29/07/2026
Gidauniyar Kole Shettima Trust Fund (KSTF), ƙarƙashin jagorancin Dr. Kole Ahmed Shettima, ta gudanar da gagarumin tallafi ga Bilal Bin Rabah Nursery, Primary and Islamiyya School da ke unguwar Isah Yuguda, Nasarawa, cikin garin Bauchi, da nufin inganta harkokin ilimi da samar da ingantaccen yanayin koyo ga ɗalibai.
Tallafin ya haɗa da litattafan rubutu na 20 leaves guda 480 (kwali 1), 40 leaves guda 192 (kwali 1), da 60 leaves guda 144, fararen allo (White Board), biro guda 1,000 (kwali 1), duster guda 12 (akwati 1), marker guda 100 (akwati 1), fensir guda 2,160 (rabin kwali), kayan goge-goge (Cleaner) guda 5,000 (kwali 1), da kuma bencuna 150 domin azuzuwa takwas na makarantar.
Haka kuma, gidauniyar ta ba makarantar Alƙur'ani Mai Tsarki guda 28, tare da sauran litattafan addinin Musulunci, domin ƙarfafa ilimin addini da tarbiyyar ɗalibai.
An bayyana cewa wannan tallafi na daga cikin manufofin Kole Shettima Trust Fund na tallafa wa ɓangaren ilimi, tare da samar da kayan koyarwa da za su taimaka wajen bunƙasa ilimin yara a Jihar Bauchi.
A nasa jawabin, shugaban makarantar ya yaba da wannan gudunmawa, yana mai cewa tallafin zai taimaka matuƙa wajen inganta harkokin koyarwa da koyo. Hakazalika, malamai da ɗaliban makarantar sun bayyana matuƙar godiyarsu ga Dr. Kole Ahmed Shettima, tare da yi masa addu'ar Allah Ya saka masa da alheri, Ya ƙara masa lafiya da ɗaukaka domin ci gaba da ayyukan alheri ga al'umma.