05/09/2023
MALAM JA'AFAR BA DAN BOKO HARAM BANE
Wani Malamin bidi'ah boka mushriki ya fito yaci mutuncin Marigayi Malam Ja'afar ya kuma alakanta shi da Boko Haram, sai dai daga baya ya janye maganar bayan yaji za'a gurfanar dashi a Kotu
Abubuwan da zai sa mutum ya alakanta Malam Ja'afar da Boko Haram gasu k**ar haka:
(1) Kiyayya
(2) Banbancin akida
(3) Jahilci
(4) Wauta
(5) Dakikanci
Kiyayya: Idan kana kin mutum tabbas zaka iya masa sharri da kage idan har baka kasance mai adalci ba
Banbancin akida: Duk wanda zai budi bakinsa mai wari yace Malam Ja'afar dan Boko Haram ne idan ka duba zaka samu yana da banbancin akida da shi, akida na sa a wani lokuta a kasa yiwa juna adalci har ma ya kai ga sharri
Jahilci: Makiya Musulunci da suke da hannu a kafa Boko Haram sun ribaci jahilai matukar ribata, duk lokacin da jahili zai yi magana akan abinda bai sani ba to yana nunawa duniya jahilcinsa ne
Wauta: Wawaye su kan kafa hujja da maganar makiya ne ko abinda s**a ji a bakin wani ba tare da bincike ba, wauta kan sa mutum ya kasa fahimtar hakikanin gaskiya, domin har yanzu akwai wawayen da s**a kasa fahimtar makircin Boko Haram s**a koma yiwa su Malam Ja'afar sharri
Dakikanci: duk lokacin da dakiki zai yi magana da wahala kaga akwai ma'ana a cikinta, dakiki ne kawai zai dubi Malami irin Ja'afar yace masa dan boko haram, kiran Malam Ja'afar dan Boko Haram tsantsar dakikanci ne
Su kansu mayakan Boko Haram din da Shugabanninsu na farko da na karshe sun san Malam Ja'afar ba dan kungiyarsu bane, sun sha alwashin daukar rayuwarsa, kuma su s**a kashe shi bayan sun dawo daga Kasar Algeria koyon ayyukan ta'addanci tun kafin kaddamar da yaki a lokacin da suke gina akidar a cikin zukata
Mutane suna cikin duhun jahilci game da sha'anin Boko Haram da sirrinta da manufar kafata, har yau sun kasa fahimtar wadanda s**a tsara rikicin Boko Haram
Shiyasa yau ake samun wadanda suke zargin Malamai irinsu Malam Ja'afar da cewa sune s**a kafa Boko Haram saboda dakikanci da wauta
Ina tunawa, a wa'adin farko na Gwamnatin Buhari, an taba yin wani taro a jami'ar BUK inda aka gayyato Malamai da sauran kwararru a fannin tsaro aka tattauna mas'aloli akan Boko Haram da ayyukan ta'addanci domin a nunawa duniya tsantsar gaskiya akan Boko Haram
Irin wannan taro ne da ya k**ata ana gudanar dashi a kalla sau daya a duk shekara saboda fa'idarsa, amma tun da akayi sau daya ba'a sake yi ba
Muna da kundin bayanai na sirri da bincike da muka haddace a kwakwalwar mu akan Boko Haram, idan Allah Ya ja kwanan mu a duniya har Littafi akan tarihin Boko Haram da manufofinta sai mun fitar, a yanzu matsayin mu bai kai mu fitar ba saboda hatsarin dake tattare da hakan
Yaa Allah Ka karbi shahadar Malam Ja'afar da Albaniy Zaria
Allah Ka hadamu da su a cikin Aljannah Madaukakiya