23/06/2026
TASU'A DA ASHURA (1)
Ina tunatar da Al'ummar Annabi Saw gobe laraba ce 9 ga watan AlMuharram wadda a ke azumin Tasu'a
Jibi Alkhamis kuma 10 a ke azumin Ashura
عن عَبْدَ اللَّهِ بْنَ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، يَقُولُ : حِينَ صَامَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَوْمَ عَاشُورَاءَ، وَأَمَرَ بِصِيَامِهِ، قَالُوا : يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنَّهُ يَوْمٌ تُعَظِّمُهُ الْيَهُودُ، وَالنَّصَارَى، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " فَإِذَا كَانَ الْعَامُ الْمُقْبِلُ - إِنْ شَاءَ اللَّهُ - صُمْنَا الْيَوْمَ التَّاسِعَ ". قَالَ : فَلَمْ يَأْتِ الْعَامُ الْمُقْبِلُ حَتَّى تُوُفِّيَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ. رواه مسلم
Ibnu Abbas ya ce : Yayin da Annabi Saw ya yi azumin Ashura kuma ya yi umarni da a yi, sai su ka ce ya Manzon Allah saw Ashura fa rana ce da Yahudu da nasara su ke girmama ta, sai Annabi saw ya ce: Idan shekara mai zuwa ta zo In sha'Allah za mu yi azumin ranar tara ma, Ibnu Abbas ya ce : shekara mai zuwan ba ta zo ba har Manzon Allah saw ya cika. Muslim 1135, Abudawuud 2445 Ibnu Majah 1736 Ahmad 1971
Note: A karshen rayuwar Annabi Saw ya na son ya saba wa yahudu kuma suna yin Azumin Ashura shi ya sa ya ce zai hada biyu dan ya saɓa musu.
Allah ya ba mu ikon yi ya kuma karba mana
Usman Ibrahim Giade
8/01/1448 23/06/2026