20/11/2025
DEDA TechHub Digital Literacy Program – 2025 Cohort 2
Biyo bayan nasarar Cohort 1, a yau Alhamis 20/11/2025, an kaddamar da Cohort 2 na Digital Literacy Program a Danja, wanda zai gudana na tsawon watanni uku. Dalibai daga makarantu da mutanen gari zasu ci gajiyar shirin.
Abubuwan da aka gudanar sun haɗa da:
1. Rijistar dalibai
2. Bayani game da abinda za a koya
3. Bayani kan dokoki da ka’idojin program
Wadanda s**a sami halartar taron sun hada da, Mal. Yushau Zakariya Salisu, Eng. Ibrahim Shehu Danja, da mambobin DEDA TechHub kamar su Umar Abdulazeez, Mubarak Bala, Baffa Haruna da sauran masu bada gudummawa.
– DEDA TechHub Media Team