Matsalolin Ido da Hanyoyin Magance Su Cikin Sauki

Matsalolin Ido da Hanyoyin Magance Su Cikin Sauki Shafi ne da zai ke kawo muku bayanai game chiwon Ido da Hanyoyin Magance Su Cikin Sauki da Hausa

DA GASKE HADA IDO YANA KAWO APOLO? Ciwon idon Apolo wata cuta ce ta kwayoyin cuta ko ƙwayoyin halitta da ke sanya idanu ...
24/08/2026

DA GASKE HADA IDO YANA KAWO APOLO?

Ciwon idon Apolo wata cuta ce ta kwayoyin cuta ko ƙwayoyin halitta da ke sanya idanu yin ja, kumburi, fitar kwantsa ko yawan hawaye, tare da tsananin ƙaiƙayi da zafi.

A lokacin da cutar ta barke a yankuna k**ar nan Arewacin Najeriya, tana saurin yaɗuwa daga mutum zuwa mutum saboda yadda ake mu'amala ta yau da kullum.

Shin da gaske hada ido da mai ciwon yana sa yaduwar ciwo?
ta wace hanya Ake kamuwa?
meya k**ata kayi domin kare kan ka daga kamuwa ?
meya k**ata kayi Idan Ka kamu da ciwon apolo?

Ku karanta cikakken rubutun a comment section



Daga Aliyu Naziru OfficerIdan ka tashi Aure karkace kai lallai iya Genotype da HIV zaku yi, yanada kuyi duk wani pre-mar...
29/04/2026

Daga Aliyu Naziru Officer
Idan ka tashi Aure karkace kai lallai iya Genotype da HIV zaku yi, yanada kuyi duk wani pre-marital test wanda ya k**ata. Wasu suna gujewa kashe kudi sai su ce a musu iya Genotype da HIV, yin hakan akwai matsala musamman ga Mace koda baida complete kudi a hannun shi yak**ata ki cika masa domin kusan status dinku

Babbar barazanar rashin yin hakan akwai Blood Group a ciki, misali ka Aure Macen da Blood Group dinta 0-Negative kai kuma sai naka yazo 0+Positive baku sani ba. Wannan shine babban tashin hankalin da ake kira "Rhesus incompatibility"

Barazanar da zaku fara fuskanta itace lokacin da Matarka ta samu ciki, Mace mai Blood Group O-Negative idan ta Aure Miji mai Positive k**ar O+, A+, B+, ko AB+, akwai yuwuwar jaririn dake cikintq ya kasance mai Positive k**ar mahaifinsa

Inda matsalar take shine, ita Matarka Negative ce, idan yaron jinin shi ya zama Positive jikin uwarshi zai dauki jinin yaron a matsayin foreign object ma'ana bakon abu haka zai saka Anti-bodies din jikin Matarka su kaiwa jaririnta farmaki

Kunsan meye dalilin daya saka zaku ga wasu Matan suna yawan zubar da ciki, suna yawan bari, suna yawon haifan yaro a Mace, suna yawan haifan yara da cutar sanyi wanda ake kira da jaundice, ko a haifa yaron da zai dinga zama kusan ko wani lokaci da cutar karancin jini na Anemia?

Wannan dalilin ya saka idan Mace tana yawan fuskantar irin wannan matsalar inhar ba'a gano dalilin ba sai a dinga cewa Mayu ne s**a Shane mata jini, ko ace mayu ne suke kashe mata yaron saboda yawan zubar da ciki da yawon haifan macaccen yaro ko yaro mai dauke da Anemia

Babban tashin hankalin na biyu a lokacin da Mace ta samu ciki shine, su mutane masu 0-Negative suna iya baiwa kowa jinin su amma su ba kowa bane yake iya basu jini sai mau irin nasu sai yasa ake kiransu da Universal Donors

A cikin mutane 100% kaso 7-8% ne kacal masu 0-Negative sai yasa samun jini mai Negative yake karanci musamman a lokacin gaggawa wanda hakan yake sanadiyar mutuwar mutane dayawa

Samun lafiyar Mace mai jini 0-Negative a lokacin da take da ciki shine a dinga yi mata Allurar Anti-D (Rhogam). Ita Anti-D ana yin ta ne saboda Anti-bodies din jikin Matarka kar su dinga kaiwa jaririn dake cikinta hari

Babban kalubale na uku shine tsadar Allurar Anti-D, kudinta yana iya kaiwa 100k, 150k ya danganta da Asibitin daka kai Matarka kuma ana yin Allurar sau biyu zuwa sau uku ya danganta da lafiyar Matarka. A lalace zaka ajiye 300k iya kudin Allura

Bawai rashin yarda da kaddara bane kaucewa fadawa cikin wannan hadarin, shi kanshi addini ya karantar da cewa ku kauracewa kanka fadawa cikin matsala ko masifa. Ubangiji Allah ya bamu lafiya da abinda lafiyar zata ci

In ji Aliyu Naziru Officer

03/04/2026

03/04/2026

Nice presentation brother.... We need to start thinking out of the Box my fellow Nigerians

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Oomarfaruq Njitti, Basiru Zubairu, Khamisu Auwal, Abdulha...
02/04/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Oomarfaruq Njitti, Basiru Zubairu, Khamisu Auwal, Abdulhadi Umar

Na san mutane da dama na tambayar menene alaƙar Mura da Ciwon Ido. To dan wani bayani da zai taimaka don fahimta cikin s...
02/04/2026

Na san mutane da dama na tambayar menene alaƙar Mura da Ciwon Ido. To dan wani bayani da zai taimaka don fahimta cikin sauki.

Mura (ko kuma Common Cold da turanci / ciwon ido (ko kuma "Pink Eye"/Conjunctivitis) suna da alaƙa kai tsaye, musamman ta hanyar ƙwayar cutar mura (Viral Infection).

Yadda alaƙar ke faruwa:
Mura na haifarwa da kwayoyin cuta irin su Adenovirus ko wasu kwayoyin cuta na numfashi (Respiratory viruses). Waɗannan kwayoyin cuta ba kawai suna shafar hanci, makogwaro da huhu ba, har ma suna iya kaiwa ga idanu.

Idan kwayar cutar ta shiga idanu (misali ta hanyar shafar ido da hannu bayan atishawa ko tari, ko ta hanyar iska), tana haifar da viral conjunctivitis — wanda ake kira "eye cold" ko ciwon ido na mura.

Hakan yana faruwa saboda idanu suna da wani tantani (conjunctiva) mai k**a da na hanci da makogwaro, don haka kwayar cuta tana yaduwa cikin sauƙi ta hanyar wannan tantanin majina (mucous membranes)

××Alamun da ke faruwa a idanu lokacin mura:

1. Ido ya zama ja ko ruwan hoda (pink/red eyes).

2. Ciwon ido, ƙaiƙayi (itching/burning), ko jin zafi.

3. Ruwa mai yawa daga idanu (watery discharge), wani lokaci farin ruwa mai ɗan kauri.

4. Kasa sakewa a cikin haske (light sensitivity).

5. Ido na iya kumbura makil da ruwa, musamman da safe.

Waɗannan alamomi na iya faruwa tare da alamun mura na yau da kullum k**ar atishawa, zubar ruwan hanci, tari, zazzaɓi ko ciwon kai.

Wani muhimmin bayani :

×× Ba duk ciwon ido ba ne na mura, amma yawancin lokuta na viral conjunctivitis yana faruwa tare da mura ko flu-like symptoms. (Mura Mai k**a da ta tsuntsaye)

Yadda ta ke yaɗuwa:

1. Ta hanyar kaiwa hannu zuwa ido (misali bayan shafa hanci ko baki).

2. Ta hanyar iska idan mutum mai mura yai atishawa ko tari kusa da kai.

3. Idan ka riga ka kamu da mura, kana iya yaɗa kwayar cutar zuwa idanunka da kanka idan ka shafi fuskar ka.

Magani da kulawa:

Viral conjunctivitis na mura yawancin lokuta yana warkewa da kansa cikin makon ni 1-2 ba tare da magani na musamman ba.
1. Magungunan kashe kwayoyin cuta (antibiotics) ba sa aiki a kan kwayar cuta virus.

2. Yi amfani da ruwan sanyi ko dumi don rage kumburi da samun jin daɗi.

3. Ka wanke idanu da ruwa mai tsabta, kada ka shafa idanu da hannu.
4. kuma kada ka raba (sharing) towel ko abin shafa Ido (Hankici) da wani.

5. Idan alamomin sun tsananta (ciwon ido mai tsanani, canjin gani, ko kumburi mai yawa), je ka ga likita ko likitan ido nan da nan — domin yana iya zama na kwayan cuta (bacterial) ko wani abu dabam.

Rigakafi:
1. Wanke hannu akai-akai.

2. Kada ka shafa idanu, hanci ko baki da hannu mara tsabta.

3. Ka guji kusanci mutanen da ke da mura.

4. Idan kana da mura, ka rufe baki da hanci lokacin atishawa/tari.

A takaice, mura na iya haifar da ciwon ido kai tsaye ta hanyar yaɗuwar kwayar cuta zuwa idanu, kuma wannan shine abin da ake kira "eye cold".
Ba shi ne kadai ba, amma yana da yawa musamman a lokacin sanyi ko lokacin murar hunturu.

Idan ka ji wani abu, ka huta sosai kuma ka kula da tsabta don kada ya yaɗu.

Bayani mai Muhimmanci:

×I Idan Alamun sun tsananta, je ka ga likita ko kwararren mai aikin ido (Ophthalmic Nurses).
Idan kaji dadin wannan bayanin, to danna mana like, don samun karfin gwaiwar cigaba da kawo muku sabbin bayanai masu inganchi.
Ku yi mana sharing

27/03/2026

Yau mu ƙaru da wannan.
Nasan akwai nasan masu yaya mata da suke da mara sa lafiya, musamman ta bangaren idanu. Ku yi hakuri da Jarrabawar, In Sha Allah alkhairi ne gare ku

22/03/2026

Barka da Sallah yan uwa. Shin kuma iya kallon video din nan qarau ba tare matsala ba?
Ko hotunan suna maka duau-dusu?
Ka yiwa kanka alkalanci mu hadu a comment section don duba yuwuwar tainaka ma da shawarwari...
Da fatan za a wuni lafiya

06/02/2026

Taba kidi, taba karatu...

Address

Kano
Dutse

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Matsalolin Ido da Hanyoyin Magance Su Cikin Sauki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Matsalolin Ido da Hanyoyin Magance Su Cikin Sauki:

Shortcuts

Share