Ahlussuffah Azare

Ahlussuffah Azare العلم والتربية أساس الحياة

12/08/2026
📢 SANARWA TA MUSAMMANAHLUSSUFFAH ACADEMYSanarwa ga Ƴan Uwa MusulmaiAssalāmu Alaikum wa Rahmatullāhi wa Barakātuh.Shahara...
09/08/2026

📢 SANARWA TA MUSAMMAN
AHLUSSUFFAH ACADEMY
Sanarwa ga Ƴan Uwa Musulmai
Assalāmu Alaikum wa Rahmatullāhi wa Barakātuh.
Shahararriyar Makarantar AHLUSSUFFAH ACADEMY, wadda aka kafa domin inganta ilimin Al-Qur’ani Mai Girma, Larabci, Ilimin Addinin Musulunci da Ilimin Boko, tana sanar da ƴan uwa Musulmai da jama'a baki ɗaya cewa:
🧑‍🏫 AN BUƊE DAMAR ƊAUKAR SABABBIN MALAMAI
Makarantar ta shirya tsaf domin ɗaukar sabbin malamai ƙwararru a fannoni kamar haka:
Malaman Ƙur’ani Mai Girma
Malaman Larabci (Arabic)
Malaman Ilimin Addinin Musulunci (Islamic Studies)
Malaman Ilimin Boko (Western Education)
📅 Lokacin miqa Application:
Duk wanda yake sha'awar yin aiki tare da AHLUSSUFFAH ACADEMY, zai iya kai application ɗinsa daga:
Litinin, 10 ga Agusta 2026
zuwa
Juma'a, 14 ga Agusta 2026.
📍 Wurin kai Application:
Harabar AHLUSSUFFAH ACADEMY, dake
Unguwar Duhuwa Zaki, yamma maso kudu da gidan man Kitabu was-Sunnah na Yamma, da Tike Azare.
📝 INTERVIEW
Za a gudanar da Interview na malamai a ranar:
Lahadi, 16 ga Agusta 2026.
Duk wanda ya gabatar da application ɗinsa ya kasance cikin shiri domin halartar interview a ranar da aka ambata.
🎒 SANARWAR ƊAUKAR SABABBIN ƊALIBAI
Haka kuma, AHLUSSUFFAH ACADEMY tana sanar da iyaye da masu kula da yara cewa ta fara ɗaukar sabbin ɗalibai domin sabon zangon karatu na shekarar 2026/2027 a waɗannan matakai:
🏫 Nursery 1
📚 Primary 1 – 3
📖 Junior Secondary School (JSS 1)
📝 REGISTRATION
An buɗe Registration tun daga yau har zuwa ranar da za a koma makaranta:
Litinin, 24 ga Agusta 2026.
Duk iyaye ko masu buƙatar shigar da yara makaranta za su iya zuwa harabar makarantar domin:
• Sayen Form
• Cike Registration
• Samun ƙarin bayani kan tsarin karatu.
📖 ƊAUKAR ƊALIBAN KWANA (BOARDING)
Haka kuma, makarantar ta fara ɗaukar ɗaliban kwana (Boarding Qur’anic System) domin koyon karatun Al-Qur’ani Mai Girma da haddarsa.
Wannan sashe an tanade shi ne domin ɗaliban da suke da sha'awar haddar Al-Qur’ani Mai Girma cikin tsari na musamman da kulawa ta ilimi da tarbiyya.
📞 DOMIN ƘARIN BAYANI
Duk wanda yake buƙatar ƙarin bayani game da:
• Aikin Malamai
• Interview
• Admission
• Registration
• Boarding Qur’anic System
zai iya tuntubar waɗannan lambobi:
📱 08031319057
📱 08036184395
AHLUSSUFFAH ACADEMY
Ilimi • Tarbiyya • Haddar Al-Qur’ani.
Allah Ya ba mu ikon gudanar da wannan aiki cikin nasara, Ya sanya albarka a cikinsa. Āmīn.
Muna maraba da ku — Sai kun zo!

21/07/2026

خيركم من تعلم القرآن وعلمه الله

Address

Duhuwa Zaki Yamma Da Vocational
Azare
751101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ahlussuffah Azare posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share