20/06/2025
DAULAR UMAWIYYAH
(41-132 bayan hijira)
RUBUTAWA siddeeq Ahmad Abubakar kumo.
Kwana Wata:22/08/2023
FASALI NA FARKO: LOKACIN MU'AWIYAH R.A
1-wanna daula ta kafu ne karkashin jagoranci sahabi Mai daraja Mai rubuta wahayi a lokacin manzon Allah salati da Aminci su tabbata gare shi,shine mu'awiyah bn Abi Sufyan,lallai wanna bawan Allah an yada karya akan shi makiya sunyi batanci akan shi .
Ya fara jagorancin sham tun lokacin Umar haka uthman ,a lokacin khilafah rashidah yayi jagoranci na shekaru 20 ,bayan ta ma yayi 20.
2-sababin kafuwar daular shine Alhasan jikin manzon Allah ya sauka daga jagoranci ya Mika mishi da ya jagoranci al'ummah gaba daya ,Wanda ana Kiran wannar shekarar da shekarar hadewa akan gaskiya,shekara ta 41 bayan hijira,shine farkon kafuwan daular ,zuwa shekara ta 132 rushewanta.
Bayan khilafah rashidah Babu daulah da tayiwa addini aiki da yada musulunci da Sunnah kamar wannar daular,shiyasa Yana daga cikin illar da akeyiwa daliban ilimi shine rashin Basu ingantacce madogara a tarihi ,su ta kwaso bayanai daga karkatattu wadanda suke s**an mutanen kirki su rike shi a matsayin madogara.
3-ta fuskar bude garuruwa kuwa ta bude garuruwa ta yankuna mabanbanta yankin rum da Yankin Bukhara da khurasan da yankunan Africa da Andalus da sauran su.
Uqbatu bn nafi'i alfihri shine Wanda ya bude yankin jaza'ir ...........
4-muawiyah ya tara committee na shura akan waye yakamata ya maye gurbin shugabanci saboda lura da abubuwan da s**a faru na fitintinu Yana tsoron ayi sabani bayan shi,sai aka nuna Dan shi yazeed bn mu'awiyah ,ya jarraba shi akan shugabanci kafun ya bashi.
Anan mu kula akwai kare rayin da ake yadawa akan yazeed na cewa Yana shaye shaye da sauran abubuwan s**a ,duka wadanna suna bukatan madogara ingantacce Wanda shine aka rasa,mafi karanci mutum ya kame bakin shi akan yada wadanna abubuwan .
5-sai mu'awiyah yaso ayiwa yazeed mubaya'ah tun Yana Raye saboda haka yayi umurni da ayi ,kowa yayi sai sahabbai guda hudu:
Abdullahi Dan Abbas
Abdullahi Dan Umar
Alhasan Dan Aliyu
Abdullahi dan Zubair
Da mu'awiyah yaji haka sai ya tashi ya taho madina mutum biyu s**a tafi Makkah saboda Basu son a tsaya musanyar magana dasu Akai sune Alhasan da ibnu zubair ,sai ya zauna da ibnu Abbas da ibnu Umar s**a tattaunawa s**aji dalilan shi ,take s**ayi mubaya'ah ga yazeed