15/02/2026
📚 MADARASATU KHITAMUHU MISK LITTAHFIZUL QURAN WAD DIRAASATIL ISLAMIYYA 📚
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Sakon Rufe Makaranta Da sanarwar daurah– Khitamuhu Misk Islamiyya, Gombe
Assalamu Alaikum Warahmatullah,
Muna godiya ga Allah (SWT) da ya ba mu ikon kammala jarrabawar zangon karatu na ɗaya (1st Term) na shekarar 2026/1447H lafiya. Makarantarmu, Khitamuhu Misk Islamiyya Gombe, ta bada hutu a ranar Asabar, 14 ga Febreru 2026 / 26 ga Sha'ban 1447H. In sha Allah, za mu dawo karatu a ranar Asabar, 28 ga Marcht 2026 (09 ga Shawwal 1447H) da yardar Allah.
An gudanar da gasar Musabaqa da Quiz tsakanin daliban makaranta, inda aka gwada su a fannonin Al-Qur’ani, Hadith, Fiqhu, Tauhid, Sirah da Lugga (Larabci). Wannan gasa ta kara wa dalibai kwarin gwiwa da kuma azama a cikin neman ilimi. Mun taya wadanda s**a yi nasara murna, kuma muna fatan dukkan dalibai za su kara himma don samun nasara a gaba.
Muna ba da Sanarwar Daurah Ramadaniyya 2026 wadda za'a fara In Sha Allah ranar 1 ga watan Ramadan zuwa 30 ga Ramadan 2026.
(Cikakken bayanin na tafe)
Muna mika godiya ta musamman ga Shugaban Makaranta (Dr Abubakar Mohammed Gombe), Allah ya kara masa lafiya da daukaka. Hakika, malamai sun taka rawar gani wajen bayar da ilimi da tarbiyya, Allah ya saka musu da alheri. Mun kuma yaba da kokarin dalibanmu masu hazaka da iyayensu da ke goyon bayan su.
Muna godiya ga al’ummar Arawa, wadanda s**a karbi makarantar hannu bibbiyu, s**a ba ta goyon baya da kulawa. Allah ya bar zumunci, ya kara albarka a cikin al’ummarmu.
Muna rokon Allah ya sa duk abin da muka koya ya amfanar da mu a duniya da lahira. .
Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.
✍️ KHITAMUHU MISK GOMBE MEDIA