13/09/2026
🌹 QAFILATUL MAHABBA BAUCHI LGA BRANCH 🌹
YAUMUL AI-TAM — RANAR MARAYU
12 September, 2026 / 30 Rabi’ul-Awwal, 1448 AH
Alhamdulillah, a ranar Asabar 12 ga September, 2026, Qafilatul Mahabba Bauchi LGA Branch ta gudanar da Hidimar Fita da Marayu, a Fariah Comprehensive Secondary School, Fadaman Mada, Bauchi.
An kai marayun filin shakatawa, tare da samar musu da abinci da kuma faranta musu rai. Wannan na daga cikin ayyukan alheri da Qafila ke gudanarwa a cikin watan Rabi’ul-Awwal.
Muna mika godiya ta musamman ga Mu’assisin Qafilatul Mahabba, Prof. Ahmad Ibrahim Maqary, bisa wannan kyakkyawar manufa da jajircewa wajen hidimar al’umma.
Haka kuma muna godiya ga Coordinator na Qafilatul Mahabba Bauchi LGA Branch da dukkan Members, bisa gudummawa, halarta da kokarin da s**a bayar wajen ganin wannan hidima ta gudana cikin nasara.
🤲 Allah Ya karɓi wannan aiki, Ya saka wa kowa da alheri, Ya ƙara mana ikon ci gaba da hidimar alheri. Ameen.
Qafilatul Mahabba Bauchi LGA Branch 🌹