Nurul Qur’an school Gombe

Nurul Qur’an school Gombe An Islamic oriented school

25/05/2026
16/05/2026

Ziyara wajen Musabaqa

Yau wasu daga cikin daliban mu da malamai sun Samu daman ziyara wajen Musabaqan Qur’ani da ake gabatarwa na makarantar Malja’us Sunna Nasarawo Gombe

25/04/2026

ALHAMDULILLAH

Wata Baiwar Allah ta turo Mana da Tankin Ruwa kyauta zuwa Makarantar Nurul Qur'an Nasarawo yau Asabar 25/04/2026, Wanda Muka cika Dam din mu 2 Mai Durum 20, sannan Muka rabawa mutanen anguwa sauran.

Kusan kullum wannar Baiwar Allah tana turo Tankin Ruwa anguwar Nasarawo kyauta a rabawa mutane.

Muna Addu'a Allah ya biya mata Bukatunta na Alkairi ya yaye mata damuwar ta, Allah ya jikan iyayenta, Allah ya karawa rayuwar ta Albarka.

SIGN:
Management

Innalillahi wainna ilaihi rajiun!Allah yayiwa daya daga cikin iyayen daliban mu rasuwa *Mal. Sani (Dan Achaba)* sanadiyy...
13/04/2026

Innalillahi wainna ilaihi rajiun!

Allah yayiwa daya daga cikin iyayen daliban mu rasuwa *Mal. Sani (Dan Achaba)* sanadiyyar hatsari, a hanyar Darazo.

Wannan bawan Allah duk term shine mutum na farko da yake fara zuwa ya biya kuɗin makarantar yarinyar sa, duk da bashi da karfi sosai amma yana kokarin ganin ya cika duk wani qa'idar makaranta akan lokaci.

Jana'iza, yau Litinin 13th April, 2026 da karfe 11am, a kofar gidanshi dake Opposite da gidan Hon. Tita, a kan titin Nassarawo, Gombe.

Allah ya rahama mishi da sauran magabatanmu. Ameen.

*NURUL QUR'AN SCHOOL NASSARAWO QUARTERS GOMBE.* _ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH_ *SANARWAN DAWOWA DAGA HUTU GOBE ALHAMIS...
01/04/2026

*NURUL QUR'AN SCHOOL NASSARAWO QUARTERS GOMBE.*

_ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH_

*SANARWAN DAWOWA DAGA HUTU GOBE ALHAMIS 02/04/2026*

Wannan makaranta me Albarka tana farin cikin sanar daku abubuwa kamar haka:
1. Insha Allah *GOBE ALHAMIS 02/04/2026* zamu dawo Makaranta tareda fara sabon Shekara *(2026/2027 Academic Session)*
2. Har yanzu MUNA SAYAR DA *FORM* TAREDA DAUKAN SABBIN ƊALIBAI.
3. Ranakun zuwa makaranta, kwana 4 a sati ( Alhamis, jumma'a karfe 03:00pm zuwa karfe 05:30pm Asabar, Lahadi karfe 09:00am zuwa karfe 01:00pm)

*SIGN*
_Idris Abdulmumini_
08067643475
_School Head_

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RA’JIUN!Allah ya yiwa Alhaji Sa’idu Muhammad (Marafan Tumu) rasuwa a safiyar alhamis dinnan b...
26/03/2026

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RA’JIUN!

Allah ya yiwa Alhaji Sa’idu Muhammad (Marafan Tumu) rasuwa a safiyar alhamis dinnan bayan gajeruwar jinya a wani asibiti dake birnin Kano bayan ya dawo daga ibadar umrah kafin ya karaso Gombe.

Alhaji Sa’idu Muhammad (Marafan Tumu) Ya kasance Mahaifi ne ga Mu'assis na wannan Makaranta ta Nurul Qur'an, Wanda ɗansa Alhaji Abdullahi Sa'idu marafa ya gina ta a matsayin wakafi.

Ana sa ran idan Allah ya iso da gawar tasa za’a masa janaza a masallacin JIBWIS na Bolari Gombe a yammacin yau alhamis ko zuwa ƙarfe 4:00pm insha Allah……….Ya danganta da yadda s**a iso.

Marafa mutum ne mai ƙoƙari wajen gina masallatai da masallata da sauran ayyukan addini.

Muna ta'ziya zuwa ga iyalansa da sauran yan uwa musulmi.

Muna addu'a Allah ya gafarta masa.

20/03/2026

*GAISUWAR SALLAH 2026/1447*
‎
‎ _Assalamu Alaikum_

‎A madadin Hukumar wannan makaranta ta *NURUL QUR'AN SCHOOL NASARAWO GOMBE* Muna muku gaisuwar sallah Tareda fatan Alkairi.
‎
‎Allah ya Karbi ayyukan Alkairi da muka gabatar ya yafe mana kura-kuran mu, Allah mai-maita mana.
‎
‎تَقَبَّلَ ٱللَّهُ مِنَّا وَ مِنكُمْ صَالِحَ ٱلْأَعْمَالْ
‎عِيدُكُمْ مُبَارَك كُلُّ عَامً وَأَنتُمْ بِخَيْرٍ
‎
‎TAQABBALALLAHU MINNA WA MONKUM SWALIHAL A'AMA.
‎EDUKUM MUBARAK, KULLU AMIN WA'ANTUM BI KAIRIN.
‎
‎✍🏼
‎Idris Abdulmumini
School Head
‎08067643475
‎

Address

No 10 Opposite Late Alhaji Na’Amadu House, Nasarawo Street Gombe
Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nurul Qur’an school Gombe posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category