARAJAR MALAMANKU, DARAJARKU. Don Allah Malamai ku yi hakuri ku yafe musu, fushi ne da kuma kaunarsu ga jama'a tare da damuwa da halin da TALAKAWA muke ciki na tsadar rayuwa ta ja s**ai wadannan kalamai, amma ina kyautata musu zato in a cikin salim-alim ne ba za sui irin wadannan kalamai ba. Allah Ya huci zukatanku Ya kara muku daraja Malamanmu.

1) Malamai: Tabbas Malamai ALLAH Ya h**e muku hanyar dakatar da wannan yunkuri na Zanga-Zanga. Ta yaya? Na'am, ku nada Manya-Manya cikinku mutum ASHIRIN tare da Manya-Manyan Pastoci da Fada-Fada na Kiristoci mutum ASHIRIN, kun ga ARBA'IN kenan ko??? To haka zaku je Fadar Maigirma Shugaban Kasa BAT ku isar da koken jama'ar Najeriya, ku ce masa ya yi abu uku ko kuma dai yadda kuka ga ya dace:

I) Ya bude bodoji, budewa ta gaske a shigo da abinci don jama'a su farfado daga sumar da suke ciki. Ku gaya masa YUNWA fa ake ciki ta bala'i. Na san ba zai so a ce wadanda yake mulka suna cikin yunwa ba.

II) A maida TALLAFI ta kowane bagare. Ta yaya ALLAH Zai tallafa maka Ya biya maka bukatarka Ya baka Shugabancin al'umma kai kuma ka ce ba zaka tallafa musu ba. Yanzu idan Uba ya ce ya dena tallafa wa 'Ya'yansa kanana ya yake so su rayu?? Wannan cire tallafin fa shi ne TURIN JEKA KA MUTU.Wadanda s**a koyi keke shekara hamsin baya sun san ma'anar TURIN JEKA KA MUTU.

III) A dauki Sojoji da 'Yansanda da sauran Jami'an Tsaro masu yawa, kowace Kasa Gwargwadon adadin Jami'an Tsaronta, Gwargwadon Kiyaye dokar 'Yan Kasarta.

Haba Malamai, ai kowa ya san zaku iya wannan aiki domin bai kai wahalar kokarinku ba yayin da kuka SULHUNTA Jamhuriyyar Nijar da ECOWAS. هذا والله أسهل من ذاك Sai mu kuma mu biku da addu'ar ALLAH YA BAKU NASARA DA DACE.

2) Matasa: Ku kuma ku bude kunnuwanku ku saurari Malamanmu idan s**ai mana wannan kokarin, ku yi musu da'a ku kyautata musu zato. ALLAH ZAI SHIGA LAMARIN INSHA ALLAH. Ku sani fa ba mu da wadansu Masu DARAJA da KIMA da MUTUNCI kamar Malamanmu. Mu zam masu neman ALBARKA. ALLAH YAI MUKU ALBARKA YA YAFE KURA-KURANKU YA YARDA DA KYAKKYAWAR MANUFARKU.

Amma fa KOWA ya sani, WALLAHI TALLAHI TALAKA YA GAJI, AN SHAKESHI, AN MAKURESHI, AN TAKURA MASA, AN KETA HADDINSA, AN KUMA KAISHI BANGO.

A GYARA kawai A Zauna LAFIYA.

Akwai Lokaci da za ai wani Abu daga nan zuwa 29 ga wata.

Idan har aka bari Matasa s**a boro, s**a bokaro, s**a fito to fa sai dai mu koma gefe guda mu yi ta Jan

لا حول ولا قوة إلا بالله

TATTAUNA AL'AMURAN DA S**A SHAFI ADDININ MUSULUNCI CIKIN TSARI DA MUTUNTA JUNA. YIN NASIHA DOMIN GYARAN ZUKATA DA DABI'UN AL'UMMA A BISA MANHAJIN SALAFUS-SALIH.

20/09/2022

Address

Abuja Quarters Gumel
Gumel

Telephone

+2348128986016

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ibrahim Chiroma Birnin Kudu - Baban Mahmud posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category