Abu Haidar Gadaka

Abu Haidar Gadaka

Share

This page was solely created for posting relevant and positive things for purpose of informing, imparting and helping people with the best we can sort

27/06/2022

Cikakkiyar jarumta itace shanye fushi a lokacin da kake da damar daukar mataki

23/06/2022

LALLAI SAKKWATAWA KUYI BABBAN KAMU

Ina ma Ina Ma Ina wajen

Ahlulbaity And Sahaba Foundation Sokoto ta shirya gagarumar lacca Mai taken.

MAKON FADAKARWA AKAN DARAJOJIN MANZON ALLAH (S.A.W)

Malamai masu gabatar da lacca suna kamar Haka.

1-Sheikh Prof Mansur Ibrahim Sokoto
2-Sheikh Dr Rabiu R/Lemo Kano
3-Sheikh Abubakar Abdulsalam (Baban Gwale) Kano
4-Sheikh Dr Jamil Sadis Zari'a
5-Sheikh Ahmad Sani Danfili
6-Sheikh Idriss Garba
7-Sheikh Dr Jabir Sani Mai Hula
8-Sheikh Dr Sani Abdullahi Jo's
9-Sheikh Imam Abu Huraira
10-Sheikh Muhammad Bashir Marafa

Ya Allah ka Kara Annabin mu manzon Rahma (S.A.W) daraja da daukaka Amin ya Hayyu ya Qayyum.

A.A Baushe (Abu Ja'afar)

11/06/2022

STATE PREACHING JIBWIS YOBE STATE!!

A Yau Asabar 11-June-2022 kungiyar Izalah ta jihar yobe zata gabatar da gagarumin wa'azi jiha a Garin Nguru dake jihar Yobe karkashin jagoranci shugaban kungiyar ta jihar Yobe Alhaji Bala Salihu Bakabe Nguru.

Ku kasance tare da manyan shafin mu na Jibwis Yobe, da kuma Jibwis Social media Fika West, page zamu kawo muku wa'azi Kai tsaye live Insha Allah.

Zaku iya garzaya domin kuyi like din shafin mu ta wannan link.

https://www.facebook.com/sunnahpreachers/

https://www.facebook.com/Jibwis-social-media-fika-West-1629287297169652/

Allah ya bada ikon zuwa yasa mu wanye lafiya Amin ya Hayyu ya Qayyum.

JIBWIS SOCIAL MEDIA YOBE STATE DIRECTORATE
Aminu Alhaji Adamu Baushe (Abu Ja'afar)
11-June-2022

Photos from Abu Haidar Gadaka's post 06/06/2022

A KASAR INDIA KUMA

Mai magana da yawun jam'iyyar Bharatiya Janata Party mai mulki na Kasar India mai suna Sambit Patra (La'anatul-Lah) ya yiwa fiyayyen Halitta (ﷺ) batanci

Babban Limamin Masallacin Haramin Makkah Sheikh Abdul-rahman Assudais yayi Allah wadai da batancin da Sambit Patra ya yiwa jagoran mu حسبنا الله ونعم الوكيل

Har an samu wasu jaridu a Kasar ta India wanda s**a zana zanen batanci s**a siffanta da fiyeyyen Halitta (ﷺ) akan zagin da shi wannan Sambit Patra ya yiwa Baban Al-Qasim (ﷺ)

Watakila zuwa gobe Gwamnatin Saudiyyah zata yanke alakar Diplomasiyya da Kasar India, muna kyautata zaton sauran Kasashen Musulmin duniya zasu dauki irin wannan matakin

Allah Ka isar wa Shugaba Halitta (ﷺ), rayuka da dukiyoyin mu sun zama fansa a gareshi (ﷺ)

Yaa Allah Ka nuna wa Sambit Patra karfin ikon Ka, Allah kasa ya zama izna ga masu hali irin nasa

04/06/2022

ABUJA MA AKWAI MASOYAN MA'AIKI (SAW)

Wannan shine wulakantaccen 'dan banga Musulmi wanda ya yiwa Baban Al-Qasim (SAW) batanci a Abuja aka zartar masa da hukuncin da ya dace da shi

Ashe a Abuja ma fiyayyen Halitta (SAW) yana da masoya 'yan gani kasheni

Allah Ka kara wa Baban Al-Qasim daraja (SAW)

Arewa Intelligence
4-6-2022

Photos from Abu Haidar Gadaka's post 27/05/2022

HOTUNA: Ziyarar Imamu Ahlus Sunnah Wal Jama'a Sheikh Abdulwahab Abdullah Kano ga Daraktan Da'awah na Kasa, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah)

Yayin wannan ziyara an tattauna muhimman batutuwa da zasu ciyar da addini da al'umma gaba

Muna rokon Allah ya karama masu lafiya da nisan kwana masu albarka. Amin

JIBWIS Katsina

26/05/2022

Duk matsayin da Allah yakai ka karka kuskura ka manta da Matsayinsa a gareka!

23/05/2022

SHAWARA GA SAMARI

Ina Baiwa samari shawara, da zaran kaje ta Fara maka yanga, tana kada maka kai, ta nuna bata da lokacinka, kace Allah ya bada sa'a kaje ka jira wadda ta dace da kai.

👉Sheikh Dr Abdallah Usman Gadon kaya (Hafizahullah)

Ya Allah ka datar damu alkhairinsa Allah ya bamu ta Gari Amin ya Hayyu ya Qayyum

22/05/2022

ALLAH YA JIKAN SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM KANO

Wannan shine Alaramma Sai'd Haruna Yankaba (Hafizahullah).

Alaramma yana cikin wadanda idan suna karanta Al-Qur'ani zaka ji yana ratsawa har cikin zuciyarka.

Kafin nan shine wanda ya jawa marigayi Sheikh Ja'afar Muhamud Baki, kafin rasuwar Malam.

Yanzu haka shi yake jawa babban malamin Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar limamin Al-Furqan dake Kano baki.

Shi fah Alaramma Sai'd ba ruwan shi da surutu kawai shi dai ya rera Al-Qur'ani Mai girma a tsanake haka yafi so.

Allah madaukakin sarki yasa Al-Qur'ani Mai girma ya cecemu Allah ya karawa Alaramma Lafiya tare da Nisan kwana, Allah ya jikan sheikh Ja'afar ya kuma gafarta masa yasa aljannace makomarsa.

Amin ya Hayyu ya Qayyum.

Aminu Alhaji Adamu Baushe (Abu Ja'afar)
22-May-2022

Photos from Abu Haidar Gadaka's post 20/05/2022

Ziyara zuwa ga Pantami Primary School, Gombe

Ziyara da Malam ya kai zuwa ga makaranatar daya kammala. Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya je ziyarar ne domin du ba ayyuka na ci gaba da ya samarwa makaranatar ta hanyar hukuma da kuma Corporate Social Responsibility (CSR) na Gina computer Centre da kuma gyaran makarantar gaba dayan ta.

Malam Pantami ya samu daman ziyarar tare da aminin sa, Shaykh Dr Dahiru Inuwa Ibrahim da s**a yi karatu tare a makarantar kuma ajinsu daya har su ka kammala. Sannan da Shaykh Abdurrahman Umar Maigona, da sauran jamaah masu yawa.

Tawagar ta samu karba ta musamman daga babban sakatare na karamar hukumar Gombe, da Headmaster na makarantar da sauran malamai.

Sannan Malam ya yaba matuka da gaske akan ingancin aiki da ya gani, na sabunta makarantar tare da gina masu kyakykyawar Computer Centre, sannan ya tunatar da dalibai su dage da karatu da manufa mai kyau.

Ranar ziyara: 13/05/2022CE

Signed: Management

Want your school to be the top-listed School/college in Damaturu?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Damaturu