Abbas Babayo Gombi

Abbas Babayo Gombi Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abbas Babayo Gombi, Tutor/Teacher, Beside kasuwan Butu old market Gombi, Gombi.

25/02/2018

At This Day 25 Feb 1601
Robert Devereux, the second Earl of Essex and former favorite of Elizabeth I, is beheaded in the Tower of London for high treason.

WATAN ZULHIJJAH DA FALALAN DAKE CIKIN GOMAN FARKONTAFiyayen lokaci cikin ranakun mako shine juma'a sannan cikin watanni ...
21/08/2017

WATAN ZULHIJJAH DA FALALAN DAKE CIKIN GOMAN FARKONTA
Fiyayen lokaci cikin ranakun mako shine juma'a sannan cikin watanni sune watanni masu alfarma
Zulhijjah
Almuharram
Rajab
Sannan a cikin wadannan watanni watan Zulhijjah wato watan aikin Hajji cikin watan goman farko s**a fi falala wajen Allah s.w.t
KADAN DAGA CIKIN FALALAR GOMAN FARKO NA WATAN ZULHIJJAH
1.Allah yayi rantsuwa da wannan ranaku
ﺍﻟﻔﺠﺮ ﻭﻟﻴﺎﻝ ﻋﺸﺮ
Jamhurun malamai sun fassara wannan ranaku da goman farko na Zul Hijjah Alhafiz Ibn Kasir cikin tafsirinsa yace "wannan shine magana mafi inganci"
2. Idan watan Zul Hijjah ya tsaya babu kyau ga wanda keda niyan layya yayi aski ko yankan faratu annabi ya hana cikin sahihu muslim1977
3.Jigajigan rukunan musulunci ana samunsu ne cikin Zul Hijjah
~Tauhidi yadda alhazai suke talbiya
~Sallah ta idul adha
~Azumi ta yadda wanda bai samu hadaya ba zai yi azumi uku a aikin hajji bakwai inya dawo gida
~Sadaka tayadda wanda yayi tamattu'i ko kirani zai hadaya a rabawa miskinai da mabukata
~Aikin hajji da wannan babu wani watan da ake samun wannan aiyukan gaba ki daya sai cikin Zul Hijjah fathul-bari juzu'i na 2 shafi na 460
4.Aikin hajji na kankama ne cikin goman farko tun daga ranar takwas zuwa ranar sha uku ga wata
5.Ranar Allah yafi yanta bayi daga wuta cikin goman farko ne wato ranar Arfa
6.Cikin goman farko Allah ya umarci alhazai su ambace shi a Masha'arur-haram wato ranar goma ga wata
7.Azumin ranar Arfa na cikin goman farko ne wanda ake ranar tare ga wata ga wanda keda ikon yi kuma bai samu zuwa aikin hajji ba Azumin na kankare zunubin shekara biyu
8.Ranar goma ga wata alhazai suke jifar jamratul akaba kuma wanda yayi jifa zai kasance haske gareshi ranar tashin kiyama
9.Hadaya ga alhazai ko layya ga mazauna gida duk ana yinsu ne ranar goma ga wata
10.Cikin goman farko ake kabarbari sabanin sauran watanni kana ma ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺐ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ ﻭ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ
Abu Huraira da Abdullahi Ibn Umar suna fita kasuwa cikin goman farko suna kabarbari mutane suna kabbara da kabarbarinsu fathul bari juzu'i na 1 shafi na 458 cikin hadisin Abdullahi bn Umar yace Manzon Allah s.a.w yace
ﻣﺎ ﻣﻦ ﺍﻳﺎﻡ ﺍﻋﻈﻢ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭ ﻻ ﺍﺣﺐ ﺍﻟﻴﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﻓﻴﻬﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺸﺮ ﻓﺄﻛﺜﻴﺮﻭ ﻓﻴﻬﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻬﻠﻴﻞ ﻭﺍﺗﻜﺒﻴﺮ ﻭﺍﺗﺤﻤﻴﺪ
Ma'ana Manzon Allah s.a.w yace Babu wata rana da aiki na gari yafi daukaka da soyuwa ga Allah fiye da kwanaki goma na farkon Zul hijjah saboda haka ku yawaita wadannan kalmomin
La'ilaha illalah Allahu akbar walillahil hamd
11.Hafsa bint Umar radiyallahu anha tace
ﺍﺭﺑﻊ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻳﺪﻋﻬﻦ ﺍﻧﺒﻲ ﺻﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻼﻡ ﺻﻴﺎﻡ ﻋﺸﻮﺭﺍﺀ ﻭﺍﻟﻌﺸﺮ ﻭ ﺛﻞ ﺛﺔ ﺍﻳﺎﻡ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺷﻬﺮ ﻭﺍﻟﺮﻛﻌﺘﻴﻦ ﻗﺒﻞ ﺍﻟﻐﺪﺍﺓ
Ma'ana abubuwa hudu Manzon Allah s.a.w baya taba barinsu
~Azumin Ashura daya ga watan Muharrah
~Azumin goman farko na Zul Hijjah
~Azumin kwanaki uku a kowane wata
~Raka'a biyu kafin sallar asubahi
Musnad Imamu Ahmad Ibn Hambal hadisi na 25,920
12.Cikin wannan wata ne aka cika mana addini wato ranar Arfa kamar yanda Buhari ya ruwaito 4606
13.Fiyayyen addua itace adduar ranar Arfa tara ga watan Zul Hijjah
14.Watan Zul Hijjah shine cikamakin watanni sanannu wanda Allah yace ﺍﻟﺤﺞ ﺍﺷﻬﺮ ﻣﻌﻠﻮﻣﺎﺕ
15.Kuma cikin watan Zul Hijja ne Allah ke alfahari da bayinsa da s**a halarci Arafa
~Muhammad Ibrahim Baw~

13/11/2015

[[Like]]

Address

Beside Kasuwan Butu Old Market Gombi
Gombi
002

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abbas Babayo Gombi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category