11/07/2026
Ban san abin da ke cikin gidajenku ba, amma ina roƙon Allah Maɗaukaki: idan akwai mara lafiya a cikinsu, Allah Ya ba shi lafiya cikin gaggawa; idan akwai mai cike da damuwa, Allah Ya kawar masa da damuwar; idan akwai wanda ake bi bashi, Allah Ya biya Ya warware masa; idan akwai wanda ke cikin jarabawa, Allah Ya yaye masa; idan akwai wanda ake yi wa hassada, Allah Ya sa ya fi ƙarfin mahassadansa; idan akwai wanda aka yi wa sihiri, Allah Ya karya shi. Allah Ya ji ƙan magabatanmu da dukkan musulmai da s**a riga mu gidan gaskiya. Allahumma Ameen. 🤲