18/07/2026
ALMAJIRI BA NAUYI BA NE, ALBARKA NE GA AL'UMMA
Tsarin tsangaya ya kasance ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da aka yaɗa ilimin Alƙur'ani a ƙasarmu tsawon ƙarni. Dubban mahaddata, limamai da malamai sun fito ne daga wannan tsari.
Muna kira ga al'umma da su daina kallon almajiri da ido na raini. A maimakon haka, mu ba shi dama, mu ƙarfafa shi, mu tallafa masa, domin yana neman ilimin da ya fi kowanne ilimi daraja.
Inganta tsangaya ba yana nufin rusa ta ba ne. Yana nufin samar da muhalli mai kyau, kulawa, lafiya da ilimi domin almajirai su samu damar cika burinsu cikin mutunci.
The Voice of Almajiri za ta ci gaba da zama muryar gaskiya, kare martabar almajirai, da kira ga duk masu ruwa da tsaki su haɗa hannu wajen inganta tsarin tsangaya.
Allah Ya albarkaci malamanmu, Ya kare almajiranmu, Ya sa Alƙur'ani ya ci gaba da haskaka zukatanmu. Amin.
✍️ Sulaiman Sani Jikan Ladan
National Chairman, The voice of almajiri