11/01/2026
RAHOTO: SAƘON UMMA ZEENATUDDEEN IBRAHEEM GA ƳAN’UWA
A ranar Asabar, 10 ga watan Janairu, Malama Umma Zeenatuddeen Ibraheem (H) ta gabatar da muhimmin jawabi ga ƴan’uwa a Gwagwalada, wanda ya ta’allaka ne kan halin da al’ummar Musulmi ke ciki a wannan lokaci mai sarkakiya.
A cikin jawabin nata, Umma (H) ta ja hankalin ƴan’uwa sosai kan yawaita addu’a musamman ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wacce ke kan gaba wajen kare Musulunci, tsayawa kan gaskiya, da goyon bayan mazlumai a fadin duniya.
Daga cikin addu’o’in da ta fi jaddada a yi su a kullum akwai:
DU'A'U AHLIS THUGŪR
Wadda Imam Ali Zainul Abideen (A.S) ya koyar, ana karanta ta domin kariya ga Musulmi masu tsaron iyakoki da al’ummomi, da neman sauƙi ga raunanan duniya, da kuma rugujewar makiya da lalacewar makircin su.
Umma ta yi kira ga kowa ya ɗauki wannan addu’a da muhimmanci, musamman a irin wannan lokaci da tsarukan zalunci ke ƙoƙarin mamaye duniya.
Ga duk mai buƙatar PDF na wannan addu’a, za a iya samu ta hanyar ziyartar Telegram na Makarantar Al-Kauthar.
Link zai kasance a comment section.
– Makarantar Al-Kauthar