Sheikh Isah Tsangaya Comprehensive Secondary School Talasse - Sitcoss

Sheikh Isah Tsangaya Comprehensive Secondary School Talasse - Sitcoss For a quality conventional and pure Islamic education.

10/10/2023

KIFI NA GANIN KA

Alhaji Buba ɗan kasuwa ne mai sukuni, yana kuma ba da bashi da ruwa. Duk sa'adda ya ɗibga wa mutum bashin da ya kasa biya, yakan kwace gidansa ko gonarsa, bai taɓa yafe bashi ba.

A cikin waɗanda ya tula wa bashi s**a kasa biya har da Malam Shehu, wanda yake da wata 'yarsa kwalbar ƙwaya. Alhaji Buba ya ce wa Malam Shehu, "sai ka aura mini 'yarka, ni kuwa in yafe maka duk bashin da nake bin ka."

Kodayake Malam Shehu bai so haka ba, to amma ya zai yi da abin da ya gagari wuta, in ji kishiyar ƙonanniya. In ban da lalura irin ta mugun tshon da ya lulluɓe shi da tamfal, watau talauci, yaya ma za a yi ya ba tsoho kuma mummuna k**ar Alhaji Buba 'yarsa?

Da Alhaji Buba ya ga Malam Shehu ya shiga duniya irin ta gizo, yana ta faman saƙe-saƙe a cikin ransa, sai ya ce masa, "domin in nuna maka adalcina, ka zo da 'yarka gidana gobe, zan yi mata ƙuri'a, abin duk da ta zaɓa, to babu makawa shi za a yi."

Kashegari Malam Shehu ya tafi da 'yarsa gidan Alhaji. S**a same shi zaune a farfajiyar gidansa fadawa kuwa, 'yan a-fito-da-tuwo-mu-ci, sun kewaye shi ana ta hira. Alhaji Buba ya ce, "kun zo? To, ƙuri'ar da zan yi wa 'yarka ita ce, zan sanya tsakuwa biyu, fara da baƙa, a cikin wannan jaka. 'Yarka za ta ɗauko tsakuwa ɗaya daga cikin jakar. Idan ta ɗauko fara, shi ke nan ba za ta aure ni ba, kuma na yafe maka kuɗin da nake bin ka. Idan kuwa ta ɗauko baƙar tsakuwa, to babu makawa ta aure ni."

Farfajiyar gidan kuwa cike take da irin 'yan ƙananan duwatsun nan na girabil. Alhaji Buba ya duƙa ya ɗauki tsakuwa biyu daga cikin duwatsun ya jefa cikin jaka da sauri. Babu wanda ya lura da cewa tsakuwoyin da Alhaji Buba ya sanya cikin jaka duka baƙaƙe ne, sai yarinyar kurum, da ma an ce kifi na ganin ka mai jar koma.

Da aka miƙa mata jaka domin ta ɗauko tsakuwa ɗaya, sai ta tsaya tana tunanin abin da ya k**ata ta yi, ta sani sarai duk tsakuwar da za ta ɗauko baƙa ce, watau za ta auri Alhaji ke nan. Shi kuwa Alhaji sai murmushi yake yi, karensa ya k**a zaki.

Can sai yarinya ta tuna da wata dabara. Ta saka hannu cikin jakar ta ɗauko tsakuwa ɗaya, tana fitowa da hannunta waje sai ta saki tsakuwar ta faɗi ƙasa cas, ta saje da sauran duwatsun da ke wurin. Ta ce, "kash, ta suɓuce mini. Amma a duba cikin jakar a ga wace tsakuwa ta rage."

Da aka duba sai aka ga baƙa, wanda ya nuna fara ke nan yarinya ta ɗauko, don haka babu maganar aure. Shi kuma Alhaji sai zare idanu, ba abin ya faɗi gaskiya ba a ce girma ya faɗi, wai raƙumi ya shanye ruwan kaza. Da haka dai Malam Shehu da 'yarsa mai hikima s**a ƙwaci kansu ga hannun Alhaji Buba.

Don haka komai za mu yi, mu tsaya mu yi tunani, tamkar yadda 'yar Malam Shehu ta yi. Kowace matsala na da mafita sai in ba a tsaya an yi tunani kanta ba.

A yi SHARE domin wasu ma su amfana.

Bukar Mada
09/10/2022

09/10/2023

Mai Alqur'ani'ani ke nufi da ?
✍️ Jaafar A Sarki

Kalmar Shaytăn an ciro tane daga (شطن) wacce ke nufin abinda bai da tsarki ko Makaskanci.

Shaytăn na nufin wani (entity) dake bijirewa wata ka'ida (rebellious) - kuma wannan zai iya kasan cewa a mutane ko Aljanu ko a dabbobi. A wata ma'anar Shaytăn na nufin; ran (soul) daya nesanta kansa daga Allah da kan turbar gaskiya.

Abinda zamu lura anan shine, Shaytăn sunane na gama gari wato (common noun) ne' amma shi kuwa sunane na ainihi (proper noun).
Wato dai abinda nake nufi anan shine, dukkan abinda yake cutarwa ko kaucewa wata ka'ida to wan nan abun shi ake nufi da - abun kuwa mutum ne ko waninsa. Shi kuma shine sunan Shaytăn din daya yaudari Babammu Ādam (a.s) kuma har yanzu yake cigaba da yaudarar Banī Adam tare da rundunarsa.

Ga wata ayar Qur'ani dana kawo a kasa wacce zata kara fahimtar damu kalmar na nufin dukkan abinda ke cutarwa - ko kuma ya kaucewa tafarkin gaskiya, yake kuma haifar da rikici, găba (enmity), rarrabuwa da barna (corruption) a tsakanin al'umma

Allah yana cewa ; انمايريد الشيطان ان يوقع بينكم() العداوۃ والبغضاء)
"Hakika ba wani abu Shaytăn ke nufiba illa ya haifar da Găba da Kiyayya a tsakaninku"

A wata ayar kuma, kalmar Shaytăn na nufin mutum mabarnaci mai cutarwa.

Qur'ani na cewa: (و كذللك جعلنا لكل نبي عدوا شياطين الانس و الجن)
"Kamar haka muka san yawa kowane annabi makiyya daga mutane da aljanu"

Saboda haka an ambaci da Shaytăn ne saboda barnarsa da mugun nufin dake tare dashi.

Hatta kwayoyin cuta (pathogenic organisms) na nufin Shaydanu.

Ga dalilin k**ar haka: Imam Ali (as) yana cewa: (لا تشربوا الماء من ثلمۃ الاناء و لا من عروته فان الشيطان يقعد علی العروۃ و الثلمۃ)

" Kada dayanku yasha ruwa daga wani abunsha (glass) ta bangaren daya tsage ko ya gutsure ko daga wajan marikin (handle) domin Shaytăn na zama a akan handle ko wajan daya b***e (broken)

Imam as-Sadiq ya kuma cewa: (و لا يشرب من اذنذالكوز ولا من كسره ان كان فانه مشرب الشياطين)

"Bai k**ata asha ruwa ta bangaren marikin (jug) ba ko ta bangaren daya karye, domin wurarene da suke mashaya ga Shaytăn (germs)

Annabi (s) yace: Kada ku tsawaita gashin bakinku (moustaches), domin Shaytăn (germs) na maida wajan mafaka (safety).

To anan zamuga ta bayyana garemu ma'anar Shaytăn na nufin microbes da suke haddasa mana cututtuka.

Saboda haka anan zamu fahimci Shaytăn nada ma'anoni daban daban, mafi shahara shine da mataimakansa; mutum mabarnaci na nufin Shaytăn; ayayin da hatta bacteria da Viruses dss na nufin .

Allah ya karemu daga sharrin Shaytăn koma wane iri s**a kasance.

13/07/2019

Ga hazo ga haɗari. Wani abu sai Climate Change.
06/10/2023

Ga hazo ga haɗari. Wani abu sai Climate Change.

05/10/2023

In kin san ke kaɗai ce a wurin mijinki yana da kyau ki rinƙa yi masa faɗa akan muhimmancin ƙara aure

Ki rinƙa nuna masa hotunan ƙawayenki kuma kina gaya masa kirkinsu da kuma kyawawan ɗabi'unsu domin kin fi kowa saninsu.

Ki takura masa sosai, ki yi masa magiya kuma ki ja hankalinsa sosai ta hanyar nuna masa ladan aikata hakan.

A ƙarshe, zaki samu ladan taimakon ƴar uwarki da ladan farantawa mijinki rai da kuma ladan ƙarfafa sunnah.

Duk wata ƙawa da take MUMINA tabbas zata so ta ga ƙawarta cikin jin daɗi da annashuwa.

Wannan shawara ce zuwa ga mata Muminai!

03/10/2023

"6 Major Findings about Tinubu from the CSU Documents

By Farooq Kperogi

Both pro- and anti-Tinubu news outlets and blogs are selectively reporting the documents that Chicago State University handed over to former Vice President Atiku Abubakar yesterday. Here are 6 non-partisan tidbits I discovered from poring over them:

1. Chicago State University’s Office of the Registrar affirmed that Bola A. Tinubu indeed attended the university “from August 1977 through June 1979” and was “awarded a Bachelor of Science in Business Administration with Honors on June 22, 1979.”

The registrar also swore to this under oath. The penalty for lying under oath in America can be steep. It is punishable by up to 10 years in prison.

This information is consistent with my September 2, 2023, column titled, “Tinubu Definitely Graduated from Chicago State University.”

2. The certificate (we call it “diploma” in the US) that Tinubu submitted to INEC is inconsistent with the certificates CSU issued in 1979 and subsequently, indicating that Tinubu forged his. (In the US, diplomas are mere ceremonial documents that most employers don’t ask for. Transcripts directly from universities are the usual ways to verify attendance and graduation.)

Although he did legitimately graduate from Chicago State University in 1979, he obviously lost his certificate and, instead of applying for a replacement, decided to forge it.

That strikes me as mysterious self-harm. It costs only $26 to get a replacement diploma from CSU. But it takes between eight and 10 weeks to receive it after filling out the Diploma Replacement Order Form.

My guess is that, in the typical last-minute, fire-brigade approach to things among Nigerian elites, Tinubu didn’t plan ahead and didn't have enough time to apply for his replacement diploma from CSU to meet INEC's deadline and decided to visit Lagos’ infamous “Oluwole” for a counterfeit replacement.

3. The Southwest College transcript that Tinubu used to get admitted to Chicago State University belongs to a female. I had questioned the authenticity of the transcript because of the many errors in it, such as the date and social security number. We await what CSU has to say about this.

This reality, though, seems to validate uncorroborated but long-standing whispers from the grapevine that Tinubu, who was allegedly born Lamidi Amoda [Yoruba Muslim domestication of Abdulhamid Ahmed] Sangodele in Osun State’s Iragbiji, stole the identity of a female Bola Adekunle Tinubu to go to America.

4. Nonetheless, this whisper may be difficult to sustain in light of the fact that Tinubu’s Chicago State University admission letter dated August 23, 1977, was addressed to “Mr. Tinubu,” not Ms. or Miss Tinubu.

Was the “F” in the transcript from Southwest College a clerical error, especially because the social security number and the dates were also clerical errors? Or was there a cover-up somewhere?

Well, we saw from the documents released to Atiku that after accepting his transfer credits from Southwest College (which later became Daley College), CSU required Tinubu to take qualifying exams in English, math, and reading, which he passed. Why did CSU allow a man who presented a transcript that belonged to a woman to take qualifying exams as a man?

Tinubu obviously identified as a man throughout the two years he studied at the school. A Nigerian CSU graduate and classmate of Tinubu’s swore under oath that Tinubu ran for and won election as president of CSU's accounting students’ association. His yearbook photo from 1979 also clearly showed a younger version of Tinubu.

And Tinubu’s handwriting and signature in the June 27, 2022, Consent to Release Student Education Records form, which authorized CSU to release his academic records to one Oluwole Afolabi of 3 Roosevelt Avenue, West Orange, New Jersey, seems to me similar to his handwriting and signatures in his CSU records.

Finally, if he used a woman’s associate degree from Southwest College to gain admission to CSU without having any background in accounting or business administration, his performance at CSU was perplexing. Of the more than 30 courses he took there, he got C’s in only three courses. The rest were A’s and B’s, which earned him honors.

5. The Bola A. Tinubu who applied to Southwest College for an associate degree in 1975 claimed to have attended Government College, Lagos, and presented a 1970 GCE A-level result with grades E in Chemistry and Biology and an F in Physics. The problem is that Government College, Lagos, was established in 1974. So, there’s a chronological conundrum there, which signposts forgery.

The GCE A-level result also shows that “Bola A. Tinubu” took the exam as an HSC student, which used to be a two-year study after 5 years of secondary school education. In other words, the owner of the certificate must have graduated from secondary school at least in 1968.

It’s not clear at the moment if the GCE A-level result is fake or authentic—or if it belongs to the man we know today as President Bola A. Tinubu. My hunch is that it doesn’t belong to him. But this will become clear in the coming days.

6. Tinubu tells the world that he was born on March 29, 1952, but the birthday recorded in his CSU transcript says he was born on March 29, 1954. The space for birthday in the Southwest College transcript he submitted to CSU is blank. So is the record of his secondary school education. These facts added to my previous suspicion that the transcript was probably fake.

If he was born in 1954, it means he was 14 years old when he graduated from high school.

Bonus: Tinubu’s last name was misspelled in a few of the CSU documents. I thought the “THUBV” misspelling in his final graduation record was bad enough until I saw “Tinububu” in one of the documents.🤣 Bubu, remember, is Buhari’s nickname among a vast swath of Nigerians. Make of that what you will.

We should all thank VP Atiku Abubakar for his doggedness, which has helped us to get this much clarity about Tinubu’s past."

13/01/2023

Official JAMB UTME registration fees, ahead of 2023 registration kickoff
.
JAMB has released the official cost of getting the registration form for the 2023 UTME. Candidates will be required to make a total payment of N5,700 to successfully register for the exam. Candidates who indicate interest to write the mock exam will be required to make an extra N1,000 payment, a total of N6,700. While Direct Entry (DE) applicants will be required to make a total payment of N4,700 to successfully apply.
For all prospective candidates for the 2023 UTME, you ought to start preparing for your exams now. The mock exam has been fixed for 16th March 2023.
You can find below, the breakdown of the cost to register for 2023 UTME, if you intend to know precisely how much you will spend to get the 2023 UTME form;
All transactions with JAMB are cashless. You are not to make any cash payment to any CBT centre as JAMB has already included their fees in the total cost of registration.
1. UTME/DE application fee - N3,500
2. Reading text (book) - N500
3. CBT centre - Registration Fee - N700
4. CBT centre - examination fee - N1,000
5. CBT centre - mock examination fee (where indicated) - N1,000
Before registration for 2023 UTME commences on 14th January, make sure you have already generated your profile code.
Candidates can also consult with parents, guardians and mentors to select the best course and school for them, using references from both the Latest JAMB syllabus and the Latest JAMB brochure.

Happy 20th Anniversary Bala Waja the fifth
02/08/2021

Happy 20th Anniversary Bala Waja the fifth

07/04/2021

Yau daliban wannan makaranta s**a samu hutun karshen zangon karatu na biyu na 2020/2021.

Wanda da yardar Allah da kudirarsa dalibai za su dawo zangon karatu na uku daga ranar 17-05-2021.

Muna rokon Allah yasa muyi azumi lafiya kuma mu sha ruwa lafiya,ya h**e mana abinda za mu yi hidimar addininsa dashi, albarkacin Manzon Allah (S.A.W) 👨‍🎓👩‍🎓👩‍🎓👩‍🎓👩‍🎓👩‍🎓👨‍🎓

©️ SITCOSS TALASSE

26/01/2019

SIYASA DA MALAMAN ADDINI...
Addini sako ne na Allah Mahalicci
zuwa ga daukacin bayinsa, sako ne
da Allah Mai girma da daukaka bai
taba turo bawa da ita ba, face
wannan bawan ya zama zababbe a
wurinsa, da ya daura shi akan wasu
sifofi da dabi’u, da su a karan kansu
sun isa su zamo dalilai na amsar
wannan sako da kuma rungumarsa
hannu bibbiyu; domin sako ne zuwa
ga kowa da kowa, saboda haka, dole
ne a bude wa kowa da kowa kofar
sauraron wannan sako k**an yanda
yake…
Alkur’ani mai girma cike yake da
bayanai da suke nuna irin zabin da
ya yi wa ‘yan sakonsa (Annabawa da
Manzanni), kuma litattafan tarihi sun
kiyaye mana irin yanda da yawan
wadanda s**a rungumi sakon Allah
ta hanyar Annabawansa sun yi hakan
ne sak**akon irin yanda ‘yan sakon
s**a sifantu da sifofin da girma da
mutuntaka tun kafin su zama
Annabawa ‘yan sakon Allah Ubangiji,
an sansu da son jama’a, da kuma
gabatar da maslahar al’umma akan
maslaharsu... An sansu da adalci, da
kuma rashin yin bambadanci wa
masu iko.. Allah Madaukakin Sarki ya
yi haka ne saboda rahamarsa zuwa
ga wadanda aka aika masu da
wannan sakon.. Kasancewar Annabin
da aka aika masu ya sami wata
babbar karaga a cikin zukatansu tun
kafin Annabci, abu ne da zai saukaka
masu amsar wannan sakon cikin
gaggawa, sakon da shi ne jin
dadinsu a duniya da lahira; muna
sane da lokacin da Sayyiduna
RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa
alihi sallam) ya tara danginsa –a
karon farko- domin isar masu da
sakon Allah, sai da ya fara da
shimfidar tuna masu da matsayin da
su da kansu s**a ba shi na
amintaccen da ba ya karya don a so
shi, ko domin yana son ya biya wata
bukatarsa ta muzguna wa wadanda
suke adawa da shi saboda wasu
dalilai, ba kuma ya son kansa, ya tara
danginsa ya ce masu : ((Yaya kuke
ganin idan na ba ku labarin cewa ga
wasu mahara can a bayan dutse suna
shirin auko maku, shin za ku gasgata
ni kuwa?)) take s**a amsa –ba tare
da tababa ba- cewa: tabbas za mu
gasgata ka, domin ba mu san ka da
komai ba sai gaskiya.
Hakika wannan shimfida mai kyau
abu ne da ake bukatarsa a tare da
duk wanda Allah ya yarda ya daura
shi a akan wannan turba ta isar da
sakon da Annabi Muhammadu
(SallalLahu alaiHi wa alihi sallam) ya
zo da shi, idan dai har Sayyiduna
RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa
alihi sallam) shi ne mafificinsu, kuma
cik**akonsu, to kuwa lallai wadanda
Allah ya zabe su su zamo gadar da
wannan sako zai bi ta kanta zuwa ga
al’umma su zamo sun sifantu da
wasu sifofi na girma da daraja,
sifofin da za su sanya al’umma – duk
da bambancinsu na siyasa da
fahimta- su rinka amsar wannan sako
cikin sauki da yarda, rungumar wani
sashe na al’umma da suke takarar
siyasa da wasu daga cikin malaman
addini suke yi abu ne da yake toshe
mutane da yawa ga barin kiran da za
a yi masu na bin addini.. Kuma
hakan ba karamin munana wa
addinin yake yi ba..
Saleh Kaura

28/12/2018

*TSAKANIN : SANA'A DA AIKIN
ALBASHI...*
*"Jack Ma"* fitaccen mawadaci ne a
kasar Sin (China), hasali ma shi ne na
daya a cikin jerin masu wadata a
kasar, ana kiyasta dukiyarsa da dalar
Amurika bibiyan 39, shi wannan
mutumin ne da kansa yake cewa :
«Da za ka ajiye kudi da ayaba a
gaban birrai, babu shakka birran
ayaban za su zaba; saboda ba su san
cewa kudin zai iya saya masu ayaba
mai yawa ba..!
Da kuma za ka yi wa mafi yawan
mutane wannan gwajin, ka ba su
zabi tsakanin yin sana'a da aikin
albashi na karshen wata, da kuwa
mafi yawan mutane za su zabi aikin
albashi na karshen wata; saboda ba
su san cewa sana'a tana kawo kudin
da ya wuce abin da ake samu a
matsayin albashi ba, ba kuma su san
cewa sana'a ita ce za ta sauya
rayuwarsu zuwa sama ba...
Cikin abubuwan da suke sanya
mutane su zama talakawa akwai
tunaninsu na cewa ba a iya samun
damammaki a harkar sana'a da
kasuwanci, saboda abin da s**a koya
a tsawon rayuwarsu ta makaranta shi
ne : ana yin aiki ne domin a sami
albashi a karshen wata, sun kuma
koyi cewa : a maimakon ka yi wa
kanka aiki domin bunkasa rayuwa,
gara ka yi wa wani aiki ya biya ka..!
Haka ne, lallai albashin karshen wata
zai iya katange ka ga barin fadawa
cikin talauci, amma kuma a gefe
daya zai katange ka ga barin shiga
cikin sahun masu arziki da
mawadata..
A tsawon rayuwa ta ban taba ganin
mutumin da yake fara aiki daga
karfe 8 na safe zuwa 3 na yamma ya
zamo mai arziki ba, Allahumma sai
dai idan barawo ne shi..»

03/05/2018

The entire management of SITCOSS want to invite the PTA meeting which include only guardian/parent of SS 3 student.Which is schedule to take place on sunday 6/5/2018,by 9am prompt at the school assembly hall.Thank you.

Address

Nassarawa Quarters Talasse, Balanga Local Government
Elelenwo

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Telephone

+2349071614406

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Isah Tsangaya Comprehensive Secondary School Talasse - Sitcoss posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Sheikh Isah Tsangaya Comprehensive Secondary School Talasse - Sitcoss:

Shortcuts

Share

Category