16/02/2022
FULANI KAM AKWAI ARNA NE?
'Yan Ta'adda sun bar kauyuka sun fara shigowa gari suna addabanmu kwana biyun nan, jiya sun shigo sau biyu (yamma da kuma dare), Haka yau Laraba ma sun shigo da safe muna cikin makaranta s**ayi ta'addancin su a gari hakan yasa yan gari s**a tunzura s**a fara zanga-zanga wannan dalilin yasa aka fitar da sanarwa a cikin makaranta cewa kada kowa ya fita sai lokacin tashi yayi watakila kafin wannan Lokacin masu zanga-zangar sun gama, hakan kuwa akayi sai da lokacin tashi yayi muka fito muna zuwa bakin Gate gari yayi shuru ba hayaniya kowa yana tsorace sai wani abokina yake tambayata "cikin fulani kam akawai arna ne?". Na rasa ma abunda da zance masa baisan cewa ni Fulani ne ba.
Wannan ba shine karonsa na farko ba duk wani kwatance da zaiyi na 'yan ta'adda da Fulani yake yi baya ma kiran cewa yan bindiga ko yan ta'adda, bana ko tanka masa amma ina matukar jin ciwon abun.
Naje wani kauye a cikin karamar hukumar Tsafe, acikin wannan kauye akwai yan ta'adda ansan su, ansan iyayensu, ansan cewa su yan ta'adda ne suna iya baro Jeji da bindigar su su shigo kauyen nasu kuma ba Fulani bane amma wani dan kauyen yana min tadin yan ta'adda yana kiransu da Fulani. Naji ciwon abun nan.
A cikin wannan kauye akawai wadanda naji su suna tadin abun da ya shafi gidan su daya daga cikin su, yace "ya taso gidan su da akwai shanu" sai dayan yai caraf yace "ashe asalinku Fulani ne?" Nan fa cikin sauri yace "a'a su ba Fulani bane, su Kanawa ne asalinsu". Wai ya fadi haka ne fa saboda a wannan kauyen suna kallon Fulani ne kawai a matsayi 'yan ta'adda.
Ina cikin rubutun nan wani yaro da nake masa karatu ya shigo nace masa bakaje makaranta bane yau? Yace min " yaje amma kowa babarsa taje ta dauke shi" saboda me?, "yace saboda fulani sun shigo gari" Nace Fulani!🤔.
Meyasa saboda an dasa masa aqidar cewa Fulani 'yan ta'adda ne.
Har ta kai ga a wannan yanki na jihar Zamfara akwai yadda ta'addacin ya koma tsakanin Hausa da Fulani. Wannan wacce irin musifa ne!.
Dan Allah!
-Fulani ba shine dan kauye ba, ko wanne irin yare akwai shi a kauye.
- ba yan kauye bane kawai yan ta'adda, akwai yan taadda acikin burane.
-Fulani ba 'yan ta'adda bane, kamar yadda akwai 'yan ta'adda cikin Fulani haka akwai su a cikin Hausawa da kuma ko wanne yare.
Allah ya dawo mana da zaman lafiya a wannan Kasa🙌, Amin.
© Ibrahim Usman
16/02/2022