19/09/2026
Na shiga matuƙar alhini da damuwa kan rasuwar ’yan Najeriya da dama a hannun jami’an Hukumar NSCDC yayin da suke tsare a jihar Neja.
Waɗannan mutane ne masu iyalai, ’ya’ya, iyaye da ’yan’uwa, waɗanda iyalansu suke da cikakken haƙƙin tsammanin cewa, duk da zargin da ake musu, gwamnati za ta kare rayuwarsu da mutuncinsu matuƙar suna hannunta.
Babu wani ɗan Najeriya da ya kamata ya shiga hannun hukumomin gwamnati ya rasa mafi muhimmancin haƙƙinsa, wato haƙƙin rayuwarsa.
Ina yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa gaggawar dakatar da jami’an da wannan al’amari ya faru a ƙarƙashin kulawarsu, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike. Wannan mataki ne mai muhimmanci na farko, amma bai kamata a tsaya a nan ba.
Dole ne binciken ya kasance mai zaman kansa, cikakke kuma a bayyane, sannan a bayyana sakamakonsa ga al'umma. Duk wanda aka samu da hannu wajen faruwar lamarin, ta hanyar aikata laifi, cin zarafi ko sakaci, dole ne ya fuskanci cikakken hukunci.
Iyalin waɗanda s**a rasu sun cancanci fiye da ta’aziyya. Sun cancanci sanin gaskiya da samun adalci. Haka kuma, ’yan Najeriya sun cancanci tabbacin cewa kasancewa a hannun gwamnati ba zai zama hukuncin kisa ba.
Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan mamatan, tare da addu’ar Allah Ya ba su haƙuri a wannan lokaci mai cike da damuwa kuma a gano gaskiyar lamarin ba tare da ɓata lokaci ba. -AA