04/04/2026
SANARWAR NAN TAKE
4 GA AFRILU, 2026
ADC TA SANAR DA KAFUWAR TSARIN WAKILAI NA MUSAMMAN A MANYAN BIRANEN DUNIYA
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta sanar da kafa wani tsari na Wakilai na Musamman a manyan biranen ƙasashen waje, a matsayin wani sabon shiri na ƙarfafa hulɗarta da ƙasashen duniya da kuma inganta ɗaukar nauyin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Wannan shiri ya zo ne sak**akon karuwar alamu na ayyukan da ba su dace da dimokuraɗiyya ba da kuma hare-haren da ake kai wa ‘yan adawa da shugabanninsu tun daga watan Yuli 2025, ciki har da yunƙurin rusa jam’iyyun adawa, raunana sahihin tsarin shugabancin jam’iyya, da kuma takaita shiga harkokin siyasa cikin ‘yanci.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a Abuja, ta ce wannan tsarin Wakilai na Musamman an kirkiro shi ne domin samar da tsayayyun hanyoyin sadarwa tsakanin ADC da manyan masu ruwa da tsaki na ƙasa da ƙasa, musamman a ƙasashe da cibiyoyi da ke ba da muhimmanci ga dimokuraɗiyya, haƙƙin ɗan Adam da kuma bin doka.
A karkashin wannan shiri, jam’iyyar za ta naɗa amintattun mutane a matsayin jakadu a wasu manyan biranen duniya da aka zaɓa bisa muhimmanci. Wadannan wakilai za su kasance manyan hanyoyin sadarwa tsakanin ADC da ƙasashen waje, majalisun dokoki, kafofin yaɗa labarai na duniya, cibiyoyin tallafawa dimokuraɗiyya, da kuma ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje.
Ta hanyar waɗannan hulɗoɗi, wakilan za su riƙa bayar da bayanai akai-akai kan muhimman batutuwa da s**a shafi yanayin siyasar Najeriya, ciki har da ci gaban siyasa, matsalolin haƙƙin ɗan Adam, tafiyar da mulki na dimokuraɗiyya, ingancin zaɓe, da kuma zarge-zargen danniya ga ‘yan adawa. Haka kuma za su isar da manufofin ADC da shawarwarin gyara ga masu ruwa da tsaki na duniya.
A cewar jam’iyyar, babban burin wannan shiri shi ne tabbatar da cewa abokan hulɗar ƙasa da ƙasa da cibiyoyin dimokuraɗiyya suna samun ingantattun bayanai masu gaskiya game da yanayin siyasar Najeriya, maimakon dogaro da bayanan gwamnati kaɗai.
ADC ta bayyana cewa ta hanyar kafa waɗannan hanyoyin hulɗa a hukumance, tana ƙarfafa amincinta a matsayin jam’iyya mai kishin dimokuraɗiyya, tare da ƙara tabbatar da kanta a matsayin madadin gwamnati mai inganci da ke da biyayya ga ka’idojin dimokuraɗiyya da kundin tsarin mulki.
Bisa la’akari da tasirin wadannan birane a duniya, jajircewarsu ga dimokuraɗiyya, da kuma yawan ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, jam’iyyar ta zaɓi biranen Washington DC; London; Brussels; Berlin; Ottawa; Paris; Pretoria; Addis Ababa; Nairobi; Accra; Geneva; da New York a matsayin wuraren da za ta mai da hankali wajen hulɗar ta na ƙasa da ƙasa.
A wani ɓangare na wannan shiri, jam’iyyar za ta kuma kafa Tsarin tattara bayanai na ƙasa (National Documentation Initiative), domin tattarawa da rubuta duk wasu abubuwan da ke shafar shiga harkokin siyasa a fadin Najeriya. A karkashin wannan tsari, rassan jam’iyya na jihohi za su riƙa tattara bayanai kan abubuwa k**ar barazana, muzgunawa, hare-hare na tashin hankali, k**a ba bisa ka’ida ba, da kuma hana gudanar da ayyukan siyasa.
ADC ta jaddada cewa wannan shiri wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa hulɗarta da ƙasashen duniya, inganta yaduwar sahihan bayanai kan siyasar Najeriya, da kuma ƙara nuna jajircewarta wajen kare dimokuraɗiyya, alhakin shugabanci, da haƙƙin ‘yan adawa.
An sanya hannu:
Malam Bolaji Abdullahi
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa
African Democratic Congress (ADC)