17/02/2022
3-UMMU SULAIM
SADAKINTA MUSULUNCI
asalin sunanta rumaisa'u ko gumaisa'u,yar milhan,mutuniyar madina,yar kabilar kazraj.
Mahaifiyar maiyiwa manzon Allah hidima "Anas bn malik".mijinta malik nadr sannan sahabin manzon Allah abu Dalha,zaidu dan sahl mutumin madina,ta haifi da dashi abu umair dan Abdullah ta halarci yakin hunayn da uhud sannan tana cikin sahabbai masu falala.
FALALARTA
-Ta kasance SADAKINTA shine MUSULUNCI.ibn Sa'ad ya ruwaito a cikin Dabaqaat daga Anas dan malik R.A yace " Abu Dalha R.A ya nemi aurenta (kafin ya musulunta)sai tace bai kamata na auri mushiriki ba,bakasan cewa da za'a kona gumakanku bazasu iya kare kansu ba,sai ya juya yana tinanin abinda ta fada.sai yace "ki bani zan amsa (wato musulunci).
Sai tace wannan shine a matsayin sadakina.
- thabitul Bannani yace "ban taba ganin mace mafi girman da karamar sadaki kamar Ummu Sulaim ba.
- na daga cikin falalarta manzon Allah yana kai mata ziyara sannan yana wasa da danta "k***n ga Anas dan malik wanda akewa alkunya da abu umair".
Anas yace wani lokaci manzon Allah ya ziyarceta sai yace "me yasa naga bakin abu umair yayi sanyi? Sai tace tsuntsunsa ne ya mutu ya kasance yana wasa dashi,sai manzon Allah yake shafar kansa yana cewa abu umair me yasamu dan tsuntsunka.sannan Anas yace bai san manzon Allah ya na shiga wani gida ba face gidanta.
- sannan ta halarci uhud
- ta kasance tayi hakuri mai kyau alokacinda danta ya rasu mijinta baya gari bayan dawowarsa ta dafa masa abinci ta har sukayi kwanciyar aure,can sai tace masa"ya abu Dalha shin kana ganin idan wani yanemi aron abu kabasshi,sannan bai maido maka ba idan kaje ansa yaki baka meyayi? Sai yace baiyi adalci ba.sia tace ubangijin da ya baka da aro ya anshi abinsa.sai ya ce Allah yaji kansa. Manzon Allah ya sanya musu albarka saita haifi da Manzon Allah yasa masa Abdullahi.
Ibaya yace Falalar wannan hakurin dasukayi wannan dan nasu Abdullahi saida ya haifi yaya bakwai dika mahaddata.