18/07/2026
TAƘARDAR TA'AZIYYA
ISLAMIYYAH SCHOOLS ASSOCIATION OF NIGERIA (ISAN)
Gombe State Chapter
Assalãmu Alaikum wa Rahmatullãhi wa Barakãtuhu.
Cikin matuƙar alhini da jimami, Islamiyyah Schools Association of Nigeria (ISAN), Gombe State Chapter, ta samu labarin rasuwar ɗaliba Amina Umar, ɗaliba a Al-Amjad Community Model School (Islamiyyah), Bomala, Gombe State, wacce ta rasu a ranar Jumma'a, 17 ga Yuli, 2026.
Bisa rahoton da muka samu daga malamanta, marigayiyar ta sanya wani magani a gashinta domin magance kwarkwata. Daga baya ta samu matsalar rashin lafiya mai tsanani wadda ta kai ga rasuwarta.
Wannan lamari ya girgiza zukatanmu matuƙa, musamman kasancewar marigayiyar na daga cikin ɗaliban da ke gab da kammala karatunsu.
Muna miƙa saƙon ta'aziyyarmu ga:
Iyayenta da iyalanta.
Shugabanci, malamai da ɗaliban Al-Amjad Community Model School (Islamiyyah).
Al'ummar Unguwar Bomala.
Da kuma ɗaukacin al'ummar Musulmi.
Muna roƙon Allah (SWT) Ya jiƙanta da rahama, Ya gafarta mata, Ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarta, Ya ba iyayenta, 'yan uwanta, malamanta da abokan karatunta haƙurin jure wannan babban rashi.
A lokaci guda, muna kira ga iyaye da masu kula da yara da su riƙa yin taka-tsantsan wajen amfani da magunguna ko wasu sinadarai, musamman waɗanda za a shafa a jiki ko gashi. Yana da muhimmanci a tabbatar da amincinsu tare da neman shawarar ƙwararrun ma'aikatan lafiya idan akwai buƙata.
Muna addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya kare ɗaukacin ɗalibanmu daga dukkan musibu, Ya albarkaci makarantunmu, Ya kuma ba mu ikon kula da amanar yaranmu yadda Ya yarda.
﴿إِنَّا لِلَّٰهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ﴾
✍️
Islamiyyah Schools Association of Nigeria (ISAN)
Gombe State Chapter