16/03/2022
GUSA! GUSA! GUSA!
Assalamu alaikum warahmatullah.
A jiya ne ƙungiyar dalibai ta wannan gari takai ziyara zuwa ga makarantar 'SENIOR SECONDARY' domin tattaunawa da kuma gani da ido akan ababen dake wakana a wannan makaranta.
Da farko, mun fara shiga ɓangaren malamai, ofishin shugaba, 'principal', yayin da muka zayyana masu dalilan ziyararmu, sannan daga bisani muka zanta da shi akan wasu daga cikin ƙalubalen da suke fuskanta.
Ya nuna rashin jin daɗinsa sarai akan; rashin zuwa makaranta (fashi) da dayawa daga cikin ɗaliban suke yi, sannan ya koka sosai wajen fincike yara mata da ake daga makaranta a yayin da suke gargarar kammala karatunsu na sakandare ɗin. "Za kaga yarinya ta ɓatar da shekaru da dama tazo har matakin aji uku na sakandare amma ba za'a barta ta ƙarasa wata uku ko huɗu ba, sedai ka ji anyi bikinta. Kaga kenan kamar tayi asarar wannan shekarun da ta yi a baya ne, tunda bata mallaki shedar karatu ba. Kuma ba ƴanmata ɗaya ko biyu ne hakan ta kasance da su, suna da yawa" - in ji shi. Waɗannan da ma wasu batutuwa, duk an tattaunasu, kamar rashin wadattun ɗakunan karatu.
Ƙungiyar tayi alƙawarin yin iya ƙoƙarin ta domin wayar da kan jama'a, musamman iyaye, akan tsige yara mata da ake daga makaranta *ba tare da wani dalili na dole ba.* A wannan ɓangaren ne muke sa ran zamu haɗa 'body' mai gwaɓi sosai wajen daƙile wannan matsala. Ina Sha Allahu.
Allah Ya kyauta.
Da muka koma ɓangaren ɗalibai, ajujuwa, mun yi bayanai ga su ɗaliban akan muhimmanci yin karatu, mallakar 'certificate' -SSCE, da kuma yadda 'absenteeism' (fashi) ke iya lalata karatu.
Sannan, mun gani da idonmu halin da suke ciki na rashin isassun 'Classes'. Domin aji uku (Sciences and Arts) suna aji guda, sannan suma aji ɗaya (Sciences and Arts) duk suna haɗe ne a mazauni guda. Sedai In za'ayi darasi wasu su fita daga ajin su bar wasu, wa iyayazu billah.😥
Abubuwan duk suna buƙatar kulawa sosai! Allah Ya bamu ikon kawar da su!
Shuaib Salisu
Secretary General
Gujungu Students Association