Mal Muhammad Bappah Arabo

  • Home
  • Mal Muhammad Bappah Arabo

Mal Muhammad Bappah Arabo Man Kana Yu Min Billahi Wal Yaumil Akhir, Fal Yaqul Khairan Au Li Yasmut

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Talatin (30)*BANKWANA DA WATAN RAMADANAAlhamdulillah, muna godiya ga Allah da Ya ba mu dama...
19/03/2026

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Talatin (30)*

BANKWANA DA WATAN RAMADANA

Alhamdulillah, muna godiya ga Allah da Ya ba mu damar yin azumin watan Ramadana cikin rai da lafiya.

Allah Ya saukar mana da albarka, alkhairi, falala, wadata, ni’ima, gafara, rahama, lafiya mai amfani, da kwanciyar hankali a gare mu, da zuriyarmu, da Musulmi baki ɗaya.

Ya Allah, Ka ‘yanta mu a cikin wannan wata mai alfarma.

Ya Allah, Kai Mai Afuwa ne, Ka yi mana afuwa, Ka gafarta mana, da iyayenmu, da dukkan Musulmi.

Ya Allah, Ka zaunar mana da ƙasarmu lafiya, Ka yafe mana zunubanmu, Ka kuma karɓi ibadunmu.

Amin, Ya Hayyu, Ya Qayyum.

A yaɗa (sharing) domin al'umma su amfana..

18/03/2026

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Ashirin Da Tara (29)*

BANKWANA DA WATAN RAMADANA

Kada ka yi nadama da tafiyar watan Ramadan. Ka mai da ko wanne lokaci kamar watan Ramadan ta hanyar ci gaba da ayyukan alkhairi da ka saba yi a lokacin azumi.

Ya Allah, ka sanya mu cikin waɗanda za a yanta daga wuta a cikin wannan wata mai albarka.
Ya Allah, kai mai afuwa ne, ka yi mana afuwa, ka gafarta mana, iyayenmu, da dukkan musulmi baki ɗaya. Amin.

A yaɗa (sharing) domin al'umma su amfana..

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Ashirin Da Hudu (24)*MU SANYA IKHLASI A CIKIN AYYUKANMU NA WATAN RAMADANAYa kamata duk mai ...
13/03/2026

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Ashirin Da Hudu (24)*

MU SANYA IKHLASI A CIKIN AYYUKANMU NA WATAN RAMADANA

Ya kamata duk mai azumi ya yi shi domin neman yardar Allah, ba don mutane su yabeshi ba. Muna jan hankalin kawunanmu: masu bayar da sadaka, karatun Alƙur'ani, ciyar da masu azumi, masu tafsirin Alƙur'ani, masu dukkufa da ibada, masu zuwa umara, limamai masu rera tilawa, da masu sauraron ayyuka na gari, da duk abin da muke yi domin yardar Allah.

Lallai in muka sanya riya a cikin wannan ibadarmu, haƙiƙa mun yi asara mai muni.

Allah ƙara tsayar da zuciyoyinmu mu yi ibada dominsa. Amin.

Ku yaɗa domin al’umma su amfana.

Barkan mu da safiyar Jumma'a ta ƙarshe a Ramadan

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Ashirin Da Ɗaya (21)*GOMAN ƘARSHE NA RAMADANA yau, mun shiga cikin goman ƙarshe na azumin w...
10/03/2026

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Ashirin Da Ɗaya (21)*

GOMAN ƘARSHE NA RAMADAN

A yau, mun shiga cikin goman ƙarshe na azumin watan Ramadan, ranakun da Allah Madaukakin Sarki ya sanyawa albarka. A cikin wadannan ranaku ne aka ware dare mafi daraja a shekara, wato Lailatul Ƙadri.

A wannan lokaci mai albarka, ana buƙatar bawa ya dage da ibada matuƙa, mu ƙara neman kusanci da Allah ta hanyar sallah, karatun Al-Qur'ani, istigfari da addu'o'i. Wannan dama ce ta neman dacewa da gafarar Allah.

Allah ya bamu ikon dacewa da daren Lailatul Ƙadri, ya sanya mu daga cikin bayin da zai karɓi ibadunsu, ya gafarta mana zunubanmu, ya amsa mana addu’o’inmu, ya kuma albarkaci rayuwarmu. Amin.

Ku yaɗa domin al’umma su amfana.

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Ashirin (20)*MU GYARA HALAYENMU A WATAN RAMADANA DA HAR BAYANSAIdan har ba mu iya guje wa z...
09/03/2026

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Ashirin (20)*

MU GYARA HALAYENMU A WATAN RAMADANA DA HAR BAYANSA

Idan har ba mu iya guje wa zunubanmu ba a lokacin da shaidanu suke a daure a watan Ramadana ba, to tabbas munfi su kansu Shaidanun Shaidanci da shu'umanchi. Domin hakan na nufin zunubin ya riga ya zama ɗabi’armu, ba wai tasirin shaidanu ba.

Ya Allah, ka ba mu ikon kamewa daga saɓonKa, ka sanya mu cikin bayinKa waɗanda Ka karɓi ibadunsu, kuma ka tabbatar da mu a kan hanya madaidaiciya har bayan Ramadana. Amin.

A raba (share) domin wasu su amfana.

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Goma Sha Bakwai  (17)*MU DAGE MU RIBAUTA A CIKIN WATAN RAMADĀNIbnu Rajab Al-Hanbaliy ya ce:...
06/03/2026

*TUNATARWAR RAMADAN: Rana Ta Goma Sha Bakwai (17)*

MU DAGE MU RIBAUTA A CIKIN WATAN RAMADĀN

Ibnu Rajab Al-Hanbaliy ya ce:
"Duk wanda bai ribatu a cikin wannan wata ba, to a yaushe zai ribatu?"

Wannan wata mai albarka dama ce ta musamman da bai kamata mu yi sakaci da ita ba. Mu dage da karatun Al-Qur’ani, mu yawaita sallolin dare, mu taimakawa mabukata, mu tuba da istigfari domin neman yardar Allah.

Ya Allah, ka sanya mu daga cikin bayinka waɗanda za ka karɓi ibadunsu a cikin wannan watan mai albarka. Amin.

Barkan mu da ranar Jumma'a , 🕋🕌📿

Mu kiyayi bin diddigi da yaɗa kuskuren wasu, kuma kada mu yi farin ciki da bayyanar aibin wani. Kowa da abin da yake ɓoy...
13/02/2026

Mu kiyayi bin diddigi da yaɗa kuskuren wasu, kuma kada mu yi farin ciki da bayyanar aibin wani. Kowa da abin da yake ɓoyewa a rayuwarsa. Mu kasance masu rufa asiri, masu mutunta juna, domin mutunci shi ne ginshiƙin zaman lafiya.

Jumma'at Kareeeem 🕋🕌📿

“Duk tsanani da wahalar aikin da mutum ke yi, roƙon wani ya fi shi wahala. Jarumi na iya faskare ya nemi kuɗi, amma zuci...
23/01/2026

“Duk tsanani da wahalar aikin da mutum ke yi, roƙon wani ya fi shi wahala. Jarumi na iya faskare ya nemi kuɗi, amma zuciyarsa ba za ta taɓa barinsa ya yi roƙo ba.”

Jumma'at Mubarak 🕌📿🕋

YA CANCANCI LAKABIN KHADIMUL QUR'AN Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shekara 102 a duniyaSheikh Dahiru Usman Bauchi ya shek...
27/11/2025

YA CANCANCI LAKABIN KHADIMUL QUR'AN

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shekara 102 a duniya

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shekara 100 a duniya yana karatun Qur'ani

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shekara fiye da 80 a duniya yana karantar da Qur'ani

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shekara fiye da 75 a duniya yana Tafsirin Al-Qur'ani Maigirma

Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi aikin Hajji da Umrah fiye da sau 300

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya haifi yara sama da 50 kuma duk sun haddace Qur'ani

Dubban daruruwan mutane sun haddace Qur'ani a sanadinsa

Bana tunanin a Nigeria akwai mutumin da ya yiwa Qur'ani hidima fiye da Sheikh Dahiru Usman

Duk kin gaskiyar mutum ya san cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya cancanci a kirashi da Khadimul Qur'an

Muna rokon Allah Ya sa Qur'ani ya ceceshi ranar hisabi

‎INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN: Sheikh Dahiru Usman Bauchi Ya Rasu‎‎Fitaccen Malamin Addinin Musulinchi A Nahiyar...
27/11/2025

‎INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN: Sheikh Dahiru Usman Bauchi Ya Rasu

‎Fitaccen Malamin Addinin Musulinchi A Nahiyar Afrika Sheikh Dahiru Bauchi Ya Rasu A Arewacin Najeriya.

‎An wayi gari da labarin rasuwar ɗaya daga cikin manyan malamai masu tasiri a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, mutum mai zurfin ilimi, basira da kishi ga ci gaban al’umma. Rasuwarsa ta bar babban gibi a duniyar ilimi da addini, musamman ga mabiya tariqa da ɗaruruwan daliban da ya koyar tsawon shekaru.

‎Marigayi Sheikh Dahiru ya shahara a fadin ƙasar nan da wajen ta wajen yada ilimin addini, gyaran tarbiyya, da kuma kira ga zaman lafiya, adalci da tsoron Allah. Kalamansa sun kasance masu lulluɓe da hikima, nasiha da tausayi—kamar yadda Annabi (SAW) ya koyar—abin da ya sanya shi abin koyi ga miliyoyin mutane.

‎A matsayin jagora mai gaskiya da jajircewa, Sheikh Dahiru ya sadaukar da rayuwarsa wajen gina al’umma, ilmantar da jama’a, da horar da dalibai waɗanda s**a yaɗa iliminsa zuwa yankuna daban-daban na duniya. Gudummawar da ya bayar ba za ta shuɗe ba, kuma tarihi ba zai manta da shi ba.

‎Al’umma daga sassa daban-daban na ƙasa na ci gaba da aika sakonnin ta’aziyya, suna bayyana shi a matsayin “tushe na ilimi” da “haske ga al’umma”.

‎Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa, Ya sanya kabarinsa cikin lambunan Aljanna.

‎Muna roƙon Ubangiji Ya ba iyalansa, almajiransa, mabiyansa da dukkan al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi.

Kayi abinda zaka iya daga Alheri kafin Lokaci ya kure maka, matukar kanada hali. Kyautatawa Iyaye, Iyali, Yan'uwa da abo...
07/11/2025

Kayi abinda zaka iya daga Alheri kafin Lokaci ya kure maka, matukar kanada hali. Kyautatawa Iyaye, Iyali, Yan'uwa da abokan Arziki, Sadakatul Jariya. Za ka ci ribar su Duniya da Lahira.

Jumma'at Kareeeem 🕋 🕌 📿

Zaka iya ɓuya, amma ba zaka iya ɓoye gaskiyar halinka ba. Kamar yadda jakin nan bai iya ɓoye kunnuwansa ba a bayan bishi...
08/10/2025

Zaka iya ɓuya, amma ba zaka iya ɓoye gaskiyar halinka ba. Kamar yadda jakin nan bai iya ɓoye kunnuwansa ba a bayan bishiyar nan, haka ma mutum ba zai iya ɓoye ainihin halinsa daga mutane gaba ɗaya ba, musamman Allah Madaukakin Sarki.

Wannan yana nuni da cewa, komai yawan ƙoƙarin da mutum zai yi wajen ɓoye gaskiya ko aikata ƙarya, wata rana gaskiyar za ta bayyana fili. Duk abin da kake aikatawa a duniya, ka tuna cewa Allah yana ganin ka, kuma babu abin da zai ɓuya gare Shi.

Saboda haka, ka tuba da gaskiya, ka daina duk wani laifi da kake aikatawa, domin Allah yana karɓar tuban bawansa idan ya tuba da zuciya ɗaya.

Allah ya sa mu dace a duniya da Lahira.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mal Muhammad Bappah Arabo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Want your school to be the top-listed School/college?

Share