مجلس الأبحاث الجلية للإمام أحمد أبي بكر الإمام

  • Home
  • Nigeria
  • Bauchi
  • مجلس الأبحاث الجلية للإمام أحمد أبي بكر الإمام
26/12/2025
26/12/2025

SUNNONIN DA SUKEDA ALAQA DA RANAR JUMU'A

ALLAH YA TSAREMU DAGA SHARRIN YAHUDU DA NASARA
03/11/2025

ALLAH YA TSAREMU DAGA SHARRIN YAHUDU DA NASARA

KHALIFAN QADIRIYYA NA JIHAR BAUCHI YA KARYATA IKIRARIN DONALD TRUMP NA KISAN KIRISTOCI A NAJERIYA

Khalifan Qadiriyya na Jihar Bauchi, Prof. Muhammad Safiyyu Abdulkadir, ya karyata ikirarin shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, wanda ya yi zargin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya.

Da yake jawabi a garin Jos, yayin gudanar da Maulidin Maulana Sidi Abdul Qadir Jilani (RTA), Khalifa Prof. ya bayyana cewa wannan ikirari “magana ce marar tushe wacce zata iya haddasa rashin jituwa da tayar da hankali tsakanin al’umma.”

"Mu a Najeriya muna rayuwa cikin zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kiristoci. Muna aiki tare, muna tarurruka tare, kuma muna zama maƙwabta cikin haɗin kai da nufin ci gaban ƙasarmu,” in ji Khalifan.

Khalifan ya ƙara da cewa, irin waɗannan kalamai daga ƙasashen waje kan iya haifar da rikici idan aka yarda da su ba tare da bincike ba. Ya shawarci Kiristotin Najeriya da sauran qasashen qetate da su yi watsi da irin waɗannan maganganu marasa hujja, su maida hankali wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai.

“Ya kamata mu tsaya kan gaskiya da adalci, mu ƙarfafa zumunci da fahimtar juna domin dorewar zaman lafiya a ƙasarmu,”.

Sannan Khalifa Ya tuhum Trump da ya nuna inda akayi hakan a matsayin sa na shugaba.

A ƙarshe, Khalifa Prof. Muhammad Safiyyu Abdulkadir ya yi addu’a ga ALLAH Madaukakin Sarki da Ya ƙara wa ƙasar lafiya, Ya tsare ta daga duk wata fitina da tashin hankali.

“ALLAH Ya ƙara mana zaman lafiya, Ya ba mu albarka da haɗin kai, Ya tsare ƙasarmu daga duk wani makirci,”.

Bauchi State Qadiriyyah Council
3rd November, 2025.

Assalamualaikum Wannan Cibiya Mai Albarka tana farin cikin gayyatar Al'umma zuwa gagarumin muhadara Mai taken "Ladabi ga...
03/10/2025

Assalamualaikum

Wannan Cibiya Mai Albarka tana farin cikin gayyatar Al'umma zuwa gagarumin muhadara Mai taken "Ladabi ga Janabin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasallama.

Wanda zai gudana yau Juma'a 03/10/2025
bayan Sallar Magriba zuwa Isha'i
A Masallacin Ibn Hajar (Masallacin Baushe) dake Sabuwar Unguwar Railway Bauchi.

Allah ya bada ikon Halarta.

30/03/2025

Allah ya Isa Mana

Address

Masjid Jami' Ibn Hajr, Sabuwar Unguwar Railway
Bauchi

Telephone

+2348102704541

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when مجلس الأبحاث الجلية للإمام أحمد أبي بكر الإمام posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share